An yi alla-wadai da waƙe-waƙen sojojin Isra'ila a cikin masallaci

Asalin hoton, X
- Marubuci, Daga Raffi Berg
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
Rundunar sojin Isra'ila ta yi alla-wadai da halayyar wasu dakarunta waɗanda aka ɗauki bidiyonsu suna waƙa da addu'o'in Yahudanci a lasifika cikin wani masallaci da ke Jenin na yankin Gaɓar Yamma da ke ƙarƙashin mamaye.
Lamarin ya zo ne yayin wani aiki da sojojin suka je yi, don tunkarar 'yan ta-da-ƙayar-baya a birnin, wanda zuwa yanzu ya yi sanadin mutuwar Falasɗinawa 11, a cewar ma'aikatar lafiya ta Falasɗin.
Rundunar sojin Isra'ila ta ce sojojin "za su fuskanci ladabtarwa kamar yadda ya dace".
Ta kuma ce za ta ɗauki mataki a kan irin waɗannan al'amura da aka ɗauki bidiyo na dakarunta a Gaza.
Bidiyon wanda ke yawo a shafukan sada zumunta, na nuna ɓangare daban-daban na masallacin.
A wani ɓangare, an ji yadda aka riƙa rera waƙa cikin harshen Hibiru game da yayewar duhu, wadda ake alaƙantawa da bikin Yahudawa na Hanukka ta cikin lasifikar da ke saman hasumiyar masallaci. Mutumin da ke ɗaukar bidiyon shi ma ya riƙa bin waƙar, yana ƙyalƙyala dariya.
Wasu sassa na bidiyon sun nuna sojoji a cikin wani masallaci suna karanta addu'o'in Yahudanci a lasifika. Ma'aikatar harkokin wajen Falasɗin ta yi alla-wadai da abin da ta kira "izgilanci da [wurin ibada] mai tsarki".
A cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Alhamis, rundunar sojin Isra'ila ta ce abin da sojojin suka yi, "ya saɓa da kundin ƙa'idojin aiki na rundunar sojojin Isra'ila a cibiyoyin addini".
Sanarwar ta ce " nan take an janye [sojojin da aka samu da hannu] daga harkokin aiki".
Ta ƙara da cewa: "Halayyar da sojojin suka nuna a bidiyon ta yi zafi kuma kwata-kwata ta saɓa da aƙidojin aikin rundunar sojin Isra'ila."
Al'amuran da suka faru a Jenin, ba su ne karon farko da sojojin Isra'ila suka yi wani abin tir na wata muguwar halayya ba, kuma aka ɗauka a bidiyo aka buga a shafukan sada zumunta a baya-bayan nan.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Tun da Isra’ila ta fara yaƙi a Gaza daga ƙarshen watan Oktoba, bidiyo ke fitowa daga Gaza, ciki har da wani da ke nuna wani soja yana farfasa kayayyaki a wani shagon sayar da kayan wasan yara, yayin da wani mutum da ke ɗaukar bidiyo yake ta ƙyalƙyala dariya.
Akwai kuma, wani da ke nuna sojoji na cinna wuta kan wasu kayayyaki a bayan mota, da kuma wani yana nuna yadda ake bincike-bincike a cikin kayan mata a wani abu da ya yi kama da gidan mutane.
A ranar Lahadi, mai Magana da yawun rundunar sojojin Isra’ila Rear Admiral Daniel Hagari ya tir da irin wannan halayya ta sojojin.
"Dakarun sojin Isra’ila na aiki bisa tsarin ƙa’idoji da aƙidar rundunar," a cewarsa. "Ana buƙatar sojoji a fagen yaƙi su nuna ƙwarewar aiki da bin ƙa’ida, kuma ba za su yi sako-sako a kan wannan ba. Ko ma dai mene ne... [bidiyon ba su] dace da aƙidojin rundunar sojin Isra’ila da umarnin da ake bas u ba, kuma za a ɗauki matakan ladabtarwa – wannan ne tsarin rundunar tsaron Isra’ila."











