Maƙwabtakar Masallaci da Coci ta hada kan Musulmai da Kiristoci

Bayanan bidiyo, Yadda maƙwabtakar Masallaci da Coci ta kawo zaman lafiya tsakanin Musulmai da Kiristoci
Maƙwabtakar Masallaci da Coci ta hada kan Musulmai da Kiristoci

Da zarar ka ambaci sunan unguwar Bagobiri a birnin Calabar da ke jihar Cross River a kudancin Najeriya, to kowa ya san yadda Musulmai da Kirista a yankin suka yi fice kan zama lafiya da juna.

A wannan unguwar, akwai wani masallaci da coci da ke dab da juna, amma tsawon shekara 30 ba a taba jink ansu ba.

Masu ibada a wuraren biyu sukan yi harkar arziki tare su taimaka wa juna a lokutan da suka dace.

Hakan yakan bai wa mutane mamaki a ƙasa irin Najeriya da ta yi ƙaurin suna wajen rikicin addini tsakanin Musulmai da Kirista.

A wannan bidiyon, za ku ga yadda zamantakewarsu ke gudana.