Ana sukar “ɓarnar kuɗin da aka yi” wajen gina masallaci a Masar

Asalin hoton, ALAMY/REUTERS
Masar ta buɗe wani katafaren masallaci da ya kafa tarihi ta fannoni da dama, kuma ya kasance na biyu mafi girma yanzu a Afirka, a sabon babban birnin ƙasar.
Sai dai kuma jama'a na ta suka a kan yawan kudin da aka kashe.
Gwamnatin ƙasar tana gina sabon birnin mulki ne a tsakiyar hamada, a wani wuri mai nisan kilomita 45, gabas da Alkahira, don rage yawan mutane daga babban birnin na yanzu wanda ya cika ya batse da jama'a.
Sai dai kuma buɗe sabon masallacin tare da wata babbar cibiyar harkokin Musulunci ya janyo ce-ce-ku-ce, da suka daga mutane da dama a shafukan sada zumunta da muhawara.
Jama'a na kokawa da gine-ginen saboda ɗumbin kudin da aka kashe yayin da ƙasar ke fama da hauhawar farashin kaya da na ayyuka, inda lamarin ya wuce kashi 30 cikin ɗari a watan Maris ɗin nan.
Sabuwar cibiyar harkokin Musuluncin wadda ta ƙunshi katafaren masallacin tana da faɗin murabba'in mita 19,000, kuma za ta iya ɗaukar masu ibada 107,000.
An kashe fam ɗin Masar miliyan 800, kwatankwacin dala miliyan 25.9, wajen gina masallacin wanda a yanzu shi ne na biyu mafi girma a Afirka, bayan Djamaa el Djazaïr da ke babban birnin Algeria, Algiers.
Kafar yaɗa labarai ta gwamnatin Masar ta bayyana cewa masallacin ya zama na ɗaya yanzu a fannoni uku a tsakanin masallatai na duniya.
Abu na farko shi ne mumbarinsa mafi tsawo yanzu a duniya, inda yake da tsawon mita 16.6 wato ƙafa 54 da rabi, kuma an yi mumbarin ne da wani itace mai kyau sosai
Abu na biyu da na uku, da masallacin ya zarce sauran masallatan duniya su ne fitilarsa ta rataye da ke tsakiyar ƙwaryar masallacin irin mai adon nan, ita ce mafi nauyi a duniya, inda ta kai nauyin kilogram 24,300, kuma ita ce mafi girma, da tsawon tsakiyarta ya kai kafa 72.2, sannan tana da hawa hudu.
Shugaban Masar Abdul Fattah al-Sisi, ya halarci bikin buɗe masallacin, wanda kafar yaɗa labaran ƙasar ta bayyana a matsayin ''Tsabar Gwanintar Masar''.
Daidai lokacin da a ɗaya bangaren ake ta suka a shafukan sada zumunta da muhawara kan aikin ginin cibiyar da kuma masallacin, ganin ɗumbin kudin da aka kashe.

Asalin hoton, Reuters
Masar na fama da gagarumar matsalar tattalin arziki, kasancewar kudinta ya rasa kusan rabin darajarsa a kan dalar Amurka a cikin shekara, wanda hakan ya sa hauhawar farashin kaya da ayyuka ta kai kololuwar da ba ta taɓa kaiwa ba a cikin shekara biyar.
Haka kuma kasar na sayar da kadarorinta ga 'yan kasuwa masu zuba jari na yankin tekun Fasha, domin ta samu kudin da za ta cike wagegen gibin kasafin kudinta.
Mutane da dama sun riƙa sukar hukumomin ƙasar a shafukan Twitter da Facebook, kan yadda suka ce tana kashe kuɗi a kan wuraren addini cikin wannan lokaci mai tsanani da miliyoyin Misirawa ke fama kafin su samu abin da za su ci.
Wani da ya yi rubutu a Facebook, kan abin da ya bayyana da ɓarnar kuɗin da gwamnati ta yi a masallacin, cewa ya yi a sayar da fitilar ratayen da kuma mumbarin da ma masallacin gaba ɗaya, idan hakan zai iya magance matsalar da ake ciki.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Wani kuma cewa ya yi a rufe masallacin duk tsawon shekara, a rika bude shi duk bayan wata uku, saboda mutane dari daya su yi amfani da shi, sai kuma a sake rufe shi.
Shi kuma wani suka ya yi kan makudan kudaden da gwamnati ke kashewa a manyan ayyuka.
Yana cewa,''to me za mu yi da mutanen da ba su da abin da za su ci ko matasan da ba za su iya aure ba? Ba matsala. Muna da masallaci mafi girma, fitalar kawa ta masallaci wadda ta fi nauyi da kuma bashin waje mafi girma wanda za mu ci gaba da biya har ranar tashin kiyama.''
Shugaba Sisi wanda ya jagoranci sojoji suka hambarar da wanda ya gada Mohammed Morsi, a 2013 sakamakon zang-zanga a kan gwamnatin marigayin ya yaba wa wadanda suka halarci bikin bude masallacin da sauran jama'a a wurin wanda firaministan kasar shi ma ya halarta.
Kakakinsa ya rika sanya hotuna na shugaban a wurin bikin a shafukan intanet, abin da kafafaen yada labarai na kasar suka bayyana da kaddamar da sabuwar jamhuriyya.











