'Nutso na riƙa yi don ceto mutanen da ruwa ya cinye gidajensu a Legas'

Wani mutum kenan ke ƙoƙarin isa shagonsa da ruwa ya cinye

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Legas ta kasance jihar da ta yi makwabtaka da ruwan tekun Atlantic da koguna da ƙoramu da kuma tafkuna
    • Marubuci, Kareemot Salami and Kelechi Anozia
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
    • Aiko rahoto daga, Lagos
  • Lokacin karatu: Minti 4

Koyaushe ruwan sama, in ji Francis Okotieboh mai shekara 50 da ke cikin fargaba.

Cikin shekarun da suka gabata, mazauna Oke Ishagun, wata unguwa mai cike da cunkoson jama'a a jihar Legas, ta fuskanci ƙaruwar ambaliya a baya-bayan nan.

“Cikin ruwa na riƙa yin iyo, ina jefa rayuwata cikin hatsari, domin ceto mutanen da ruwa ya cinye gidajensu,'' in ji shi.

Yanayin ya yi matuƙar munana, ta yadda Okotieboh ya rasa duka abubuwan da ya mallaka.

''Na rasa komai da na mallaka,'' in j shi.

“Talbijin ɗina da kujerun ɗakina da firinjina da komai. babu abin da ya rage min sai gado da wasu tsummokarana da ke kan gadona''.

''Abin da nake yi yanzu idan na tashi daga barci shi ne na yi wanka na zo wajen aiki''. Wanan shi ne halin da mafi yawan al'ummar unguwar Oke Ishaun ke gudanar da rayuwarsu''.

Francis Okotieboh ya rasa duka abn da ya mallaka sakamakon ambaliyar
Bayanan hoto, Francis Okotieboh ya rasa duka abin da ya mallaka sakamakon ambaliyar

Yawan aukuwar ambaliya

Legas, birnin da ke da ingantaccen tsarin makamashi, na fama da matsalar ambaliya a shekarun baya-bayan nan.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ƙaruwar ruwan saman da ake samu a shekara na ƙara haifar da hatsarin kwararar ruwan zuwa wasu unguwanni, lamarin da zai iya haifar da nutsewar wasu unguwannin birnin.

Ambaliyar ta baya-bayan nan ta haifar da asarar rayuka da dukiyoyin al'umma.

Lagos mai mazauna miliyan 21, da dama daga cikinsu na zaune a unguwanni masu cunkuso da ba hukuma ce ta tsara su ba.

Jihar Legas na yankin da ruwa ya zagaye da suka ƙunshi ƙoramu da tafkuna da kogunan da ke kwarara zuwa tekun Atlantica.

Wasu gidaje ko unguwannin ƙasar na kusa da ruwa.

A watan Janairu, Ofishin kula da ayyukan jinƙai na Majalisar Dinkin Duniya, ya wallafa wani ƙwarya-ƙwaryar bincike da ya gano cewa babu wasu mataai da ake ɗauka na rage hatsarin ambaliyar a birnin wanda ke cikin hatsarin nutsewa nan da 2050.

“Legas da kuma yankin Niger Delta sun kasance a kwari, lamarin da ke ambaliya sauƙin auka musu, saboda yawan ƙoramu d arafuka da tafkuna da kogunan da suka kewaysu'', in ji rahoton.

A cikin gomman shekarun da suka wuce, samun ƙaruwar gine-gine cikin sauri, haɗe da rashin bin cikakken tsarin gine-gine, ya sa legas ta ƙara kusantar gaɓar ruwa.

Wannan ya rage ƙarfin magudanan ruwa, lamarin da ya sa birnin ke ƙara shiga hatsarin ambaliya.

“Magana dta gaskiya ina ganin matsalar Legas ta daban ce. Akwai matsalar rashin ingantaccen tsarin kwalbatoci, haka kuma akwai batun matsalar shara,'' in ji Mustapha Ewenla, wani ƙwararre kan tsara birane.

“Sauyin yanayi na daga cikin manyan matsaloli. Muna ganin sauye-sauyen yanayi, ciki har da mamakon ruwan sama, wanda ke yi wa magunan ruwa barazana'', in ji shi.

Tsarin magudanan ruwan birnin ba shi da ƙarfin da zai iya daƙile ƙaruwar yawan ruwan saman da sauyin yanayi ya haddasa.

Tsufan fayif da toshewar magunan ruwa da rashin sarrafa ruwan da ke tsaye sun munana matsalar.

Ƙungiyar bayar da agaji ta Red Cross ta ce ta gudanar da ayyukan jin ƙai masu yawa ga mutanen da wata masifar ƙaddara kamar abaliya ruwa ta shafa a Legas da wasu sassan Najeriya.

Ige Oladimeji, shugaban sashen daƙile aukuwar bala'o'i na ƙungiyar Red Cross a Legas ya ce a wannan shekarar kaɗai ƙungiyarsu ta tallafa wa fiye da iyalai 200 da ambaliya ta haifar wa matsaloli.

“A wannan shekara, gidje da dama sun ruguje,'' in ji shi.

“Mun koya wa mutanen wasu garuruwa yadda za su taftace muhallansu , sanna muka tallafa musu da wuraren wanke hannu da wayar da kai da tallafin kuɗi''

A woman walks through flooded back streets in a Lagos suburb

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A watan Janairu, wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya kan sauyin yanayi ya nuna cewa birnin Legas na cikin hatsarin nutsewa nan da 2050.

Magance magudanun ruwa

Masanin tsarin birane, Mustapha Ewenla ya ce ana buƙatar ɗaukar mata daban-daban domin magance matsalar ambaliya a jihar.

“Yana da kyau gwamnati ta ƙara ƙoƙarin faɗaɗa gine-ginen magudanun ruwa tare da hna mutane gini a kusa da hanyoyin ruwa,'' in ji shi.

To sai dai gwamnati na cewa ta magance matsalar, bayan da aka samu ci gaba a shekarun baya-bayan nan.

“Legas na tattare da wasu ƙalubale masu tarin yawa, kasancewar tana gaɓar ruwa ta kuma yi iyaka da tekun Atalantica, da koguna da tafkuna,'' in ji kwamishinan muhalli na jihar, Tokunbo Wahab.

“Mutane sun jima suna ɗaukar doka da hannunsu wajen datse hanyoyin ruwa wajen gina gidajensu, wanda kuma na daga cikin dalilan da ke haddasa ambaliyar'', in ji shi.

“Amma abin da muka yi cikin shekara guda da ta gabata shi ne mun tabbatar da duk inda aka datse hanyar ruwa an buɗe ta''.

Kwamishinan muhalli da albarkatun ruwa na jihar Legas, Tokunbo Wahab
Bayanan hoto, Kwamishinan muhalli da albarkatun ruwa na jihar Legas, Tokunbo Wahab

Kwamishinan tsara birane na jihar Legas, Oluyinka Olumide, ya ce gwamnati ta mayar da hankali wajen samar da ayyukan da za su magance ambaliya.

“An yashe duka magudanun ruwa masu matsala. A yanzu mu fito da wani tsari na sai mun takardar amincewa ga duk wanda zai yi gini a yankin,'' in ji shi.

Ya ƙara da cewa ofishinsa na tabbatar da cewa ba a bayar da takardar amincewa ga masu gini a kan hanyoyin ruwa ba, ta hanyar aiki hukumomi da ƙungiyoyin cikin gida da na waje.

A yayin da Legas ke ci gaba da bunƙasa, masana sun amince cewa yana da matuƙa muhimmanci a fifita gine-ginen da za su jure wa sauyin yanayi.

“Idan za mu ɗauki matakan da suka dace, za mu iya magance matsalolin da ke damunmu, sannu a hankali,'' in ji shi.

A gidan wani makwabcinsa da ke unguwar Oke Ishagun, Francis Okotieboh na fatan gwamnati za ta yi duk abin da ya kamata domin kare rayuka da dukiyoyin jama'ar yankin.

“Muna fatan magance matsalar ambaliya ta dindindin a jihar Legas,'' in ji shi.