Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Waɗanne hanyoyi Najeriya za ta bi don kawar da matsalar yunwa a Arewa?
Shirin bayar da tallafin abinci na Majalisar Dinkin Duniya a arewa maso gabashin Najeriya ya zo ƙarshe.
Haka nan ƙungiyar likitoci masu bayar da agaji ta Medecins Sans Frontieres ta yi gargaɗin cewa za a samu mace-macen dubban yara a arewa saboda ƙarancin abinci mai gina jiki matuƙar ba a kai ɗaukin gaggawa ba.
A cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar ranar 25 ga watan Yuli, ta ce "a halin yanzu arewacin Najeriya na fuskantar mummunar matsalar ƙarancin abinci".
Sanarwar ta ƙara da cewa a misali, "tun daga 2021 da MSF ke aiki a jihar Katsina, tana ganin yadda ake kawo ƙarin yara da ke cikin matsananciyar yunwa kuma ake samun ƙaruwar mace-mace sanadiyyar ƙarancin abinci mai gina jiki."
"Zuwa ƙarshen watan Yunin 2025, kimanin yara masu fama da tamowa 70,000 ne suka karɓi magani a hannun jami'anmu a Katsina, ciki har da yara 10,000 da aka kwantar a asibiti a cikin matsanancin hali," a cewar MSF.
A fadin arewacin Najeriya yunwa na addabar al'umma sanadiyyar tashe-tashen hankali da kuma rashin ƙarfin tattalin arziƙi.
Rikicin Boko Haram wanda ya tarwatsa miliyoyin mutane a yankin tafkin Chadi na ci gaba da hana manoma noma gonakinsu da kuma ayyukan kamun kifi, inda mutane da dama ke zaune a wasu sansanonin da aka tanada, suna dogaro da tallafi ƙungiyoyin bayar da agaji.
A jihohin arewa ,maso yammacin ƙasar kuwa rikicin ƴan fashin daji masu garkuwa da mutane ya haifar da asarar rayuka masu ɗimbin yawa da tarwatsa ƙauyuka da dama waɗanda suka dogara kan ayyulka na noma da kiwo.
A yanzu da ƙungiyar WFP ta dakatar da bayar da agaji a arewa maso gabas, ana bayyana fargabar cewa lamarin zai ƙara jefa mutane cikin bala'i da kuma ta'azzara rashin zaman lafiya.
"Dakatar da tallafin da ake bai wa mutane zai saka 'yan Boko Haram su rinjayi matasa su shiga kungiyar, cikin sauƙi wanda hakan zai ƙara haddasa rashin tsaro a ɗaukacin yankin," in ji Trust Mlambo, shugaban ayyuka a yankin daga WFP, yayin zantawa da BBC.
Mece ce mafita ga Najeriya?
Hussaini Abdu, masani kan tattalin arziƙi da taimakon gaggawa a Afirka ya ce yanayin na da ban-tsoro, sai dai ya ce akwai hanyoyin wucin-gadi da kuma na dindindin da Najeriya za ta iya bi wajen shawo kan matsalar.
Hanyoyin wucin-gadin su ne:
Cike gurbin kuɗin tallafi
Mataki na farko da Dakta Hussaini Abdu ke ganin ya kamata ƙasar ta ɗauka shi ne "fahimtar giɓin da za a samu sannan a yi ƙoƙarin cikewa, wato a ware kudaden da za su cike giɓin da za a samu" sanadiyyar dakatar da tallafin da ƙungiyoyi ke bayarwa.
To amma tambayar ita ce: Ko Najeriya za ta iya cike wannan giɓi?
Miliyoyin daloli ne hukumin agaji ke narkarwa wajen samar da tallafi a arewacin Najeriya domin samar da sauƙi ga al'ummar da rikice-rikice suka tarwatsa.
A watan Janairun 2025, Hukumar bayar da agajin jin-ƙai ta Majalisar Dinkin Duniya (OCHA) ta bayyana cewa ana buƙatar jimillar kuɗi sama da dala miliyan 910 domin tallafa wa mutane miliyan 3.6 da ke neman agajin ceton rai a arewa maso gabashin Najeriya.
Jihohin su ne Borno da Adamawa da kuma Yobe, inda ta ce "jimillar mutum miliyan 7.8 ne ke neman agaji."
Hussaini Abdu ya ce: "Abu ne mai wahala saboda ba ƙananan kuɗade ne ake kashewa ba."
Ƙoƙon bara na diflomasiyya
Wata hanyar da masanin ke ganin Najeriya za ta iya bi ita ce ta neman tallafi daga ƙungiyoyi da kuma ƙasashen duniya, duk da cewa abu ne da yawancin ƙasashe ba su cika son yi ba.
Dakta Abdu ya ce "gwamnatin Najeriya ta yi amfani da ƙarfinta na diflomasiyya wajen neman ƙasashe da ƙungiyoyi su ƙara ƙaimi wajen bayar da tallafi.
"Idan kana cikin wani hali, dole ne ka nemi taimako," in ji masanin.
Ya kuma ƙara da cewa za a iya sauya akalar kudin da ake kashewa wajen gina gadoji, zuwa ɓangaren yaƙi da yunwa.
To amma waɗanne matakai ne na dindindin da Najeriyar za ta iya ɗauka wajen kawar da yunwa?
Magance matsalar tsaro
"Dama abubuwan da ke hana manoma zuwa gonaki a wannan hali shi ne rashin tsaro," in ji Hussaini Abdu.
"A yi maganin rashin tsaro da ya addabi al'umma, musamman a arewacin Najeriya inda ake yaƙi da ƴan bidiga a gabashi da yammaci da kuma tsakiyar arewacin Najeriya".
Baya ga matsalar Boko Haram a arewa maso gabas da ta ƴan fashin daji a arewa maso yamma, a arewa ta tsakiyar Najeriya ma ana fama da matsalar rikici mai nasaba da ƙabilanci da kuma addini.
A baya-bayan nan hare-hare da aka kai a jihohin Benue da Filato sun haifar da asarar rayukar fiye da mutum 100.
Hare-haren baya-bayan nan biyu da aka kai ranar 13 da 14 ga watan Yuni sun tayar da hankalin ƴan ƙasar, lamarin da ya sa shugaban ƙasar Bola Tinubu ya bayar da umarnin gaggauta kawo ƙarshen rikicin.
To amma matsalar ita ce an shafe sama da shekara 15 yanzu haka ana fama da irin wadannan rikice-rikice da suka addabi yankin na arewacin Najeriya, duk kuwa da ƙoƙarin da gwamnati ta ce tana yi.
Hussaini Abdu ya ce wajibi ne sai Najeriya ta ɗauki ƙwararan matakai kafin ta samu nasarar kakkaɓe matsalar tsaro da ƙasar ke fuskanta.
Sauran abubuwan da masanin ya zayyana a matsayin mafita wajen daƙile matsalar yunwa a arewacin Najeriya su ne:
- Fadakar da al'umma kan amfani da abinci mai gina jiki
- Tallafa wa manoma
"Idan aka tallafa, manoma za su ci gaba da ƙoƙarin noman abincikn da ake buƙata, domin Najeriya na iya ciyar da kanta."