Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yarjeniyoyi huɗu da aka ƙulla tsakanin Nijar da Chadi
Shugaban ƙasar Chadi Mahamat Idriss Déby Itno ya kammala ziyarar wuni biyu da ya kai birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar.
Wannan ne karo na biyu da Deby ke kai ziyara Nijar tun bayan juyin mulkin da sojojin ƙasar suka yi wa gwamnatin Mohammed Bazoum a ranar 26 ga watan Yulin 2023.
A lokacin ziyarar ta Mahamat Deby, an ga yadda ya yi jerin ganawa tare da shugaban Nijar Abdourahamane Tiani, inda aka cimma yarjeniyoyi da dama.
Muhimman abubuwan da suka cimmawa a lokacin wannan ziyara su ne:
- Zirga-zirgar al'umma tsakanin ƙasashen ba tare da wani shinge ba
- Samar da bututun man fetur daga Nijar zuwa Chadi
Baya ga wadannan, ƙasashen biyu sun tattauna kan batutuwa da dama da nufin ƙara haɗa kai wajen ganin an samu ci gaba mai ɗorewa, ganin cewa al'ummomin ƙasashen biyu sun daɗe suna kyakkyawar mu'amala:
Tallafa wa juna wajen yaki da ta'addanci
Shugabannin ƙasashen biyu sun ƙara nanata goyon baya ga ɓangaren tsaro, musamman wajen yaƙi da ta'addanci.
Sun yi na'am da irin haɗin-kai da ɓangarorin tsaronsu da kuma dakaru ke bayar wa - wanda ya sa aka samu nasarori da dama a yaƙi da ƙungiyoyi masu riƙe da makamai a yankin Tafkin Chadi.
Sun kuma bai wa ministocin tsaronsu da su shirya taro da ƙwararru a ɓangaren domin inganta tsare-tsare da ake yi wajen ƙarfafa matakan tsaro a yankunan.
Mayaƙa masu iƙirarin jihadi sun sha yi wa sojojin Nijar da kuma na Chadin kwantan-ɓauna, inda suke hallaka da dama a yawan lokuta - wani abu da masana ke kiran cewa idan ba a ɗauki mataki ba lamarin zai ƙara munana.
Zuba jari
Har ila yau, shugabannin sun amince cewa za su kyautata dangantaka domin bunƙasa harkokin kasuwanci tsakanin ƙasashen biyu (Nijar da Chadi) - wanda kafin a samu haka sai an samar da zaman lafiya, tsaro da kuma ci gaba, a cewarsu.
Sauran abubuwan da suka amince da su su ne:
- Rattaɓa hannu kan bunƙasa ɓangaren zuba jari
- Ƙarfafa haɗin-kai don yaƙi da kasuwanci na bogi
- Amfani da iyaƙokin ƙasar da suka dace don mu'amalar kasuwanci
- Ƙara wa matasa kwarin gwiwa don koyon sana'o'i da kuma bunƙasa masana'antu masu zaman kansu
Samar da bututun mai daga Nijar zuwa Chadi
A ɓangaren makamashi kuwa, ƙasashen na Chadi da Nijar sun amince da aiki tare don ganin an kammala aikin wutar Salkadamna, wanda ake sa ran zai iya samar da yawan megawat 5,200.
Nijar ɗin ta kuma amince don samarwa da takwararta ta Chadi da man dizel da ya kamata.
Suna kuma duba yiwuwar ganin an ƙarafafa hulɗar kasuwanci da za ta kai ga gina butun mai daga Nijar zuwa Chadi.
Ɓangaren siyasa da diflomasiyya
A ɓangaren siyasa da diflomasiyya kuwa, ƙasashen biyu sun yi maraba da batun aika manyan tawagogi domin tattaunawa kan batutuwa da suke damun ƙasashen da kuma yankin.
Sauran abubuwan da suka amince da su sun haɗa da:
- Nuna buƙatar ƙarfafa dangantakar siyasa, kimiyya, al'adu da kuma dukkan matakai
- Sun kuma amince cewa za a riƙa gudanar da zama a-kai-a-kai don tattauna matsaloli da suke damun ƙasashen - an gudanar da wanda ya wuce a Yamai, na gaba kuma za a yi ne a N'Djamena
- Sun ce ƴan ƙasashen biyu za su iya zirga-zirga a kowane lokaci ko ba tare da biza ba
- Nijar ta yi maraba da matakin Chadi na buɗe ofishin jakadanci a Diffa
- An bai wa ministocin harkokin wajen ƙasashen umarnin aiwatar da matakin ba da daɗe wa ba
Shugaban gwamnatin mulkin sojin ta Nijar, Janar Abdourahamane Tiani, ya gode wa shugaban na Chadi kan ziyarar da ya kai wa ƙasarsa.
Ana dai ganin ziyara za ta ƙara inganta dangantakar ƙasashen biyu - waɗanda ke fama da matsaloli da dama ciki har da rashin tsaro, inda mayaƙa ke kashe gomman mutane har ma da sojoji.