Yadda sabon harajin kunna janareta da sola ke tayar da ƙura a Nijar

Lokacin karatu: Minti 4

A Jamhuriyar Nijar, sanya haraji kan amfani da janareta da hasken rana wato sola na tayar da ƙura, inda ƴanƙasar da dama suka bayyana damuwa game da sabon matakin gwamnati, wanda masu fafutika suke ganin ya zo a lokacin da bai dace ba.

Wannan matakin gwamnatin da ta sanar cewa za kakkaɓe tsohuwar dokar harajin makamashi ta ƙasar domin fara karɓar haraji daga duk masu amfani da janareta da na'urorin hasken rana a gida ko wajen sana'a na zuwa ne a daidai lokacin da ƙasar ke fama da matsin tattalin arziki da ƙarancin wutar lantarki.

Masu ƙananan sana'o'i na ganin harajin a matsayin wani nauyi da bai dace a ɗora musu ba.

Al'umma da dama a Jamhuriyar Nijar sun koma amfani da hanyar samun lantarki ta hasken rana ko kuma na'urar janerata saboda tsananin ƙarancin wutar lantarki a baya-bayan nan.

Lamarin ya ƙara tabarɓarewa ne tun bayan tuntsurar da gwamnatin shugaban ƙasar Mohamed Bazoum, inda ƙasashen da ke maƙwaftaka da kasar suka ƙaƙaba mata takunkumai.

Gwamnatin mulkin sojin ƙasar ta bayar a wa'adin zuwa ƙarshen wannan watan ga mutanen ƙasar ciki har da masu manyan gine-gine da kamfanoni da ɗaiɗaikun mutane da su fara biyan haraji ko kuma su fuskanci fushin hukuma.

Me dokar hareje-haren ta ce?

A shekarar 2018 ce gwamnatin tsohon shugaban ƙasar, Mahamadou Issoufou ta fito da waɗannan haraje-haraje, sai dai ƙungiyoyin fararen hula sun shafe watanni suna zanga-zangar nuna rashin amincewa da ita.

Sai dai wannan gwamnatin ta yanzu ta ɗauki matakin karkaɗewa tare da dawo da batun.

A wasu takardun umarni daga ma'aikatar tattalin arzikin ƙasar, waɗanda babban daraktan sashen haraji na gwamnatin ƙasar Abdourahamane Malam Saley ya sanya wa hannu ne suka bayyana waɗannan matakan.

Ɗaya daga cikin takardun na cewa: Ana "tunatar da ƴanƙasar masu amfani da hanyar samar da lantarki ta ƙashin kansu cewa dole su biya ragowar harajin gidaje kafin 30 ga watan Yunin 2025 kamar yadda sashe na 1085 na kundin harajin ƙasar ya tanada".

A wata takardar kuma, hukumar harajin cewa ta yi tana tunatar da ƴan ƙasar cewa, "za a rufe karɓar harajin da ake kira Professional Lease Income Tax (IRBP) a ranar 30 ga Yuni."

Haka kuma wata takardar ta ce, "muna tunatar da masu biyan haraji cewa dole su biya ragowar harajin gine-ginensu kafin ranar 30 ga Yunin 2025 kamar yadda dokokin ƙasar suka tanada."

Haka kuma wata wasiƙar ta yi kira ga "ƴan ƙasar masu bayar da haya da su biya haraji kafin ranar 30 ga watan Yunin 2025."

A duk wasiƙun, gwamnatin ta bayyana cewa saɓa dokokin zai sa mutum ya fuskanci fushin hukuma, kamar yadda dokokin ƙasar suka tanada ga waɗanda suka saɓa dokar harajin ƙasar.

Abin da ƴan ƙasar suke cewa

Wani mai aikin hannu ne da ke amfani da janareta domin samun lantarki, a zantawarsa da BBC ya ce bai dace a ƙara musu haraji ba ɗoriya a kan waɗanda suke biya.

A cewarsa, "abubuwa ne da talakawa suke amfani da su saboda halin da ake ciki na ƙunci da damuwa a ɓangaren makamashi. Wani lokacin idan ma an samu aikin, sai mutane su ƙi zuwa karɓa saboda halin da ake ciki a matsin tattalin arziki.

"Yanzu haka a wurinmu akwai kayan da suka kai shekara biyu ba a zo an karɓa ba, ko kuma a zo a karɓa ba a iya ba. Sannan a haka kuma a zo a ƙara mana haraji!" in ji shi, inda ya ƙara da cewa amma dama can suna biyan haraji na gwamnati.

A game da batun cewa gwamnati ta ɗauki wannan matakin ne domin samun kuɗaɗen gudanar da aikace-aikace, sai Lawali ya ce zai fi dacewa a duba wasu hanyoyi, ba takura wa talakawa ba.

"A sake shawara a nemo manyan hanyoyin samun kuɗin shiga, amma yawan ɗaura wa talakawa haraji musamman ca ikin halin da ake ciki yana iya kawo matsala."

A nasa ɓangaren, wani ɗan fafutikar kare haƙƙin ɗan'adam, Ahmadu Ɗankwari a ƙasar ya ce, "ta wane hanya suka bi wajen ƙididdige mutanen da suke amfani da janareta da sola ɗin da za su biya harajin. Kowa ya san muna cikin ƙangi a wannan ƙasar. Yanzu kuma wanda ya ɗan samu hali ya sanya sola don ya riƙa ganin haske sai a tilasta shi ya biya haraji?"

A wasu sassan birane da karkara, ana gudanar da zanga-zanga cikin lumana, yayin da masu ruwa da tsaki ke bukatar a soke harajin ko a sake duba yadda za a aiwatar da shi ba tare da cutar da talakawa ba.

Wannan lamari na iya zama wata jarabawa ga gwamnatin Nijar dangane da yadda take mu'amala da matsalolin tattalin arziki da bukatun al'ummarta.