Wadanne abubuwa za a tattauna a haduwar Putin da Xi Jinping?

Asalin hoton, AFP
Shugaban Rasha Vladimir Putin da takwaransa na China Xi Jinping za su gana a wannan makon, a wani taro da za a yi a Uzbekistan.
Shugabannin Indiya da Pakistan da Turkiyya da Iran da sauransu su ma za su hadu a taron na Shanghai Cooperation Organisation (SCO) a birnin Samarkand daga ranar 15-16 ga watan Satumba, amma fadar Kremlin ta bayyana haduwar Putin da shugaban China a matsayin ''mai muhimmanci.''
Shugabannin biyu sun yi haduwar karshe ne a gasar Olympics ta hunturu da aka yi a Beijing cikin watan Fabrairu, a lokacin da suka fitar da sanarwar hadin gwuiwa cewa dangantaka tsakanin kasashen biyu ba ta da ''iyaka''.
Jim kadan kuma bayan haka ne Rasha ta kutsa Ukraine.
Shin ko abubuwa sun sauya?
BBC ta yi duba kan abin da Moscow ke bukata a wannan haduwa, da kuma abin da Beijing za ta nema daga haduwar.
Ga Shugaba Putin, alaka mai karfi da Beijing na daga cikin abubuwan da yake da buri a yanayin da ya samu kansa, don alakar Rasha da China ka iya kawo cikas ga karfin fada a jin Kasashen Yamma.
Wannan shiri ne da Putin ya dade yana son ganin ya aiwatar, amma babu wani lokaci da ya kamata Kremlin ta samu biyan wannan bukata kamar a yanzu.
Bayan Vladimir Putin ya kutsa Ukraine, ya fuskanci takunkumi da kauracewa daga kasashen Yamma, saboda haka yana da muradin ganawa da shugabannin duniya masu karfin fada a ji kamar Xi Jinping.
Sai dai bukatar ganawa da Shugaban China da Putin ke yi ta wuce ta haduwar ido-da-ido kawai.

Asalin hoton, AFP
Na farko yana so yaga China ta zuba jari a kasarsa, ta kuma habaka fasahar zamani da kulla yarjejeniyar kasuwanci, la'akari da takunkumin da aka kakaba masa kan yakin Ukraine.
Bayan ficewar kamfanoni kasashen Yamma, Vladimir Putin na son ganin ya maye gurbinsu da na China.
Irin yadda Kasashen Yamma ke son rage dogaro da mai da gas din Rasha, Moscow za ta so ta mayar da kasuwarta China.
Bugu da kari Moscow na son makamai daga Beijing musamman saboda yakin da take yi a Ukraine, to amma babu alamun China ta shirya taimaka mata ta wannan fannin.

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Tafiyar Xi Jinping zuwa Uzbekistan da Kazakhstan ita ce balaguronsa na farko kasashen waje tun bayan bullor cutar korona a 2020.
Tana kuma zuwa yayin da ake shirin gudanar da babban taron jam'iyyar Chinese Communist Party (CCP) a ranar 16 ga watan Oktober, in, inda ake sa ran sake zabar Xi a karo na uku.
Duk da har yanzu kafar yada labaran kasa a China ba ta bada cikakken bayani kan haduwar shugaban da Putin ba, Taiwan da Hong Kong na kallon halartar Xi wannan taro, a matsayin wata farfaganda ta nuna wa duniya cewa yana da cikakken iko da kasarsa.
A baya bayannan babban jami'in huldar diflomasiyya a China Yang Jiechi, ya bayyana irin goyon bayan da Beijing ke bai wa Moscow, a taronsu da jakada mai barin gado Andrey Denisov.
Sai dai Beijing na taka tsantsan kan wurin ganin ta zama yar ba ruwanmu a yakin Ukraine. Tana neman goyon bayan Moscow a halin da ta samu kanta na tsamin dangantaka da kasashen Yamma, amma kuma ba ta son matse wa Putin.
A yanzu da yakin Ukraine ke bai wa Putin ruwa, da kuma bukatar wasu mabiya Twitter a Rasha na ya yi murabus, Za a sa ido sosai don ganin yadda ganawar shi da Xi za ta kasance.
Shin ko Xi zai nesanta kansa daga shugaban Rashar, ko kuma zai bashi hadin kai, don gudun kar ya samu kansa a yanayin fuskantar kauracewa mai muni idan har aka kawar da Putin?











