China da Rasha sun ƙi yarda da Amurka kan sanya wa Koriya ta Arewa takunkumi

Asalin hoton, Reuters
China da Rasha sun yi watsi da kiran da Amurka ta yi musu na bayar da goyon bayan kara sanya wa Koriya ta Arewa takunkumi saboda shirinta na manyan makamaki masu linzami.
A yayin taron kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya, Larabar nan, Amurka ta ce muddin aka bar kasar ta ci gaba da kera makman ba tare da an hukunta ta ba, to hakan tamkar izini ne aka ba ta ta ci gaba da gwajin.
Wannan bukata da Amurkar ta gabatar ta neman taka wa Koriya ta Arewa birki a kan shirinta na kera makamai masu linzami, ya biyo bayan yadda Koriyar musamman a baya bayan nan ta shiga gwajin irin wadannana manyan makaman masu linzami kusan ba kakkautawa wani bayan wani abin da ke zaman wata fargaba ga makwabciyarta Koriya ta Kudu, kawa ga Amurka.

Asalin hoton, Google
Manyan kasashen biyu China da Rasha, ba ma sun ki mara wa Amurka baya ba ne a kan wannan kuduri nata na neman dakatar da Pyongyang daga gwajin makaman, ta hanyar kara mata karin takunkumi ba, maimakon haka sun ma nemi da a sassauta mata wadanda aka sanya mata ne bisa abin da suka ce dalilai na jin-kai.
Da take kokarin shawo kan mambobin kwamitin na tsaro kan su bayar da goyon baya ga bukatar ta Amurka, jakadiyar kasar a Majalisar Dinkin Duniya, Linda Thomas-Greenfield, ta nemi shawo kan yan kwamitin ta hanyar nuna muhimmancin tafiya tare ba tare kuma da bata lokaci ba kann muradin.
Ta ce ''A yi magana a yanzu da kakkarfa kuma hadaddiyar murya wajen suka da yin Allah-wadarai da halayyar Koriya ta Arewa.
Muna bukatar ɗaukar mataki a yanzu domin hana ci gaba da samar da makaman da suka saba ka'ida kafin a makara.
Muna karfafa wa dukkanin mambobin kwamitin da su bayar da goyon baya ga shawararmu, tare kuma da nuna cewa kwamitin tsaron zai mayar da martini ga barazanar da ake yi wa zaman lafiya da tsaro na duniya da kuma keta dokokinsa karara."
Ita kuwa China tare da Rasha wadanda suka ki matakin na Amurk tare da neman akasinsa, wato dage wa Koriya ta Arewar takunkumin da aka sanya mata tun a baya, sun nuna cewa bukatar ta Amurka, ba shawara ce da ta dace ba, wajen hana kera makaman, kamar yadda jakadan China a Majalisar ta dinkin duniya Zhang Jun ya nuna:
Ya ce "Wannan sabuwar shawara da Amurka ta kawo ta yin amfani da babi na bakwai na dokokin na Majalisar Dinkin Duniya ta ta'allaka ne a kan sanya Karin takunkumi, wanda hakan ba hanya ce da ta dace ba wajen shawo kan lamarin na yanzu a wannan yanki.
Abin takaicin shi ne Amurka ta rufe ido ta kawar da kai ga shawara da ta dace da sauran mambobi masu ruwa da tsaki suka gabatar ta bayar da fifiko a kan tasirin sanya takunkumi da take gani.
Mun yi amanna cewa Amurka za ta sauya wannan dabi'a tata. Abu ne da zai iya yuwuwa mambobin su cimma matsaya. Muna fatan mambobin kwamitin za su yi tunani su amince da shawarwarin hadin guiwa na China da Rasha.''
Mambobin kwmitin tsaron dai su goma sha biyar sun rabu kan yadda za a bullowa batun gwajin makaman na Koriya ta Arewa, tun bayan da kwmitin ya tsaurara takunkumin da ya sanya wa kasar a shekara ta 2017.
Zuwa yanzu dai gwamnatin Koriya ta Arewar ta yi gwajin sabbin makamai masu linzami 17 a shekarar nan, abin da ya zarta wanda ta yi jumulla shekara biyu da ta wuce.











