Koriya Ta Arewa: Amurka ta tura manzon musamman Koriya Ta Arewa ya je ya jiyo dalilin harba makamai

Kim Jong Un

Asalin hoton, Google

Bayanan hoto, Shugaba Biden da Kim Jon Un

Wakilin Amurka a Koriya ta Arewa, Sung Kim, ya isa yankin domin tattauna gwajin makami mai linzami da Pyongyang ta yi a baya-bayan nan.

Ya je birnin Seoul ne domin ganawa da jami'an Koriya ta Kudu, ciki har da wakilin kasar kan nukiliya Noh Kyu-duk.

Ana kuma sa ran zai tattauna da wakilan shugaban kasa mai jiran gado, Yoon Suk-yeol, wanda zai hau karagar mulki a wata mai zuwa.

A ranar Asabar ne Koriya ta Arewa ta gwada wani makami mai cin gajeren zango wanda ake kyautata zaton an kera shi ne domin daukar wani makamin nukiliya.

Bayanan bidiyo, Wace ce Kim Yo-jong, 'ɓoyayyiyar ƙanwar' shugaban Koriya ta Arewa Kim Jung-un?