Kim Jong-un: Me ya sa shugaban Koriya ta Arewa ya rame?

Asalin hoton, EPA/KCNA
- Marubuci, Daga Alistair Coleman
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Monitoring
Kafar watsa labaran Koriya ta Arewa ta wallafa bidiyon wani dan kasar yana nuna damuwarsa kan "rame sosai" da shugabansu Kim Jong-un ya yi.
Batun lafiyar shugaban kasar ba abu ne da ake tattaunawa a bainar jama'a ba a kasar da kafafen watsa labaranta suke sirrinta abubuwan da suka shafe shi.
Kazalika gidan talbijin na kasar ya wallafa bidiyon Mr Kim wanda ya nuna shi a rame idan aka kwatanta da yadda yake a shekarun baya bayan nan.

Asalin hoton, Reuters
Ana ta yada jita-jita kan yanayin lafiyar shugaban na Koriya ta Arewa tun da ya hau kan mulki a kusan shekaru goma da suka gabata, amma ba kasafai gwamnatin kasar da ke komai cikin matukar sirri take tabbatar da hakan ba.
Me 'yan kasar Koriya Ta Arewa suka gani a talbijin?
Bidiyo guda biyu da babban gidan talbijin na kasar, Korea Central Television, ya nuna, sun tayar da hankalin 'yan kasar game da halin koshin lafiyar shugabansu.
Daya daga cikin bidiyon ya nuna shi a rame sosai lokacin da yake isa wurin wani bikin rawa.

Asalin hoton, Korea Central TV
Bidiyo na biyu - wanda ba kasafai ake fitarwa ba - ya nuna wani mazaunin birnin Pyongyang da ba a fadi sunansa ba yana shaida wa labaran Central TV ranar Juma'a cewa: "Ganin [Mr Kim] a rame kamar haka ya sanya dukkanmu mun fada halin bakin ciki."
"Kowa ya soma kuka," a cewarsa.
Hotuna da bidiyon da aka dauka a lokacin taron jam'iyyar Workers Party a watan nan sun nuna Mr Kim ya rame.
A sharhin da shafin intanet na NK News ya yi ya bayyana cewa an matse igiyar da ke jikin agogonsa mai matukar tsada a lokacin da ya halarci wurin bikin rawar, abin da ke nuna cewa ya rame sosai.
Har yanzu ba mu san dalilin da ya sa aka fitar da bidiyon dan kasar ta Koriya Ta Arewa wanda ya nuna damuwarsa kan ramewar Mr Kim ba.
Sai dai But Kwak Gil Seob, wanda ke shugabancin shafin intanet na One Korea Center, wanda ya yi shura kan harkokin Koriya Ta Arewa, ya shaida wa BBC cewa gwamnatin kasar "ba za ta taba yarda a watsa labaran da ba za su yi wa Kim Jong-un dadi ba" - ma'ana an watsa bidiyon ne "domin nuna cewa shi da kansa Kim Jong-un ne yake rage kibarsa".
Me ya sa wannan batu yake da muhimmanci?
Batun koshin lafiyar Mr Kim abu ne da ya rika jan hankalin 'yan kasar Koriya Ta Arewa tun da ya zama shugaban kasa.
Ya gaji mahaifinsa Kim Jong-il a watan Disambar 2011 kuma masu lura da lamuran Koriya Ta Arewa sun ga yadda yake kara kiba tun da ya hau kan mulki.
Mr Kim yana cikin jikokin Kim da ya zama shugaban kasar, kuma ana kallon Koriya Ta Arewa a matsayin kasar da ake mulki bisa gado.
Babu tabbacin wanda zai gaji Kim Jong-un kuma mutuwarsa ko kuma rashin lafiyar da za ta hana shi iya gudanar da mulki tana iya haifar da gibi a kasar, lamarin da zai haifar da zaman zulumi a Gabashin East Asiya.
Ana hasashen cewa idan aka ayyana Kim Yo-jong a matsayin wadda ba ta dace ta gaje shi ba, mulkin kasar zai iya fita daga hannun zuriyar Kim a karon farko.











