Shugaban Koriya: Ta Arewa Kim Jong-un ya fito bainar jama'a

North Korea's leader Kim Jong-un pictured by state media opening a fertiliser factory on 1 May 2020

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Kafar yada labaran kasar ta saki wannan hoton a ranar Juma'a inda ta ce Kim e a yayin bude kamfanin taki

Kim Jong-un ya bayyana a bainar jama'a a karon farko bayan kwana 20, kamar yadda kafar yada labaran gwamnatin kasar ta ce.

Kamfanin dillancin labaran kasar na KCNA ya ruwaito cewa shugaban Koriya Ta Arewan ya yanke kyalle a yayin bude kamfanin taki.

Ya kara da cewa mutanen da suke kamfanin sun barke da sowa da tafi a lokacin da ya bayyana ranar Juma'a.

Bayyanar tasa - ta farko a kafar talbijin din kasar tun bayan ganinsa ranar 12 ga watan Afrilu - na zuwa ne a yayin da ake ta yada jita-jita kan batun lafiyarsa.

Sai dai ba za a iya tabbatar da rahotannin baya-bayan nan kan ganin nasa ba wadanda aka ji daga Koriya Ta Arewan.

KCNA ta saki wasu hotuna da ta ce sun nuna Mr Kim yana yanke kyalle a wajen kamfanin.

Da aka tambayi shugaban kasar Amurka Donald Trump kan rahoton ganin Mr Kim, sai ya ce ba ya so ya yi magana a yanzu.

Me kafar yada labaran kasar ta ce?

A cewar kamfanin dillancin labaran Koriya Ta Arewa (KCNA), Mr Kim ya je wajen ne karkashin rakiyar manyan jami'an kasar da suka hada da 'yar uwarsa Kim Yo-jong.

Kim Jong-un pictured by state media opening a fertiliser factory 1 May 2020

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, KCNA ya ce a barke da sowa da tafi a lokacin da aka ga Kim Jong-un a wajen bude kamfanin taki

Mr Kim ya ce ya gamsu da tsarin kamfanin, sannan ya yabi kamfanin da taimakawa ci gaban masana'antar sinadarai da abinci da yake yi, a cewar KCNA.

Yaushe ne aka fara yada wannan jita-jita?

A baya-bayan nan Kim bai halarci bikin murnar zagayowar ranar haihuwar kakansa na wajen mahaifi ba da ya gudana a ranar 15 ga watan Afrilu.

Wannan daya ne daga cikin manyan bukukuwa da ake yi a kowacce shekara, bikin murnar zagayowar ranar haihuwar wanda ya kafa kasar.

Kim Jong-un bai taba kin halarta bikin ba - kuma abu ne mai wahala ya ki halartar bikin kan radin kansa.

Rashin halartar tasa ne ya janyo wannan jita-jita da shaci-fadi da ba za a iya kaucewa ba - wanda ke da wuyar gano dalili.

Tun ranar 12 ga watan Afrilu rabon da Kim Jong-un ya bayyana a kafafen labarai na kasar "a lokacin da yake duba wasu jiragen yaki". Kamar ko yaushe hotunan lokacin sun nuna shi cikin natsuwa da kwanciyar hankali."

Celebration of Kim Il-sung's birth anniversary on 15 April

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Kim Jong-un bai taba kin halartar bikin zagayowar ranar haihuwar kakansa ba

Jita-jitar rashin lafiyar Mr Kim Jong-un ta fara bayyana ne a wani rahoto na wata kafar intanet da wasu 'yan kasar masu adawa da mulkinsa suka fitar a farkon watan nan.

Wata boyayyiyar majiya ta shaida wa Daily NK cewa sun fahimci yana fama da ciwon zuciya tun watan Agustan bara ''amma abin ya yi muni bayan da ya ci gaba da ziyartar Mount Paektu".

A ranar Laraba 29 ga watan Afrilu Sakataren harkokin wajen Amurka, Mike Pompeo ya ce jami'an kasar sun ce ba su ga shugaban Koriya Ta Arewa Kim Jong-un ba a 'yan kwanakin nan, kuma suna sa ido kan rahotannin lafiyarsa.

Presentational grey line