Amurka ta dade ba ta ji duriyar shugaban Koriya Ta Arewa Kim Jong-un ba - Pompeo

Kim Jong-un (centre) inspects North Korea's Air Force units on 12 April 2020

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Hoton karshe da aka ga Kim a ciki shi ne tun wanda aka dauka a ranar 12 ga wata Afrilu yana duba ayyuka

Sakataren harkokin wajen Amurka, Mike Pompeo ya ce jami'an kasar sun ce ba su ga shugaban Koriya Ta Arewa Kim Jong-un ba a 'yan kwanakin nan, kuma suna sa ido kan rahotannin lafiyarsa.

Ya kuma bayyana damuwarsa dangane da hasashen da suke da shi na barkewar annobar korona ko kuma yunwa.

Mista Kim mai shekara 36 dai ba a kara ganin sa a bainar jama'a ba tun ranar 12 ga watan Afrilu lokacin da ya bayyana a gidan talbijin din kasar.

To sai dai jami'an gwamnatin Koriya Ta Kudu sun ce rahotannin ba gaskiya ba ne.

Rashin bayyanar Kim Jong-un a wasu taruka da ya saba halarta ne dai ya janyo rade-radin ko shugaban na Koriya Ta Arewa na raye cikin koshin lafiya.

Sai dai kuma wasu na ganin Kim Jong-un yana wani wajen shakatawa na Wonsan don kare kansa daga yiwuwar kamuwa da cutar korona.

Kasar, wacce take boye abubuwan da suka shafe ta, ta rufe kan iyakokinta a karshen watan Janairu sakamakon bullar annobar cutar korona.

Me Mike Pompeo ya ce?

Da aka nemi ya tofa tasa kan rahotannin rashin lafiyar Mr Kim a tashar Fox News ranar Laraba, Mista Pompeo ya ce: "Ba mu gan shi ba. Ba mu da wasu bayanai ko labari a yau, amma muna sa ido sosai.

US Secretary of State Mike Pompeo. Photo: 29 April 2020

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Mike Pompeo ya yi ta tattaunawa mai muhimmanci da Koriya Ta Arewa a shekarun baya-bayan nan

''Akwai fargaba sosai kan yiwuwar samun fari da karancin abinci a Koriya Ta Arewa,'' ya kara da cewa.

''Muna bin diddigin wadannan abubuwan daya bayan daya, saboda suna da tasiri a kan abin da muka sa a gaba, wanda shi ne rusa shirin nukiliyar Koriya Ta Arewa.''

An yi amannar cewa a shekarun 1990 yunwa da fari sun kashe dubun-dubatar 'yan Koriya Ta Arewa.

Presentational white space

A ranar Litinin, Shugaba Donald Trump ya ce ''ya san abin da ke faruwa da Mr Kim,'' amma ya kara da cewa ''Ba zan iya cewa komai akai ba.''

''Ina dai yi masa fatan alheri,'' a cewarsa.

Sau uku Mr Trump ya hadu da Mr Kim a shekarar 2018 - amma batun wargaza shirin nukiliyar ya tsaya a watannin baya-bayan nan.

Yaushe aka fara yada jita-jitar?

A baya-bayan nan ba a ga Kim Jong-un a wajen bikin zagayowar ranar haihuwar kakansa ranar 15 ga watan Afrilu ba. Bikin na daya daga cikin manyan bukukuwa da ake yi duk shekara.

Kim Jong-un bai taba kin halartar bikin ba - kuma ga dukkan alamu ba haka siddan ya ki halarta ba.

Celebrations for birth anniversary of President Kim Il-sung

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, An fara yada jita-jitar ne bayan da aka ga bai samu halartar bikin zagayowar ranar haihuwar kakansa ba

Rashin halartarsa taron ya jawo jita-jita, sai dai tabbatar da hakan ba abu ne mai sauki ba.

Ranar 12 ga watan Afrilu ne lokaci na karshe da aka ga Kim Jong-un a gidan talbijin din kasar, inda aka nuna shi yana duba wasu jiragen yaki, a faifan bidiyon da ba a sanya ranar da aka dauke shi ba. Kamar ko yaushe ya kasance cikin nishadi da annashuwa.

Kwana daya bayan nan ya jagoranci wani taron siyasa, kamar yadda rahotannin gidan talbijin na kasar suka ce. Amma tun daga sannan ba a sake ganinsa ba.

Jita-jitar rashin lafiyar Mr Kim Jong-un ta fara bayyana ne a wani rahoto na wata kafar intanet da wasu 'yan kasar masu adawa da mulkinsa suka fitar a farkon watan nan.

Wata boyayyiyar majiya ta shaida wa Daily NK cewa sun fahimci yana fama da ciwon zuciya tun watan Agustan bara ''amma abin ya yi muni bayan da ya ci gaba da ziyartar Mount Paektu".