Koriya Ta Arewa: Amurka ta tura manzon musamman Koriya Ta Arewa ya je ya jiyo dalilin harba makamai

Wakilin Amurka a Koriya ta Arewa, Sung Kim, ya isa yankin domin tattauna gwajin makami mai linzami da Pyongyang ta yi a baya-bayan nan.

Ya je birnin Seoul ne domin ganawa da jami'an Koriya ta Kudu, ciki har da wakilin kasar kan nukiliya Noh Kyu-duk.

Ana kuma sa ran zai tattauna da wakilan shugaban kasa mai jiran gado, Yoon Suk-yeol, wanda zai hau karagar mulki a wata mai zuwa.

A ranar Asabar ne Koriya ta Arewa ta gwada wani makami mai cin gajeren zango wanda ake kyautata zaton an kera shi ne domin daukar wani makamin nukiliya.