Akwai yiwuwar wasu halittu na rayuwa a wata duniya

Asalin hoton, Cambridge University
- Marubuci, Pallab Ghosh
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Science Correspondent
- Lokacin karatu: Minti 5
Masana kimiyya sun gano cewa akwai yiwuwar wasu halittu na rayuwa a wata duniya ta daban.
Tawagar masana daga jami'ar Cambridge da ke yin bincike kan duniyar, sun gano cewa akwai alamun halittu kaɗan da ke can.
Wannan shi ne karo na biyu, kuma mai ƙayatarwa da madubin hangen nesa na sararin samaniya na James Webb ya gano cewa akwai alamun wata duniya da ake rayuwa a ciki.
Sai dai tawagar da kuma masana sararin samaniya sun bayyana cewa ana buƙatar tattara ƙarin bincike domin tabbatar da gaskiyar hakan.
Jagoran binciken, Farfesa Nikku Madhusudhana na jami'ar Cambridge, ya faɗa wa BBC cewa yana fatan samun hujjoji nan ba da jimawa ba.
"Wannan ne babban hujjar cewa akwai yiwuwar wasu halittu na rayuwa a wata duniya. Ina da tabbacin cewa za mu iya tabbatar da hakan nan da shekara ɗaya zuwa biyu".
Duniyar mai suna K2-18b ta nunka girman duniyarmu ta Earth sau biyu da rabi, kuma nisansa da mu ya kai mil tiriliyan 700.
Madubin hangen nesa na sararin samaniya na James Webb yana da karfin da zai iya ganin ƙananan halittu daga inda suke rayuwa har zuwa rana.
Tawagar ta jami'ar Cambridge ta gano cewa yanayin duniyar zai iya ya saka a iya rayuwa a can.
Farfesa Madhusudhan ya ce ya ji mamaki irin albarkatu da aka gano a duniyar, a wani aikin sa ido da suka yi.
"Albarkatun da ke wancan duniyar ya nunƙa na duniyar Earth har sau dubu ɗaya," in ji shi.
"Don haka, idan batun rayuwa a duniyar ya tabbata, to za a ji daɗin zama a cikin ta," a cewar Farfesan.
Ya ƙara da cewa: "Idan har muka tabbatar akwai rayuwa a duniyar k2-18b, hakan zai kasance abu mai kyau."

Asalin hoton, NASA
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Binciken da za a yi zai iya tabbatar da gaskiya ko kuma akasin haka, kamar yadda tawagar Farfesa Madhusudhan ta bayyana.
Da farko, wannan ganowa da aka yi ba ta kai ma'aunin da ake buƙata na iƙirarin samun nasara a bincike ba.
Dangane da haka, masu binciken na buƙatar samun tabbacin da ya kai kashi 99.9 na cewa sakamakon binciken su ya zama gaskiya ba saɓanin haka ba.
Wannan binciken ya kai kashi 99.7. Wanda ya nuna akawai alamun gaskiya, amma bai kai yadda zai gamsar da ɗaukacin masana kimiyya ba. Sai dai ya zarce kashi 68 da aka samu a watanni 18 da suka wuce, wanda masana kimiyya suka nuna shakku a kansa a lokacin.
Amma ko da tawagar masu binciken na jami'ar Cambridge suka samu isassun hujjoji, ba za a karkare cewa hujjar ta nuna akwai yiwuwar rayuwa a wata duniya ba, a cewar Farfesa Catherine Heymans na jami'ar Edinburgh kuma masaniyar sararin samaniya a wata cibiya a Scotland, wadda ke matsayin mai zaman kanta a tawagar binciken.
"Duk da rashin tabbas ɗin da ake ciki, akwai tambayar cewa a ina aka fara gano sakamakon binciken," kamar yadda ta faɗa wa BBC.
"A duniya ana samar da ƙananan halittu a cikin teku, amma ko da cikakkun bayanai ba za mu iya cewa tabbas ga asalin halittun ba saboda abubuwa masu ban mamaki suna faruwa a cikin sararin samaniya kuma ba mu san abin da sauran abin da ke faruwa a wannan duniyar da za ta iya samar da ƙananan halittu ba".
Tawagar jami'ar Cambridge ta amince da wannan ra'ayi, wadda ke aiki tare da wasu ƙungiyoyi don ganin ko za a iya samar da halittu a cikin ɗakin gwaje-gwaje.
Sauran ƙungiyoyin bincike sun gabatar da batun, na irin bayanai da aka samu daga duniyar ta K2-18b. Akwai muhawara mai ƙarfi tsakanin masana kimiyya ba kawai game da wanzuwar halittu ba, amma har ga abubuwan da ke cikin duniyar.
Dalilin da ya sa yawancin masu bincike suka gano cewa duniyar K2-18B tana da ruwa mai yawa shi ne rashin sinadarin amonia a cikinsa. Ka'idarsu ita ce ammoniya tana shiga cikin ruwa mai yawa a ƙasa.
Sai dai ana iya bayyana shi da tekun narkakkar dutse, wanda zai hana rayuwa, a cewar Farfesa Oliver Shorttle na Jami'ar Cambridge.
"Duk abin da muka sani game da duniyoyin da ke kewaye da wasu taurari, suna fitowa ne daga ɗan ƙaramin haske wanda ke kallon yanayinsu. Don haka abu ne mai ban mamaki da ya kamata mu yi nazari a kai, ba kawai don alamun rayuwa ba, har ma da komai.
"Abin da masana kimiyya ke muhawara game da duniyar K2-18b shi ne yadda yanayinsa zai kasance da kuma tsarinsa," in ji shi.
Dr Nicolas Wogan a hukumar sararin samaniyar ta Amurka NASA, yana da wani fassara na bayanan da aka samu. Ya wallafa bincike da ke nuna cewa duniyar K2-18b girmanta ba shi da yawa - kuma ba ta da sarari.
Sai dai wasu ƙungiyoyi sun kalubalanci bayanan da aka tattara bisa dalilin cewa ba su dace da bayanai daga madubin hangen nesa na sararin samaniya na James Webb ba, wanda ke nuna muhawarar masana kimiyyar kan kasancewar rayuwa a duniyar K2-18b.
Farfesa Madhusudhan ya yarda cewa har yanzu akwai sauran aiki a gabansu idan har suna son tabbatar da gaskiyar bincikensu. Amma ya yi imanin shi da tawagarsa suna kan hanya madaidaiciya.
"Gomman shekaru daga yanzu, za mu iya waiwaya a wannan lokacin kuma mu gane lokacin da sararin samaniya suka samu.
"Wannan na iya zama batu mai muhimmanci, inda ba za to ba tsammani ainihin tambayar ko mu kaɗai ne a sararin samaniya shi ne wanda za mu iya amsawa."
An wallafa binciken a cikin mujallar The Astrophysical Journal Letters.












