Me ya sa Nasa ke bincike kan halittun da ke shawagi a sararin samaniya?
Me ya sa Nasa ke bincike kan halittun da ke shawagi a sararin samaniya?
Danna hoton da ke sama don kallon bidiyon:
Ana bayar da rahotannin cewa ana ganin dubban wasu halittu da wasu abubuwa da ba a saba gani ba suna shawagi a sararin samaniya.
Mutane daga faɗin duniya sun ce suna yawan ganin waɗannan abubuwa da aka fi kira da UFOs ko UAPs.
Sai dai a baya masana kimiyya sun sha musanta hakan suna cewa abubuwan da ake cewa ana ganin ɗin ba komai ba ne face gizo.
A yanzu hukumar binciken sararin samaniya ta Nasa ta haɗa wata tawaga ta musamman ta masana kmiyya don su yi bincike kan waɗannan baƙin abubuwa da zummar son samo amsa a ƙarshe.






