Ko za a mayar da wasu ƙasashen saniyar ware a samun iko da albarkatun sararin samaniya?

Bayanan bidiyo, Ko za a mayar da wasu ƙasashen saniyar ware a samun iko da albarkatun sararin samaniya?
Ko za a mayar da wasu ƙasashen saniyar ware a samun iko da albarkatun sararin samaniya?

Danna hoton da ke sama don kallon bidiyon:

An ware ranar 30 ga kowane watan Yuni a matsayin ranar duwatsun astiriyod da ke sararin samaniya ta duniya, don wayar da kai a kan duwatsun astiriyods da ke ɗauke da ma’adinai masu daraja.

A yayin da albarkatu da ma’adinai ke ƙarewa a duniyarmu ta Earth, wasu masana kimiyya sun bayar da shawarar cewa za a iya amfani da astiriyods a sarrafa su.

Sai dai abin tambayar a nan shi ne ko za a mayar da ƙasashe masu tasowa saniyar ware a wannan harkar?