Dalilin yin husufin wata kwana biyu a jere

Bayanan bidiyo, Dalilin yin kusufin wata kwana biyu a jere

Danna hoton sama domin kallon bidiyon

An samu husufi da ya faru ne a ranakun lahadi 15 ga watan Mayu zuwa ranar Litinin 16 ga watan Mayu kuma cikakken kusufin wata ne da za a iya gani daga duka Arewaci da Kudancin Amurka, har ma da wasu bangarorin kasashen Turai da Afrika.

Watan ya koma launin ja a lokacin husufin wanda ya danganta da yanayin irin lokutan yankuna, ana kiran wannan da suna "blood moon" wato ''wata mai jini''.

Ali Abubakar Sadiq, ɗalibi a fannin kimiya da addini ya yi wa BBC bayani game da husufi da abin da ke haddasa shi a mahanga ta kimiya.