Mene ne kusufi kuma kusufi nawa ake da su a duniya?

Asalin hoton, Reuters
Kusufi kan zama abubuwan kallo da nishadi na ilimin taurari ne.
Akwai dalilai masu karfi cewa duka rassan bangaren harkokin yawon bude ido sun tashi tsaye wajen kula da wadanda ke son yin tozali da su.
Kusufi mai zuwa zai faru ne a ranakun 15 ko 16 ga watan Mayu kuma cikakken kusufin wata ne da za a iya gani daga duka Arewaci da Kudancin Amurka, har ma da wasu bangarorin kasashen Turai da Afrika.
Za ku iya ganin watan ya koma launin ja a lokacin kusufin wanda ya danganta da yanayin irin lokutan ku, ana kiran wannan da suna "blood moon" wato ''wata mai jini''.
Launin ja na "blood moon" ba wai wani takamaimen suna na kimiyya bane. A lokacin da Wata ya kasance cikin cikakken kusufi yana komawa launin ja ne.
Yana faruwa ne a lokacin da Wata ya shiga ta cikin tsakiyar duniyar Earth ya kuma toshe duka hanyoyin hasken ranar da ke shiga kai tsaye daga sararin saman Wata.
Wasu hasken ranar kan kai da saman watan a kaikaice ta hanyar sararin duniyar ta Earth, ya lullube Watan da hasken launukan ja, da rawaya da ruwan goro.
Amma wannan daya ne kawai daga cikin ire-iren kusufin.
"A takaice, akwai kusufi iri biyu: na Wata da kuma na Rana,''wani masanin ilimin taurari a Cibiyar Kimiyyar Sadarwa na Jami'ar Chile ya rubuta a sabon littafinsa mai suna "Illustrated Astronomy".
Amma kuma ya yi nuni da cewa: A fasahance akwai kusufi na uku wanda ya kunshi taurari biyu.''
Ga bayanan wadannan kusufi iri uku da kuma na'ukansu daban-baban:
KUSUFIN WATA

Asalin hoton, AFP
Kusufin Wata na faruwa ne a lokacin da duniyar Earth ta shiga tsakanin Rana da Wata, tare da toshe haske.
Ta wani gefen kuma, lokacin kusufin wata, abin da muke gani a cikin inuwar duniyar Earth da ke kan saman farin Wata ne.
Kamar yadda cibiyar bincike ta Instituto de Astrofísica de Canarias (IAC) ta bayyana: ''Ganin kusufin Rana ya danganta da yanayin wurin da mutumin da ke kallo yake.
Akasarin haka na faruwa da kusufin wata: ana iya ganin faruwar hakan daga ko wane wuri a doron duniyarmu inda Wata ke tsakanin layin da ya raba sararin samaniya da duniyar Earth a lokacin kusufin.''
Jagoran ya kuma ce '' ba kamar sauran kusufai na Rana ba, inda tsarin matakan kusufin ya danganta ga daidai inda mutum ya ke, a kusufin wata wannan kan kasance iri daya, koda kuwa daga ko a ina kake kallo.''
Kusufin wata ya kasu kashi uku.
Cikakken kusufin wata
Lokacin cikakken kusufin wata, hukumar lura da binciken sararin samaniya ta Amurka NASA ta bayyana cewa, Wata da Rana na fuskantar juna daga bangare biyu na duniyar Earth.
"Duk da cewa Wata na cikin inuwar duniyar Earth - NASA ta kara bayyanawa - wasu hasken ranar kan kai ga cikin Watan.''
Wannan hasken rana na bi ta cikin sararin duniyar Earth, wanda ke tace akasarin shudin haske - shi yasa lokacin kusufin, Wata kan koma launin ja, wanda a wasu lokuta akan yi masa lakabi da "blood moon" ko wata mai jini.
A cewar IAC, "saboda dogon layin da ke ratsa tsakiyar duniyarmu linki hudu ne fiye da na wata, inuwarta kuma ta fi fadi, don saboda cikakken kusufinsa zai kai tsawon mintoci 104."
Kuma abin da za mu iya gani ne a ranar 15 da 16 ga watan Mayu, wanda ya danganta da yanayin lokutan mu.
Kusufi kadan na wata
Kamar yadda sunansa ya nuna, kusufi kadan na wata na faruwa ne a lokacin da wani bangaren kadai na Wata ya shiga cikin inuwar duniyar Earth.
Launin ja mai duhu - amma a wasu lokuta baki-bakin ruwan toka kan bayyana a saman farin watan, wanda shi ma ya danganta ga girman kusufin.
Wannan na faruwa ne saboda banbanci tsakanin wuri mai inuwa da kuma saman wata mai haske da inuwar ba ta ratsa ta kai ba.
Kamar yadda hukumar NASA ta bayyana, a yayin da cikakken kusufin wata abu ne na ba kasafai ba, kusufi kadan na wata kan faru sau daya ko akalla sau biyu a shekara.
Ana sa ran faruwar kusufi kadan na wata a cikin watan Oktobar shekara mai zuwa, kuma za a iya gani a akasarin fadin duniya.

Asalin hoton, Getty Images
Karamin kusufin wata lunar
Don haka, wannan kusufi ba shi da yawa da ganinsa da idanu ya danganta fa bangaren watan da ya shiga bangaren kusufin: yana kankancewa yana kara zama mafi wahalar iya kallo.
Saboda haka, galibi wannan kusufin ba a cika magana a kan sa ba a cikin jerin kalandar da aka tanada ga kowa in bam asana kimiyya ba.
KUSUFIN RANA
A wasu lokuta, idan Wata ya zagayar duniyar Earth, yana tafiya tsakanin Rana da duniyarmu, tare da kare haske daga tauraro da kuma haddasa kusufin rana.
Ta wani gefen kuma, Watan kan yi inuwa a kan saman duniyar Earth.
Amma akwai kuma kusufin wata kashi uku, kana wadannan sun banbanta da juna ne ta hanyar yanayin yaya da kuma yawan yadda Watan ke lullube Ranar.
Cikakken kusufin Rana
Cikakken kusufin rana na faruwa ne a lokacin da Rana, da duniyar Earth da Wata suka hadu a wani yanayin da Watan ke lullube hasken rana baki daya.
A cikin dakikoki kadan (ko a wasu lokuta ma mintoci), sararin samaniya ta kasance cikin tsananin duhu kamar ka ce dare ne.
A wasu bayanai na hukumar NASA, "cikakken kusufin rana kan faru ne a duniyar Earth saboda arashi na ilimin lisafi da kan faru ba zato ba tsammani'': Rana ta linka Wata sau 400 a fadi, kana tana da nisan da ya linka na Wata sau 400.
"Wannan ilimin lisafi na nufin cewa a lokacin da suka hadu sosai, Wata yana lullube daukacin saman Rana, tare da haddasa cikakken kusufi,'' in ji NASA.

Asalin hoton, NASA
Layin da ke bin diddigin inuwar Wata a zagayen sararin duniyar Earth ana kiran sa da ''path of totality" kana a cikin wannan karamin wuri ne ake iya ganin wannan daukacin cikakken duhun.
A duka bangarorin biyu na zirin, ana iya ganin kusufin kadan daga tsawon dubban kilomita.
Kana kara nesa daga daukacin zirin, sa'annan kara ganin karamin bangaren Ranar da Watan ke lullubewa.
"A bisa bincike mai zurfi, kusufin rana mafi dadewa ka iya kaiwa tsawon minti bakwai da dakikoki 32,'' in ji masanin ilimin taurari dan kasar Chile.
Kusufin rana na gaba zai faru ne a watan Afrilun shekara mai zuwa, amma bukatar kasancewa a kasar Australia kafin ka iya ganin shi sosai.
Kusufin zobe

Asalin hoton, Getty
Lokacin da Wata ya kara yin nesa daga duniyar Earth sa'annan ya kara zama ''karami'', ba zai lullube daukacin Rana ba.
Don haka ana iya ganin Rana a yanayin fasalin zobe a zagayen Wata, kuma ana kiran wannan da suna annular solar eclipse ko kuma kusufin zobe.
Kamar dai a lokacin cikakken kusufin rana, lokacin wannan yanayi akwai wata 'yar hanya a inda ake iya ganin kusufin a yanayi mai kamar zobe.
A watan Oktobar shekara mai zuwa ne ake sa ran ganin kusufin zoben a Arewaci da Kudancin Amurka, har ma da yankin Antarctica da wasu yankunan Afirka ta Yamma.
Kamar yadda hukumar NASA ta bayyana, wannan kusufi galibi ya fi kowannen dadewa, saboda za a iya kallon zoben har na tsawon minti goma.
Tagwayen kusufi

Asalin hoton, Getty Images
Beamín ya bayyana cewa tagwayen kusufi ko hybrid ecilpse wani yanayi ne da ke faruwa ''lokacin da Wata ke nesa da inda zai iya lullube Rana gabaki daya, amma a yayin da yake kara tafiya, yana dada gusawa a hankali nesa da duniyar Earth kana ya dakatar da lullube Ranar, ya rikide ya koma kusufin zobe.''
"Zai kuma iya farawa daga kusufin zobe kana ya matsa kusa ya zama cikakken kusufi," Beamín ya kara bayyanawa.
Kusufin na hybrid bai cika faruwa ba, wanda (kashi 4 bisa dari ne kawai a cikin duka kusufin rana da ke faruwa), kamar yadda cibiyar bincike ta Instituto de Astrofísica de Canarias (IAC) ta bayyana.
NASA ta bayyana cewa faruwar wannan kusufi na karshe a shekarar 2013 ne, kuma za a jira har sai ranar 20 ga watan Afrilun shekarar 2023 kafin a sake ganin wani irin sa, wanda za a iya gani a kasashen Indonesia, da Australia da Papua New Guinea.
TAGWAYEN KUSUFI
Ba duka kusufi bane suka kunshi Rana da Wata: Taurari na nesa ma kan iya yin kusufi.
"Kashi 50 bisa dari na taurari na cikin tsarin taurari biyu ko fiye da haka,'' in ji Beamín a littafinsa na "Illustrated Astronomy", da ake iya samu a shafin yanar gizo kyauta.
"Tun da akwai taurari da dama a sararin samaniyarmu, wasu daga cikin irin wadannan taurari da suka kunshi taurari biyu da ke zagaya da'irarsu da ke hade sosai da duniyar Earth, su kan wuce ta gaban juna tare da lullube ta,'' ya kara bayyanawa.
"Ana kiran wadannan taurari biyu, tagwayen taurari masu kusufi.''










