An yi kusufin wata mafi tsawo a duniya

Asalin hoton, NASA
A ranar Juma'a 27 ga watan Yuli aka yi kusufin wata da ba a taba yin irinsa ba a duniya.
Ya kasance kusufin wata mafi tsayi da aka taba yi a karni na 21, a cewar Hukumar Kula da Sararin Samaniya.
An ga kusufin da tun a farko aka ce zai dauki tsawon sa'a daya da minti 43.
Mene ne kusufin wata dundum?
Kusufin wata kan faru ne a yayin da Rana da Dunyiar Earth da kuma Wata suka jeru da juna, hakan na nufin Duniyar Earth na daf a tsakanin Rana da Wata, inda ta tare hasken rana.
Kusufin kan faru ne a yayin da Wata ya shiga karkashin inuwar da Duniyar Earth ta samar.

Asalin hoton, Getty Images
Me ya sa ake kiransa "bakin wata"?
Daren da kusufin zai faru zai hadu da lamarin da aka fi sani da "Blood moon" ko "bakin wata" saboda yadda yake zama ja-jahur.
A yayin da kusufin na ranar ga watan Yuli watan zai tsaya a wani waje, inda shi mafi nisa tsakaninsa da duniya.
Yaushe kuma a ina aka ga kusufin?
An ga kusufin da aka yi ranar 27 ga watan Yulin a mafi yawancin sassan Turai da Afirka da Gabas Ta Tsakiya da Tsakiyar Asiya da Australia - kusan dai a ko ina ban da Kudancin Amurka.
Ba a bukatar wata babbar na'ura don kallon kusufin, abin hangen nesa ma kawai ya isa a duba da shi.
Wadanda suka kasance a wajen da za su iya kallo, za su ga kusufin ta yankin da wata ya yi kasa-kasa, inda aka ce zai fi bayyana sosai da misalin karfe 8.21 agogon GMT.

Asalin hoton, Getty Images
A ina aka fi ganinsa da kyau?
Wajen da aka fi ganin wannan kusufi da kyau shi ne rabin gabashin Afirka, da Gabas Ta tsakiya da Tsakiyar Asiya.
Ba za a ga kusufin a yankuna irin Tsakiya da Arewacin Amurka ba.
A kudancin Amurka kuwa, za a gan wani bangare nasa ne kawai a yankunan gabashi, kamar a biranen Buenos Aires da Montevideo da Sao Paulo da kuma Rio de Janeiro.
A wadancan biranen da wadanda ke kusa da su, za a ga kusufin ne a yayin da watan ke bacewa daga sararin samaniya.










