Me kuke son sani kan wasan Senegal da Sudan da na Mali da Tunisiya a Afcon?

Afcon

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 6

Za a fara karawar zagaye na biyu tsakanin tawaga 16 tun daga ranar Asabar da za a fara da wasa biyu a gasar cin kofin Afirka da Morocco ke karɓar bakunci.

Tun daga ranar Laraba aka kammala zagayen cikin rukuni, inda aka samu 12 da suka yi na ɗaya da na bibiyu daga rukuni shida ɗauke da tawaga hurhuɗu kowanne.

Daga baya aka zaɓo hudun da suka kare a mataki na uku a cikin rukuni, amma da maki mai yawa da suka haɗa da Mozambique da Benin da Sudan da kuma Tanzaniya.

Shin su waye za su kai zagayen kwata fainal a Afcon a Morocco?

Za a fara wasa tsakanin Mali da Tunisia

Afcon

Asalin hoton, Getty Images

Mali ta kare a mataki na biyu a rukunin farko, za ta kece raini da Tunisiya, wadda ta yi ta biyu a rukuni na uku.

Wannan shi ne wasa na 16 da zasu kece raini a tsakaninsu, inda Tunisiya ta yi nasara bakwai, Mali ta ci biyar da kuma canjaras uku a tsakaninsu.

Sai dai sau huɗu suka fafata a Afcon a baya, inda Mali ta ci wasa biyu da yin canjaras biyu.

Kuma wannan shi ne karon farko da za su fuskanci juna a gasar cin kofin Afirka a karawar ziri ɗaya kwale, wadanda suka huɗu a cikin rukuni.

Wannan shi ne karo na huɗu a jere da za su kece raini a Afcon bayan 2019 da 2021 da kuma 2023, waɗanda suka fara da kece raini a 1994.

Wasa tsakanin Mali da Tunisiya

Sun kara sau 15 a tsakaninsu, inda Tunisiya ta yi nasara bakwai, Mali ta ci wasa biyar da canjaras uku.

Wannan shi ne karo na biyar da za su kara a Afcon, Inda Mali ta ci wasa biyu da canjaras biyu daga ciki.

Wasannin da suka yi a Afcon a tarihi da ƴan wasan da suka ci ƙwallayen:

1994 – Rukunin Farko (26 ga watan Maris 1994)

Tunisia 0 Mali 2 (Coulibaly 25', Sidibe 35')

2019 – Rukuni na biyar (28 ga watan Yuni 2019)

Tunisia 1 (Khazri 70') Mali 1 (Samassekou 60')

2021 – Rukuni na shida (12 ga watan Janairu 2022)

Tunisia 0 Mali 1 (Kone bugun fenariti 48')

2023 – Rukuni na biyar (20 ga watan Janairu 2024)

Tunisia 1 (Rafia 20') Mali 1 (Sinayoko 10')

Bajintar da Mali ke yi a wasannin Afcon

Afcon

Asalin hoton, Getty Images

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Mali ta kare a mataki na biyu a rukunin farko da Morocco ta yi ta ɗaya.

Wannan shi ne karo na huɗu a jere da za ta fafata a zagaye na biyu a Afcon.

Ta haura mataki na biyu a gasar cin kofin Afirka a karo na 10 kenan.

Ta yi canjaras 24 daga wasa 62 a Afcon da cin wasa 21 aka doke ta 17 daga ciki.

Ta kai zagayen kwata fainal a karon farko a 2023 da yin nasara 2-1 a kan Burkina Faso.

Idan har ta yi nasara ranar Asabar, za ta kai zagayen kwata fainals karo na bakwai kenan, bayan 1994 da 2002 da 2004 da 2012 da 2013 da kuma 2023.

Wasan da aka zura mata ƙwallaye da yawa a ziri ɗaya ƙwale shi ne doke ta 4-0 da Zambia ta yi a 1994 da kuma a hannun Morocco a 2004 duk a zagayen daf da karfe.

Ba tawagar da ta kai ta Mali karɓara jan kati a gasa uku baya a Afcon mai uku a tarihi.

Har yanzu ba ta ci ƙwallo ba a minti na 45 ɗin farko a gasar da Morocco ke shiryawa.

Dukkan ƙwallayen da ta zura a raga a Afcon huɗu bya - bayan an yi hutu an koma zagaye na biyu take cin ƙwallyen.

Rawar Tunisia a babbar gasar tamaula ta Afirka

Afcon

Asalin hoton, Getty Images

Tunisiya ta kai zagayen ƴan 16 a bana, bayan da ta kasa kai bante a 2023.

Karo na 14 kenan da ta kai wannan matakin a tarihin Afcon.

Waɗanda suka fi ta yawan zuwa zagaye na biyu a Afcon, sun haɗa da Masar sau 20 da Najeriya sau 19 da Ghana sau 18 da Ivory Coast da Kamaru kowacce mai 17.

Ta ci ƙwallo 105 a Afcon an kuma zura mata 101 a wasa 86.

A wasa uku a baya bayan nan a wannan matakin na zagaye na biyu ta ci karawa ɗaya da canjaras ɗaya.

Da zarar ta yi nasara a wasannan na ranar Asabar za ta kai gurbin kwata fainal sau 12 kenan.

Ta kuma kai kwata fainal a Afcon biyar daga bakwai baya.

Wasa na biyu shi ne tsakanin Senegal da Sudan

Afcon

Asalin hoton, Getty Images

Senegal ta ja ragamar rukuni na huɗu ba tare da rashin nasara ba, za kuma ta kece raini da Sudan, wacce aka yi wa alfarma daga rukuni na biyar, wadda ta yi ta uku.

Wannan kuma shi ne karon farko da za su fafata a babbar gasar tamaula ta Afirka.

Sai dai kuma sau bakwai suna fuskantar juna a sauran wasannin, inda Senegal ta yi nasara huɗu da canjaras uku - kuma wasa huɗu daga ciki a shekarar 2025 suka yi.

Senegal ba ta taɓa rashin nasara a hannun tawaga daga gabashin Afirka ba a Afcon daga wasa biyar da ta yi da su, inda ta yi nasara huɗu da canjaras ɗaya.

Sudan ce ta huɗu da Sengal za ta fuskanta daga Gabashin Afirka, bayan Habasha da Kenya da kuma Uganda.

Wannan shi ne karo na biyu da Senegal za ta kara da tawaga daga Gabashin Afirka a zagayen ziri ɗaya kwale, tun bayan cin Uganda 1-0 a 2019 a zagayen ƴan 16.

Karo na 11 da Sudan za ta kece raini da tawaga daga Afirka ta Yamma, inda ta ci karawa uku daga wasa 10 da canjaras ɗaya da rashin nasara shida.

Sai dai kuma Sudan ta yi rashin nasara biyu a Afcon da ta kara da tawaga daga Afirka ta Yamma a hannun Najeriya a 2021 a cikin rukuni da kuma a hannun Burkina Faso a wasannin da Morocco ke shiryawa.

Bajintar da Senegal ke yi a Afcon

Sadio Mane

Asalin hoton, Getty Images

  • Ba a doke ta ba a karawar cikin rukuni da cin ƙwallo bakwai aka zura mata ɗaya a raga.
  • Ta kai zagaye na biyu ba tare da rashin nasara ba a gasa uku kenan a Afcon.
  • Sannan ta yi ta farko a rukuni a kowacce gasa ukun da ta gabata a gasar cin kofin Afirka a 2021 da 2023 da kuma 2025.
  • Yanzu haka Segegal ta yi wasa 14 a gasar cin kofin Afirka ba tare da an doke ta ba, ta yi nasara tara da canjaras biyar daga ciki.
  • Ta kai zagayen ƴan 16 karo uku a baya da yin nasara biyu daga ciki a baya-bayan nan.
  • Sadio Mane yana da hannu a cin ƙwallo 17 a Afcon, wanda ya ci 10 ya bayar da bakwai aka zura a raga, shi ne kan gaba a wannan ƙwazon tun daga 2010.
  • Mane shi ne kan gaba a yawan bayar da ƙwallaye ana zurawa a raga mai bakwai tun daga 2010.

Kokarin Sudan a gasar cin kofin Afirka

Afcon

Asalin hoton, Getty Images

  • Wannan shi ne karo na uku da Sudan ta kai zagaye na biyu a tarihin Afcon tun bayan da ta yi hakan a 1970 da kuma 2012.
  • Ta kawo wannan matakin da maki uku, kenan mafi karanci da ta kai gurbin ƴan 16 a tarihinta a Afcon.
  • Kuma karon farko da ta kai zagaye na biyu a gasar cin kofin Afirka tun daga 2012.
  • Sai dai kuma wasa ɗaya Sudan ta yi nasara daga bakwai a Afcon da canjaras ɗaya da rashin nasara biyar.
  • Wannan shi ne karo na uku da kociya, Kwesi Appiah zai ja tawaga a zagaye na biyu a Afcon.