Putin ya fitar da sabon sharaɗin amfani da makaman nukiliya

Asalin hoton, Getty Images
Shugaban ƙasar Rasha, Vladimir Putin ya ce Rasha za ta duba yiwuwar ayyana duk wani hari daga ƙasar da ba ta da makamin nukiliya amma ta samu goyon bayan ƙasar da ke da makamin nukiliya da harin haɗaka, a wani martani da ake yi wa kallon barazana ga amfani da makaman nukiliya a yaƙin da yake yi da Ukraine.
A wani jawabinsa na ranar Laraba da daddare, shugaban na Rasha ya ce gwamnatinsa na duba yiwuwar sauya dokokin da ƙa'idoji kan amfani da makamin nukiliya da za su bai wa Rashar damar amfani da makaman.
Kasar Ukraine dai ba ta da makaman nukuliya amma kuma tana samun tallafin soji daga Amurka da sauran ƙasashe masu ƙarfin nukiliya.
Kalaman Putin ɗin dai na zuwa ne a daidai lokacin da Ukraine ke neman a sahhale mata yin amfani da makamai masu linzami masu dogon zango ga sansanonin dakarun Rasha.
Shugaban Ukraine, Volodomyr Zelensky ya yi tafiya zuwa Amurka a wannan makon kuma zai gana da shugaban Amurkar, Joe Biden a Washinton ranar Alhamis, inda ake tunanin buƙatar Ukraine ɗin za ta kankane tattaunawar.
Ukraine dai ta ƙara kutsawa zuwa cikin Rasha a wannan shekarar kuma tana son ta kai hare-hare kan wasu wurare a cikin Rashar.
Da yake mayar da martani ga kalaman na Putin, shugaban ma'aikatan Volodomyr Zelensky, Andriy Yermak ya ce Rasha "ba ta da komai sai koƙarin tsorata duniya da batun makamin nukiliya".
Shugaba Putin ya yi barazanar yin amfani da makaman nukiliya a baya. Ukraine ta soki shirin " ana amfani da barazanar amfani da makaman nukiliya domin tsorata ƙawayenta su tallafa mata da ƙarfin soji."
China wadda kawar Rasha ce ta nemi da ƙasashen biyu su mayar da wuƙarsu, inda rahotanni ke nuna cewa shugaba Xi Jinping na China ya gargaɗi Putin da ya guji amfani da makaman nukiliya.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
To sai dai kuma a ranar Laraba bayan taron kwamitin tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya, Putin ya sanar da shirinsa na faɗada yaƙin.
Za a buɗe sabon babi na makamin nukiliya zai " fayyace sharuɗɗa da Rasha za ta bi wajen amfani da makaman nukiliya," kamar yadda Putin ya yi gargaɗi kuma ya ce yanayin zai kunshi tsarin da duniya ta amince da shi a hare-haren makamai masu linzami a kan Moscow.
Ya ce Rasha za ta duba yiwuwar irin wannan "dama" na amfani da makaman nukiliya idan har ta fahimci an fara yin amfani da makamai masu linzami da jiragen yaƙi da jirage maras matuƙa a yankunanta, abun da ke matuƙar yin barazana ga ƴancin ƙasar.
Ya ƙara da cewa "duk wata ƙasa da ta taimakawa wata da makamin nukiliya a ka kai wa Rasha hari, to za a ayyana wannan harin da harin haɗin gwiwa a kan tarayyar Rashar."
Makaman nukliya na Rasha sun kasance "abubuwa mafi muhimmanci wajen tabbatar da tsaron ƙasar da al'umarta", in ji shugaban na Rasha.
Tundai bayan yaƙin duniya na biyu, ƙasashe masu makamin nukiliya suka shiga tattaunawar ganin an taƙaita amfani da makaman bisa tunanin cewa idan ƙasashe suka yi amfani da makaman to za a samu mummunan sakamako daga kowane ɓangare.
To sai ana samun yanayin da ake amfani da ƙananan makaman nukiliya da aka tanada domin rugurguza wurin da aka hara ba tare da sinadarin makamin ya warwatsu ba.
A watan Yuni ne Putin ya gabatar da wani gargaɗi ga ƙasashen Tarayyar Turai da ke tallafa wa Ukraine, inda ya ce Rasha na da "hanyoyi da dabarun amfani makaman nukiliya fiye da abin da ƙasashen na turai ke da shi ko da ma Amurka za ta kawo nata."
Kakakin Rashar, Dmitri Peskov ya ce "ana duba yiwuwar sanya wannan sauye-sauye a kundi."










