Putin ya gargaɗi ƙasashen Yamma kan taimakon Ukraine

Shugaban ƙasar Rasha Vladimir Putin yana jagorantar zaman majalisar tsaron ƙasar.

Asalin hoton, Sputnik/Aleksey Babushkin/Kremlin

    • Marubuci, Steve Rosenberg
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Russia editor, BBC News
  • Lokacin karatu: Minti 3

Wani take da aka yi wayi gari da shi a jaridar Kommersant ta yau ta bayyana wata dirama, inda ta ce, "Vladimir Putin ya ja layi."

Shin ƙasashen Yamma za su tsallake layin? idan kuma za su iya, ta yaya Rasha za ta mayar da martani?

Da yake magana a St Petersburg, Shugaba Putin ya bayyana gargaɗi kai-tsaye zuwa ga ƙasashen Yamma: kar ku bari Ukraine ta yi amfani da makamanku masu linzami masu cin dogon zango domin kai farmaki a yankunan Rasha.

A cewarsa, Rasha za ta yi nazarin tare da bibiyar ƙasashen Nato da "suke da hannu" a yaƙin na Ukraine.

"Wannan zai nuna cewa ƙasashen NATO, da Amurka da Turai suna yaƙi da Rasha ne,"

Ya ce idan har Ukraine za ta kai harin makami mai linzami zuwa Rasha, dole ta yi amfani da wasu bayanai daga tauraron ɗan Adam na ƙasashen Yamma, sannan dakarun ƙasashen NATO ne kaɗai za su iya "aika makamai masu linzamin a irin wannan yanayi."

Rasha ta sha jan layi a baya, amma ana tsallakawa.

A ranar 24 ga Fabrailun 2022, lokacin da ya sanar da fara "aikin soji na musamman" - yaƙin fito na fito da Ukraine - Shugaba Putin ya yi gargaɗi "ga waɗanda suke da niyyar shiga sharo ba shanu daga ƙasashen waje."

"Duk wanda ya yi niyyar kawo mana tsaiko ko kuma ya yi barazana ga ƙasarmu ko mutanenmu, dole zai gane cewa Rasha za ta mayar da martani cikin sauri," inji shugaban na Rasha.

"Kuma abin da zai biyo baya, abu ne da ba a taɓa gani ba a tarihi."

Sai dai ƙasashen ya Yamma sun kunnen uwar shegu da gargaɗin, inda suka taimaka wa Ukraine da tankokin yaƙi da makamai masu linzami, har da jiragen yaƙin F-16 na Amurka.

Tuni Rasha ta zargi Ukraine da amfani da makamai masu linzami masu cin dogon zangp na ATACMS na Amurka wajen kai hare-hare a Crimea, wani yankin Ukraine da Rasha ta mamaye.

Jiragen ATACMS suna ɓarin wuta a atisayen sojin Amurka da Koriya ta Kudu.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Jiragen ATACMS suna ɓarin wuta a atisayen sojin Amurka da Koriya ta Kudu.
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Abin da ya bayyana, a cikin shekara biyu da suka gabata shi ne, Rasha da kafafen sadarwa na ƙasar sun sha zargin ƙasashen Yamma da "yaƙi da Rasha," ko kuma "ƙaddamar da yaƙi" a Rasha, duk da cewa Rashar ce ta fara kai hari a Ukraine.

Amma daga maganganun Putin na kwanan nan, ya nuna cewa kai hare-hare a kan yankunan Rasha ta hanyar amfani da makaman ƙasashen Yamma masu linzami zai bude wani sabon babi a yaƙin.

Sai dai abin da bai bayyana ba a jawabinsa na jiya shi ne yadda za su mayar da martani.

"Za mu ɗauki mataki ne daidai da irin barazanar da muka gani," inji Vladimir Putin.

A ranar Juma'a, Rasha ta dakatar da tantance jami'an jakadancin Burtaniya, inda ta zarge su da "leƙen asiri" da kuma barazana ga tsaron Rasha.

Amma ana hasashen martanin Putin zai yi girma saboda ya ɗan tsegunta hakan a watan Yuni.

A wata ganawa da ya yi shugabannin kafafen sadarwa na duniya, an tambaye shi cewa shin Rasha za ta mayar da martani idan Ukraine ta yi amfani da makaman ƙasashen Yamma wajen kai mata hari?

Sai ya ce, "da farko dai, lallai za mu inganta tsaron sararin samaniyarmu, za mu riƙ tarwatsa makamansu masu linzamanin."

"Na biyu kuma idan har wani yana tunanin zai bayar da irin waɗannan makaman domin a kawo mana hari, sannan a jawo wa mutanenmu tashin hankali, me ya sa muma ba za mu bayar da irin makaman ba ga ƙasashen da suke buƙatarsu domin kai hare-hare a wurare masu muhimmanci na irin waɗannan ƙasashen kamar yadda suka yi wa Rasha?"

Abin da yake nufi shi ne, shi ma zai ba maƙiyan ƙasashen Yamma makamai domin su ƙara ƙarfi.

A farkon wannan watan, Mataimakin Ministan Harkokin Wajen Rasha, Sergei Ryabkov ya sanar da cewa Rasha za ta sake duba dokokinta na nukiliya: wato batun yaushe ya kamata Rasha ta yi amfani da makaman nukiliya.

Firaiministan Burtani Starmer da Sakataren Harkokin Waje Lammy lokacin da suka isa Amurka

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Firaiministan Burtani Starmer da Sakataren Harkokin Waje Lammy lokacin da suka isa Amurka.

Sai dai yanzu haka Sir Keir Starmer yana birnin Washington domin ganawa da Shugaba Biden. Ana tunanin daga cikin abubuwan da shugabannin biyu za su tattauna akwai batun Ukraine ta yi amfani da makamai masu linzami masu cin dogon zango.

"Rasha ce ta fara yaƙin na. Ita ce ta ƙaddamar da haramtaccen hari a Ukraine," inji Sir Keir a lokacin da ya isa Wahington. "Rasha idan ta ga dama za ta iya kawo ƙarshen yaƙin."