Tambayoyi biyar kan hare-haren da Ukraine ta kai yankin Kursk na Rasha

Asalin hoton, Reuters
- Marubuci, Kateryna Khinkulova
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
- Lokacin karatu: Minti 6
Harin da Ukraine ta kai yankin Rasha ranar 6 ga watan Agusta ya zo da bazata ba ga Moscow kadai ba, amma har ga yawancin wadanda ke cikin Ukraine da kuma masu sa ido kan yakin daga waje.
Me ya sa Kyiv ta kai wannan hari a daidai lokacin da dakarunta suka gaji da yaki a wurare da dama? Kusan mako daya, sojojin Rasha na ci gaba da dakile wannan hari sai dai an fara gano dalilin da ya sa aka kai harin.
Ga wasu tambayoyi biyar kan wannan ci gaba da aka samu a yakin Ukraine wanda ake ganin zai iya shafar yadda yakin yake ci gaba da wanzuwa cikin watanni masu zuwa.
Me ya faru a Kursk?
A ranar 6 ga watan Agusta, sojojin Ukraine suka kai wani harin bazata zuwa lardin Kursk na Rasha, da ke makwabtaka da ita. Sai dai an kasa samun sahihan bayanai kan wannan hari da aka kai kawo yanzu.
Tun da farko, an yi tsammanin cewa wasu kungiyoyi masu zagon kasa ga Rasha ne wadanda ke adawa da gwamnatin shugaba Vladimir Putin suka kai harin.
Sun yi kokarin shiga cikin Rasha daga Ukraine, kuma an nuna cewa akwai daruruwan jami'ai 'yan kabilu daban-daban daga Rasha.
Sai dai yayin da wannan hari ya nausa zuwa cikin yankin Rasha - inda shafukan sojojin Rashar ke ruwaito cewa ana ci gaba da gwabza fada a yankin mai nisan kilomita 30 daga iyaka da kuma abin da gwamnan yankin Kursk ke fada wa shugaba Putin cewa kauyuka 28 na hannun Ukraine, ta fito karara cewa akwai hannun sojojin Ukraine a ciki.

Asalin hoton, Reuters
Ta nuna cewa yayin da Rasha ta karkata akalar sojojinta zuwa wurare daban-daban da ake ci gaba da gwabza fada, Ukraine ta yi amfani da rashin isassun jami'an tsaro a kan iyaka wajen kutsawa zuwa cikin Rasha.
Wani babban jami'im Ukraine da ba a bayyana sunansa ba ya fada wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa: ''Muna ci gaba da kai hare-hare. Burin mu shi ne karya lagon abokan gaba, janyo musu asara mai yawa da kuma lalata al'amura a Rasha saboda sun kasa tsare kan iyakarsu.''
Me ya sa Ukraine ta kai wa Rasha hari a yankin Kursk?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Tun da farko, Ukraine ba ta sanar da batun kai harin ba, inda sai ranar 10 ga watan Agusta shugaba Volodymyr Zelensky ya fito ya bayyana hakan. Ya yi ikirarin cewa Ukraine ta ci gaba da dannawa da kuma tura yakin zuwa yankunan abokan gabarta.
Bai bayar da wasu dalilai ba kan abin da ya sa aka kai harin, sai dai ranar 12 ga Agusta ya sanar da cewa kusan yankin Rasha mai murabba'i 1,000 na karkashin ikon Kyiv.
Kwararru kan harkar soji da kuma siyasa wadanda ke kokarin amsa tambayar me ya sa aka kai harin, yawancinsu sun amince da cewa Ukraine ta kai harin ne domin jirkita hankalin Rasha.
A tsawon watanni da suka wuce, Ukraine ta fukanci matsaloli wajen dakile sojojin Rasha a gabashin kasarta, wadanda ke ci gaba da dannawa, da kuma kwace yankin Chasiv Yar mai muhimmanci a watan da ya gabata. Al'amarin ya fi kazanta a arewa maso gabas da kuma kudancin kasar.
Duk da cewa sojojin Rasha sun fi na Ukraine yawa da kuma irin makamaki da ke hannunsu a yankuna da dama da ake gwabza fada, hukumomin Ukraine sun yanke shawarar daukar kasada wajen kirkiro da wani sabon daga na fada mai nisan daruruwan kilomitoci, domin gajiyar da dakarun na Rasha, da kuma karkata hankalin daga kudancin kasar zuwa yankin Kursk na Rasha.

Asalin hoton, Reuters
Wani kwararre kan harkar tsaro, farfesa Mark Galeotti ya fada wa BBC cewa Ukraine na cikin wani yaki da take kokarin rage wa ta hanyar far wa abokan gabarsu, ba tare da aika dakaru da yawa ba, amma yanzu suna son daukar kasada domin samun nasara.
Wani kwamdandan sojojin Ukraine, da yake tattaunawa da jaridar The Economist, ya kuma ce wannan abin da aka yi caca ce: "Mun aika dakarunmu da suke shirye don yaki zuwa iyakokin da ba su da isasshen tsaro". Ya kara da cewa kasadar da suka dauka na samun nasara sai dai ba da sauri ba kamar yadda Kyiv ke fata.
"Kwamandojinsu ba wawaye bane... Suna janye jami'ansu, sai dai ba cikin sauri yadda muke bukata ba. Sun san ba za mu kara kai dakaru zuwa nisan kilomita 80 ko 100 ba."

Asalin hoton, AFP
Ta yaya Rasha ta mayar da martani?
Rasha dai ta kwatanta harin da Ukraine ta kai a matsayin "aikin ta'addanci".
Kimanin mutum 121,000 ne aka bai wa umarnin tashi daga yankin Kursk sannan wasu 11,000 kuma an kwashe su daga yankin Belgorod mai makwabtaka.
Hukumomin Rasha sun ayyana dokar ta-baci ta tarayya a yankin tare da biyan diyyar dala 115 ga kowane mutum da ke zaune a yankin.
Babban hafsan hafsoshin sojin Rasha Janar Valery Gerasimov ya yi ikirarin cewa a makon da ya gabata an dakatar da kutsen na Ukraine.
Janar Gerasimov bai halarci sabon taron kwamitin sulhu na Rasha wanda shugaba Putin ya jagoranta ba, wanda aka yi domin warware wannan rikici. Sai dai a daya bangaren kuma, daya daga cikin makusantan Putin ya halarci taron, wato shugaban hukumar tsaron Rasha ta FSB, Alexander Bortnikov.
A cikin sanarwarsa ta baya-bayan nan game da abubuwan da suka faru, Shugaba Putin ya zargi Ukraine da kai hari kan fararen hula masu zaman lafiya kuma ya yi alkawarin mayar da martanin da ya dace.
Farfesa Galeotti ya ce Ukraine na fuskantar babban barazana na mayar da martani daga Rasha.
"Putin na iya kiran wani taron gangamin ya kuma kawo karin sojoji dubu dari cikin dakarunsa."
Ya kara da cewa Rasha za ta iya nemo wasu hanyoyin da za ta kara ruruta wutar rikicin.
A cikin 'yan watannin da suka gabata Ukraine ta fuskanci mummunan harin bam da Rasha ta kai kan kayayyakin makamashinta, wanda ya janyo lalacewar yawanci daga cikinsu. Wannan kamfen na iya yiwuwa ma fi tsanani.

Shin fada a Kursk na nufin Ukraine ta sauya akalar yakin?
Raguwar harin da Rasha ta kai cikin Ukraine abu ne da ya kamata a yi duba a kai - kuma hakan ba yana nuna cewa za a kawo karshen wannan yaki nan kusa ba.
Kamar yadda Mark Galeotti ya ce, “yanki ne mai nisan kilomita 50, kuma idan aka duba girman Rasha da Ukraine, wannan na nuna cewa ba a mayar da hankali kan wurin ba. Sai dai tasirin siyasarsa yana da muhimmanci."
Wasu kwararru sun kalubalanci cewa Ukraine na son nuna wa kawayenta na Yamma, musamman ma Amurka, cewa dakarunta za su iya ci gaba da fada. Wannan ya kara nuna karfin Kyiv na akalla lokaci kankani, na ci gaba da tattaunawa kan karfinta: Dakarunta da ke cikin Rasha da nisan kilomita da bai fi 30 ba, na nuna cewa da wuya Moscow ta amince da wata shawara na janyewa daga yankunan da suka mamaye.
Harin da aka kai ya kuma sauya akalar yakin ga 'yan Rasha da ke zaune cikin kasar - Wannan ba yaki ne mai nisa ba wanda ake wa lakabi da "aikin soji na musamman", sai dai abu da ya shafe su kai-tsaye.

Asalin hoton, EPA-EFE/REX/Shutterstock
Wakiliyar BBC daga Gabashin Turai Sara Rainsford ta ce: "Duba da irin rahotanni da ke fitowa daga yankin Kursk, duk da irin iyaka da aka yi wa 'yanjarida a Rasha, na nuna cewa akwai wasu tambayoyi da ke bukatar amsarsu kan harin."










