'Sudan na cikin barazanar shiga babban bala'i'

Lokacin karatu: Minti 3

Sudan da ke fama da tsananin yaƙi na cikin barazanar zama ƙasar da ta gaza saboda taɓarɓarewar yanayin da fararen hula ke ciki a daidai lokacin da ƙungiyoyi masu riƙe da makamai ke ƙaruwa, kamar yadda shugaban wata ƙungiyar bayar da agaji ya shaida wa BBC.

Ba ya ga ɓangarori biyu da ke faɗa da juna a Sudan - sojojin ƙasar da kuma dakaru RSF - akwai wasu ƙananan ƙungiyoyi na kabilu da ke riƙe da makamai, inda suke ci gaba da satar abinci da kuma afka wa fararen hula, in ji shugaban ƙungiyar kula da ƴan gudun hijira ta ƙasar Norway, Jan Egeland.

"Ɓangarorin biyu na ragargaza gine-gine, suna yi wa al'ummar kisan kiyashi," in ji shi.

A tsawon watanni 19, an yi artabu tsakanin sojoji da kuma dakarun RSF domin samun iko, abin da ya tilasta wa mutum sama da miliyan 10 tserewa gidajensu da kuma jefa ƙasar cikin barazanar faɗawa ƙangin yunwa.

"Abubuwan da na gani sun ƙara tabbatar min da cewa wannan shi ne babbar matsalar jin-kai da muka taɓa gani da idonmu, babbar matsalar ƙarancin abinci da kuma ta ɗaiɗaita mutane," in ji Mista Egeland, bayan ziyara da ya kai Sudan.

A watan Satumba, hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta ce matsalar yunwa ta karaɗe ko'ina a faɗin Sudan.

An tilasta wa wuraren bayar da abinci kyauta rufewa saboda rashin masu ɗaukar nauyi. Egeland ya ce rashin taimakon jin-ƙai na janyo mutuwar mutane.

"Ana fama da yunwa a sassan Sudan da dama," in ji shi, inda ya ƙara da cewa ana amfani da matsalar wajen ƙara tsananta yaƙi.

Wasu ƙwararru kan harkar samar da abinci na fargabar cewa mutum kusan miliyan 2.5 za su mutu sakamakon yunwa a ƙarshen wannan shekara.

Mista Egeland ya yi gargaɗin cewa "duniya ta gaza a Sudan baki-ɗaya" saboda kasa yin abin da ya kamata.

Ya faɗa wa BBC cewa idan Turai na son kauce wa matsalar kwararowar bakin-haure, to ya kamata ta "bayar da agaji, kariya da kuma zaman lafiya a wannan yanki na duniya".

"Ba a bayar da taimakon da ya kamata, duk da cewa shi ne babbar matsalar jin-kai a duniya," in ji Egeland.

Dubban mutane ne aka kashe tun bayan ɓarkewar yaƙi a Sudan. Ƙungiyoyin kare hakkin ɗan'adam sun nuna fargabar cewa ana aiwatar da kisan-ƙare-dangi a Sudan.

Duk da haka, an ƙasa cimma yarjejeniyar samun zaman lafiya a tattaunawa tsakanin sojojin Sudan da kuma dakarun RSF.

"Yaƙin zai tsaya ne idan waɗannan ɓangarori suka ga cewa za su rasa abubuwa da yawa idan aka ci gaba da faɗa, maimakon yin abin da ya kamata," in ji Egeland.