Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Matan da aka yi wa fyaɗe a Sudan sun fara kashe kan su'
- Marubuci, Ian Wafula
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Africa security correspondent
- Lokacin karatu: Minti 3
Gargaɗi: Wannan labarin na ƙunshe da wasu bayanai da suke tayar da hankali.
Mata da dama sun kashe kansu a jihar Gezira ta Sudan bayan dakarun RSF sun musu fyaɗe a yaƙin da ake ci gaba da gwabzawa a ƙasar, kamar yadda ƙungiyoyin hare haƙƙin ɗan'adam suka bayyana.
Wannan bayanin na zuwa ne bayan Majalisar Ɗinkin Duniya ta zargi dakarun na RSF da aikata "manyan laifuka" ciki har da kisan kiyashi a jihar a makon jiya.
A yanzu da dakarun na RSF suke ta ƙara kutsawa, wata ƙungiyar kare haƙƙin ɗan'adam ta bayyana wa BBC cewa tana ganawa da wasu mata guda shida waɗanda suke tunanin kashe kan su saboda fargabar cin zarafi.
Amma RSF sun musanta zargin na Majalisar Ɗinkin Duniya, inda suka shaida wa BBC cewa zargin, "ba shi da makama."
Fafutikar ƙwace ikon mulkin ƙasar da ake gwabzawa tsakanin sojojin ƙasar da dakarun RSF ya ci dubban mutane, sannan ya raba sama da mutum miliyan 11 da muhallansu tun bayan ɓarkewar yaƙin a watan Afrilun 2023.
Shugaban shirin samar da abinci na Majalisar Ɗinkin Duniya, Cindy McCain, ta ziyarci sansanin raba abincin agaji na ƙasar da ke Port Sudan a wannan makon, inda ta shaida wa BBC cewa ƙasar na iya fuskantar matsalar buƙatar ayyukan jinƙai mafi tsanani a duniya idan ba a tsagaita wuta ba.
Ta yi gargaɗin cewa miliyoyin mutane za su iya mutuwa saboda yunwa.
Rahotannin yadda dakarun RSF suka zafafa hare-hare a jihar Gezira ya biyo bayan yadda kwamandansu a jihar, Abu Aqla Kayka ya koma ɓangaren sojin ƙasar.
"Sai RSF suka fara ramuwar gayya a yankunan da Abu Kayka yake da ƙarfin iko. Sun kashe na kashewa, sun sace na sacewa, sannan sun yi wa mata manya da ƙananan fyaɗe," in ji Hala al-Karib, shugabar ƙungiyar Strategic Initiative for Women in the Horn of Africa (Siha) a zantawarta da BBC.
Siha, ƙungiyar ce da ke tattara bayanan matan da aka ci wa zarafi a Sudan a lokacin yaƙin, ta tabbatar da cewa mata sun kashe kansu a makon jiya a jihar Gezira.
Ms Karib ta ce mata biyu ƴan ƙauyan Al Seriha ne, ta ukun kuma ƴar birnin Ruffa ce.
Ƴaruwar matan da ta kashe kanta a ƙauyen ta bayyana wa Siha cewa ƴaruwarta ta kashe kanta ne bayan wani mayaƙin RSF ya mata fyaɗe a gaban mahaifinta da ɗanuwanta, sannan ya kashe su.
A makon jiya an yaɗa wasu faye-fayen bidiyo da suke nuna gomman gawarwaki da aka lulluɓe da ake zargin dakarun RSF ne suka kashe a Al Seriha.
Binciken ƙwaƙwaf na BBC ya tabbatar da bidiyon, inda ya nuna cewa an ɗauki bidiyon ne a wani masallaci da ke Al Seriha.
Sai dai samu hujjar waɗanda suka kashe kansu ne a yankuna biyu daga cikin guda 50 da suka fuskanci hari, in ji Ms Karib, sannan ta ƙara da cewa adadin zai fi haka.
Wata mai fafutika a Gezira, wadda ba ta so a bayyana sunanta, ta tabbatar wa BBC cewa wasu mata sun kashe kansu bayan SRF sun kashe mazansu.
Ta ce ta ga saƙon WhatsApp daga wata wadda ta bayyana cewa ƴaruwarta ta kashe kanta bayan dakarun RSF sun mata fyaɗe, sannan suka kashe mata ƴanuwanta biyar da kawunnanta a Al Seriha.
Amma ta ce da wahala a tabbatar da yawaitar kashe kai daga kafofin sadarwa saboda yanayin rashin ingancin layin sadarwa.
A ranar Talata, wani rahoton Majalisar Ɗinkin Duniya ta fitar mai shafi 80, ya ce tun bayan da yaƙin ya ɓarke, an samu rahotonnin aƙalla cin zarafi guda 400 zuwa Yulin 2024, inda ake hasashen asalin adadin ya haura haka.
Waɗanda aka samu bayanin game da su sun haɗa da masu shekaru tsakanin takwas zuwa 75 - kuma mafi yawansu suna buƙatar ganin likita, amma yawancin asibitoci an lalata su a yaƙin, in ji Majalisar Ɗinkin Duniya.
Kakakin RSF, Nizar Sayed Ahmed ya shaida wa BBC cewa, "waɗannan zarge-zargen ƙarya ne, kuma ba su da tushe," in ji shi.
"Idan ana so a tabbatar da gaskiyar lamarin, dole Majalisar Ɗinkin Duniya ta tura masu bincike na musamman zuwa Sudan su gane wa idonsu," in ji shi.
Ms Karib ta shaida wa BBC cewa ƙungiyar Siha na ƙoƙarin ci gaba da tattaunawa da matan guda shida waɗanda suke tunanin kashe kansu saboda fargabar dakarun RSF za su iya cimma su, har su ci zarafinsu.
Ta ce suna ba su shawarwari, sannan suna ƙoƙarin ganin yadda za su iya tseratar da su zuwa wani wuri mai aminci.
Ta ce kuma suna ƙoƙarin taimakon wata ƴar shekara 13 da wasu gungun mayaƙan RSF suka mata fyaɗe a Gezira, wadda take matuƙar buƙatar ganin likita.
Ta ce yarinyar tana ta zubar da jini, kuma tana hanyar tafiya ƙauyen sabuwar Halfa daga ƙauyensu da ke arewacin Ruffa.