Shin wa ke da iko da Tafkin Chadi?

Lokacin karatu: Minti 3

Tafkin Chadi, yanki ne da ya hada kasashen Najeriya da Nijar da Kamaru da kuma Chadi, sai dai kuma ana ganin yanzu yankin ya zamo mafakar 'yanta'adda.

A kwanakin baya Babban Hafsan Sojojin Ruwan Najeriya, Vice Admiral Idi Abbas, ya kai ziyara Tafkin Chadin, inda ya ba da tabbacin cewa dakarun sojin ƙasar na zafafa ƙoƙarin tsare tafkin da hanyoyin ruwan da ke kusa.

Shi ma gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya yi kira da a samu hadin guiwar rundunonin tsaro domin kaddamar da hare-hare kan maboyar 'yan Boko Haram a Tafkin wanda da ya ce nan ne mafakar 'yanta'adda.

Masana lamuran tsaro irinsu Barista Audu Bulama Bukarti, sun bayyana muhimmancin tabbatar da tsaro a yankin.

Barista Bukarti ya shaida wa BBC cewa, 'yan Boko Haram da kuma 'yan ISWAP, ba wai kawai sun mayar da yankin Tafkin Chadi wajen buya ba, a nan ne suke kai hare-hare ba.

"Tafkin, na ba su damar gudanar da abubuwa da dama wadanda idan har aka kwace ikon yankin daga wajensu, to dukkan abubuwan da suke ba za su yiwu ba", in ji shi.

Tsokacin masanin ke nuna cewa babu tabbas kan ikon tafkin wanda ya hada kasashen Najeriya da Chadi da Nijar da kuma Kamaru.

"Tafkin ya zama tamkar maboyarsu, suna abin da suka ga dama a ciki, amma duk da haka idan gwamnatin Najeriya ta yi abin da ya dace tsaf za ta karbe ikon Tafkin da ke bangarenta," in ji Bukarti.

Yadda ƴanta'adda ke amfana da Tafkin Chadi

Kasancewar ruwa albarka ne ga ɗan'adam, don haka akwai albarkatu a ciki.

Dr Bukatarti ya ce 'yanta'addan da ke yankin suna yi abubuwa kamar, " Amfani da ruwan da ke tafkin wajen shigo da makamai da kayan abinci da sauran kayan masarufi da ma mai da dai sauran bukatunsu."

"Suna kuma amfani da albarkatun Tafkin Chadi wajen noma domin suna da manyan gonaki suna kamun kifi duk a wajen har ma suna ba masunta dama su ma su yi sannan su biya su haraji." In ji shi.

Ya ƙara da cewa Tafkin Chadi waje ne mai surkuki sosai wato akwai duhun bishiyoyi a wajen, sannan ga rashin kyawun hanya, kuma 'yan Boko Haram duk sun dasa bama-bamai wanda su kadai ne suka san inda suka sanya su.

"Idan kamar jami'an tsaro suka shiga ciki sai sun yi a hankali idan ba haka ba bam ya tashi da su," a cewarsa.

Masanin tsaron ya ce gwamnatin Najeriya da jami'an tsaron da ake da su sun fi karfin 'yan Boko Haram nesa ba kusa ba, lallai ne a samu dabarun da za a bi domin zuba sojojin kasa wanda su ne za su jagoranci aikin tabbatar da tsaro a Tafkin, sannan sai a samu sojojin sama da na ruwa su taimaka musu, ta hakan ne za a iya yakar 'yan Boko Haram a kwato Tafkin."

Ya ce hanya ta biyu da za a iya kwato tafkin daga wajen 'yanta'adda ita ce a hada karfi da karfe da kasashen da tafkin ya shiga ciki domin kwato shi idan har ana son samun galaba