Abubuwan da ya kamata ku sani kan allurar riga-kafin ƙyandar biri

Asalin hoton, AFP
- Marubuci, Makuochi Okafor
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- Lokacin karatu: Minti 4
Ƙasashen Afirka da dama sun soma daukar matakin yin rigakafin ƙyandar biri.
Wannan shine karon farko da za a aiwatar da gagarumin shirin rigakafin ƙyandar birin wato Mpox, wadda ake sa ran za a yi wa dubban mutanen da suka fi zama cikin hatsarin kamuwa a Firka.
Tun farkon wannan shekarar an samu ɓullar cutar a ƙasashen Afirka 16, inda a makon da ya gabata cutar ta ɓulla ƙasar Ghana kamar yadda hukumar lafiya ta duniya, WHO ta tabbatar.
A Jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo cutar tafi ƙamari inda aka samu mutane, 22,000 da suka kamu, yayin da mutane sama da 700 suka rasu kamar yadda Cibiyar daƙile yaɗuwa cutuka ta Afirka , CDC ta sanar.
Kongo ta yanke shawarar soma gwajin allurar rigakafin ne a Goma inda cutar tafi ƙamari.
Cutar ba ta yi ƙamari a Najeriya ba,inda mutane 70 suka kamu da cutar.
Hukumomin lafiya a Najeriya sun bayyana cewa za su yi wa mutanen da suka fi hatsarin kamuwa da cutar rigakafi a jihohin, Ogun, Akwa Ibom, Filato, Cross River da Abia.
Ƙasar Rwanda ita ce ƙsa ta farko da cutar ta fara ɓulla kuma ta fara yin rigakafin cutar a watan da ya gabata. Rwanda na fama da cutar ƙyandar biri da kuma zazzaɓin Marburg, wanda ake sa ran samar da rigakafinsa da magani ƴan makwanni masu zuwa.
Ga abubuwan da ya kamata ku sani

Asalin hoton, AFP
Wace rigakafi ce a ƙasa?
Hukumar lafiya ta duniya, WHO ta bada shawarar amafni da rigakafi guda uku wajen yaƙi da cutar ƙyandar biri.
Akwai samfarn MVA-BN wadda kamfanin Danish Bavarian Nordic ya samar, ita ce kuma ta farko da WHO ta bada shawrar amfani da ita a watan Satumba.
Sauran rigakafin guda biyu sune, LC-16 wadda kamfanin ƙasar Japan , KM Biologics yake samarwa.
Wanda aka yi wa rigakafin zai dauki mako biyu kafin ya samu kariya daga cutar.
Cutar ƙyandar biri da ƙaranbau ƴan gida ɗaya ne, alamominsu da abubuwan dake haifar da su da alamominsu duk ɗaya ne
Su waye za a iya ba riga-kafin ?
Hukumar lafiya ta duniya, WHO ba ta bada shawara ƙasashe su yi wa al'ummarsu gaba ɗaya rigakafin ba, inda ta bada shawarar farawa da wadanda suka fi htsarin kamuwa da cuta.
Wadanda suka zama cikin hatsarin kamuwa da cutar sun haɗa da ma'aikatan lafiya da wadanda wasu na kusa da su suka kamu ciki harda yara, da mutanen dake da abokanan rayuwa sama da ɗaya, da mazan dake saduwa da mace fiye da ɗaya da kuam mata masu zaman kansu.
Za a iya yi wa yara rigakafin ?
A yanzu dai samfarin, LC-16 ce kaɗai WHO ta amince da ayi wa ƴan ƙasa da shekara 18.
WHO ta ce samfarin MVA-BN za a iya yiwa ƴn ƙasa da shekara 18 a wani yanayi na musamman.
Hakan na nufin za a iya amfani da ita n kadai a yanayi na gaggawa domin samar da kariya ga mutane masu yawa.
Misali kamar ƙasar Kongo da ke akwai yara da dama da suka kamu, za a iya amfani da samfarin, MVA-BN. Sai dai samfarin ACAM2000 ba a amince a yi amfani da ita ba kan yara.
Yaya ake yin rigakafin?
Ana yin allurar rigakafin samfurin MVA-BN sau biyu, inda ake bada kwana 28 tsakanin allurar farko da ta biyu, kuma ana yin ta a jikin dantsen hannu.
Sauran rigakafin biyu ana yin su ne sau guda ta hanyar amfani da sirinji na musamman, inda ake tsira shi kan fata wurare da dama kuma wani lokaci rigakafin na barin tabo a jikin inda aka yi ta.
Shin akwai wasu illoli?

Asalin hoton, AFP
Kamar kowace rigakafi, wasu mutanen kan fuskanci wasu matsaloli da suka haɗa da zafi da kumburi a inda aka yi rigakafin da kuma ƙaiƙayi da ciwon ka da mutuwar jiki da ciwon gaɓoɓi da amai da zazzabi.
Shin wanda aka yi wa rigakafin na iya kamuwa?
Akwai yiyuwar wanda ya anshi rigakafin ya kamu da cutar, sai dai WHO da CDC sun ce yiyuwar hakan na da wuya.
Rigakafi na rage haɗarin kamuwa da cutar tana kuma rage radadi koda an kamu da ita, alamomin kan zo da sauƙi.
Yanayin lafiyar jikin wanda aka yiwa rigakafin da shekaru na shafar tsawon lokacin da allurar za ta yi aiki a jiki.
Shin an tabbatar da ingancin waɗannan riga-kafi?

Asalin hoton, AFP
Masu bincike na ci gaba da tattara bayanan ingancin wadannan rigakafi bayan da aka fara samun ɓarkewar cutar a 2022, cewar Dr. Samuel Boland jami'in WHO a Afirka.
Bayanai sun nuna cewa rigakafin an aiki sosai ga wanda ya kammala karɓar rigakafin.
Ya ce ana ci gaba da bincike kan sabuwar cutar samfarin Clade 1b, an gano cewa rigakafin tana bada kariya, a wani bincike da aka gudanar kan yadda rigakafin ke aiki wurare daban-daban.
Dr Boland ya shaida wa BBC cewa WHO na ci gaba da sabnya ido kan yadda cutar Mpox ke bazuwa da kuma yadda maganinta ke amfani.
Darakta janar na CDC Afirka, Jean Kaseya ya ce an amince da amfani da rigakafin MVA-BN saboda angano cewa tafi aiki kan cutar.
Me za ka yi idan ka ga wasu alamomin cutar sun bayyana a jikinka?
Idan har kaga wasu alamomi da suka haɗa da ciwon aki da ciwon jiki da ciwon baya da mutuwar jiki da kumburi da ƙuraje, ko kuma kaga wasu alamomi da baka gane masu ba, sai a tuntuɓi ma'aikatun lafiya mafi kusa domin samun agajin da ya kamata.










