'Ina kallo iyalina suka mutu’: Labarin kisan kiyashin da ake yi wa Musulmai a Myanmar

Asalin hoton, BBC/Aamir Peerzada
- Marubuci, Yogita Limaye
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, South Asia & Afghanistan correspondent
- Aiko rahoto daga, Bangladesh-Myanmar border
- Lokacin karatu: Minti 9
Kashedi: A cikin wannan rahoton akwai bayanai masu tayar da hankali.
Fayaz da matarsa sun yi tunanin sun riga sun tsira a lokacin da wani bam ya fashe: "Muna shiga cikin kwale-kwalen ne ɗaya bayan ɗaya - a nan kawai muka fara ji an fara jefo mana bam."
Hayaniya da ihuce-ihuce kawai kake ji da misalin ƙarfe 17:00 na agogon yankin a ranar 5 ga Agusta, Fayaz ya ce a lokacin da dubban mutanen Rohingya suke turuwar zuwa bakin tekun Naf a birnin Maungdaw.
Harin da aka kai a ƙauyukan yankin ne suka tayar da ɗaruruwan iyalai, ciki har da na Fayaz suke ganin bin tekun ne kaɗai hanyar tsira-dole su tsere daga Kudancin Myanmar zuwa Bangaladesh.
Fayaz na ɗauke ne da jaka cike da duk wani abu da za su iya kwasowa. Ita kuma matarsa tana ɗauke da ƴarsu mai shekara shida, sai kuma babban ɗansu yana biye da su da kuma ƴar uwar matarsa a gaba ita ma riƙe da ɗanta mai wata 8 a duniya.
Bom ɗin farko da aka jefo nan take ya kashe ƴar uwar matarsa. Ɗanta kuma ya ji rauni, amma bai mutu ba.
"Sai na ruga na ɗauko shi... amma sai ya mutu a lokacin da muka fake muna jiran a ƙaƙƙauta jefo bom ɗin."
Shi ma Nisar ya kawo bakin tekun da misalin ƙarfe 17;00, bayan ya yanke shawarar tserewa tare da mahaifiyarsa, da matarsa da ɗansa da ƴarsa da ƙanwarsa. "Mun ji shawagin jirgi ne ta samanmu, kawai sai muka ƙarar fashewar wani abu," inji shi, sannan ya ƙara da cewa, "sai muka faɗi a ƙasa. Sun yi amfani da jirgi mara matuƙi ne wajen jefo mana bom."
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Nisar ne kaɗai ya tsira a cikin iyalansa.
Fayaz, da matarsa da ƴaƴansa mata sun samu nasarar tserewa zuwa tsallaken tekun.
Amma duk da roƙon da Fayaz ya yi, direban jirgin ruwan ya hana shi ɗauko gawar jaririn. "Ya ce babu amfanin ɗauko gawa, sai na haƙa rami a bakin tekun na binne shi."
Yanzu suna Bangladesh, inda ya ɗan fi inda suka fito lumana, amma duk da haka, idan hukumomi suka kama su, za a iya mayar da su ƙasarsu. Nisar na riƙe da Qur'ani, cike da mamakin yadda a ranar ɗaya ya rasa komai.
"Da na san hakan zai faru, da ban yi yunƙutin ficewa daga birnin ba," inji Nisar.
Akwai ɗaure kai da wahalar fahimtar haƙiƙanin abin da ke faruwa a Yaƙin Basasar Myanmar.
Amma BBC ta yi ƙoƙarin bayyana abin da ya faru a ranar 5 ga Agusta ta hanyar tattaunawa kai tsaye da waɗanda abin ya shafa, ciki har da gomman waɗanda suka tsira zuwa Bangladesh, da kuma wasu faya-fayan bidiyo da suka bayar.
Dukkan waɗanda suka tsira ɗin-fararen hula na Rohingya waɗanda ba sa ɗauke da makami- sun yi tariyar abin da ya faru, inda suka bayyana yadda aka ɗauki awa biyu ana musu ruwan bama-bamai. A daidai lokacin da wasu ke cewa an yi amfani da jirage marasa matuƙa ne, wasu kuma na cewa an yi amfani ne da bindigogi da motocin yaƙi. Asibitin Ƙungiyar Likitoci na MSF da ke aiki a Bangladesh ya ce ya samu ƙarin mutanen Rohingya da dama da suka zo da raunuka bayan ranar da lamarin ya faru-kusan rabin waɗanda suka ji raunin matane da ƙananan yara.
Wasu daga cikin bidiyoyi waɗanda suka tsira da BBC ta tantance sun nuna yadda jini ya mamale gaɓar tekun, da kuma mutane da jina-jina, waɗanda mafi yawansu mata ne da ƙananan yara. Sai dai ba a tantance mutum ne suka mutu ba, amma ganau da dama sun tabbatar wa BBC cewa sun ga gawarwaki da dama.
Waɗanda suka tsira sun bayyana mana cewa mayaƙan Arakan, ɗaya daga cikin ƙungiyoyin ƴan ta'adda a Myanmar, wadda a ƴan watannin nan suka fatattaki sojoji baki ɗaya daga Jihar Rakhine ne, suka kawo musu harin.
Sun ce an fara kawo musu harin ne a ƙauyukansu, wanda ya tilasta musu tserewa, sannan aka sake kai musu harin a bakin teku a lokacin da suke yunƙurin tserewa.
AA ta ƙi cewa komai, amma kakakinta, Khaing Tukha ya ƙaryata zargin, inda amsa tambayoyin BBC da sanarwar cewa, "lamarin ya auku ne a yankunan da ba a ƙarƙashinmu suke ba." Sannan ya zargi ƴan gwagwarmayar Rohingya da shirya kisan kiyashin tare da ɗaura wa AA laifin.
Amma duk da haka Nisar yana nan kan fahimtarsa.
"Ƙarya sojojin Arakan suke yi," inji shi. "Su ne suka kawo harin. Su kaɗai ne a yankinmu a ranar, sannan ai sun yi makonni suna kawo mana hare-hare. Ba sa so su bar Musulmi su rayu."
Yawancin Musulmin Rohingya na Myanmar suna zaune ne a Rakhine, inda ba su da yawa-Masu bin addinin Budha sun fi yawa a jihar- inda kuma mazaunan biyu sun daɗe ba sa ga maciji. A 2017, lokacin da sojojin Myanmar suka kashe dubban mutanen Rohingya a wani hari da Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana da, "kisan ƙare dangi,' wasu daga mutanen Rakhine sun taya su wajen kai hare-haren.
Yanzu da rikici yake ƙara ta'azzara tsakanin ƴan ta'adda da AA, wadda ke da goyon bayan mutanen Rakhine, sai lamarin ya ƙara jefa mutanen Rohingya cikin tarko.

Asalin hoton, Handout
Duk da fargabar da suke ciki na yiwuwar kama su a Bangladesh, a mayar da su Myanmar, waɗanda suka tsira daga Rohingya ɗin sun bayyana wa BBC cewa a shirye suke su bayyana yadda lamarin ya faru domin fayyace komai, musamman kasancewar lamarin ya auku ne a yanki da ƴan jarida da ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam ba sa iya zuwa.
"Na rasa komai, ni kaina ban san yadda na tsira ba," in ji Nisar.
Attajirin ɗan kasuwa ne a Rohingya, wanda dole ya sayar da filinsa da gidansa a lokacin da harin ya yi ƙamari. Amma lamarin ya ƙazance cikin sauri fiye da yadda ya yi tsammani, don haka tilas a ranar 5 ga Agusta, dole shi da iyalansa suka bar Myanmar.
Kuka yake yi a lokacin da yake nuna jikin ƴarsa a wani bidiyon: "A hannuna ƴata ta rasu kiran sunan Allah. Sai nake kallo kamar barci take yi. yarinya ce da take sona sosa."
A cikin bidiyon kuma ya sake nuna matarsa da ƙanwarsa jinana lokacin da suke raye. Bai samu damar ɗauko su ba saboda bama-baman na cigaba da faɗowa. Dole ya bar su, sannan daga bisani ya samu labarin cewa sun mutu.

Asalin hoton, BBC/Aamir Peerzada
"Babu inda ya rage da ake zama lafiya, dole muka tsere zuwa rafin domin mu tsallaka zuwa Bangladesh," inji Fayaz. Harbe-harben da jafo bama-bamai sun biyo su ne ƙauya-ƙauye, sannan da aka zo bakin tekun, dole Fayiz ya ba direban kwale-kwalen duka kuɗinsa kafin ya tsallakar da su.
Cikin damuwa da baƙin ciki, yana riƙe da hoton ɗansa jina-jina.
"Idan ba Sojojin Arakan ba ne suka kawo mana hari, so wane ne to?" "Ta inda bama-baman suke fitowa, na san sojojin Arakan ɗin suna wajen. Ko suna nufin tsawa ce ta faɗo daga sama?"
Irin waɗannan zarge-zargen ne ke sanya alamar tambaya a kan sojojin Arakan ɗin, waɗanda suke bayyana kansu da ƙungiyar kawo sauyi ta dukkanin mutanen Rakhine.
Tun bara, sojojin Arakan wato AA, ɗaya daga cikin ƙungiyoyin ƴan bindiga a Myanmar, suke samun galaba a kan sojojin ƙasar.
Amma kuma wannan galabar da ake samu a kan sojojin, shi ne yake ƙara zama barazana ga mutanen Rohingya, waɗanda a da suka bayyana wa BBC cewa ana tilasta musu shiga yaƙi da AA ɗin.
Ɗaya daga cikin waɗanda suka tsira daga harin na 5 ga Agusta ya shaida wa BBC cewa masu ƙayar bayan ARSA, waɗanda suke da alaƙa da na cikin shugabannin sojin da suke mulkin ƙasar suna cikin taron mutanen da suke yunƙurin tserewa a lokacin- wanda wataƙila hakan ya taimaka wajen zafafa harin.
"Ko da kuwa a ce akwai wanda suke hari, to sun yi amfani da ƙarfin tsiya. Akwai mata da yara ƙanana da dattawa a cikin waɗanda aka kashe. kan mai uwa da wabi suka yi," inji John Quinley, darakta Ƙungiyar Kare Haƙƙin ɗan Adam ta Fortify, wada ke bincike a kan harin.
"Don haka babu abin da zai sa mu yarda cewa akwai dalilin abin da ya faru a ranar 5 ga Agusta. Dole a binciki sojojin Arakan, sannan a tuhumi kwamandojin rundunar."
Wannan al'amari ba ƙaramin tashin hankali ba ne ga mutanen Rohingya. Sama da mutum miliyan ne daga cikinsu suka tsere zuwa Bangladesh tun daga shekarar 2017, ƙasar da da suke rayuwa a cikin ƙananan bacoci a wani ƙaramin sansani.
Yanzu haka wasu na ta ƙara zuwa ne saboda yadda yakin ya isa Rakhine, amma ba kamar 2017 ba, lokacin da Bangladesh ta buɗe musu boda suna shiga. Yanzu ƙasar ta ce ba za ta iya barin mutanen Rohingya su cigaba da shiga ƙasarsu ba.
Waɗanda suka tsira, kuma suke da kuɗin hawa kwale-kwale- an faɗa wa BBC cewa ana biyan Burmese kyat 600,000 ($184; £141) duk tafiya ɗaya- sannan dole a shiga Bangaladesh a ɓoye saboda tsere wa jami'an tsaron bodar Bangladesh, ko kuma a ɓoye a sansanin mutanen Rohingya.
Lokacin da Fayaz da iyalansa suka iso Bangladesh a ranar 6 ga Agusta, jami'an tsaron bodar ne suka ba su abinci, sai suka saka su a wani kwale-kwalen suka ce a mayar da su ƙasarsu.
"Kwana biyu muka yi a saman teku babu ci babu sha," inji shi. "Sai na riƙa ɗebo ruwa daga tekun ina ba yarana suna sha, sannan na riƙa roƙon wasu da muke ciki tare da su suna ba mu biskit ina ba su."
Amma sun samu nasarar shiga Bangladesh a zagaye na biyu. Amma aƙalla kwale-kwale biyu ne suke kife saboda mutane sun mus yawa. Wata bazawara, da yaranta guda 10 ta ce ta samu nasarar ɓoye yaranta ne a lokacin da ake jefo bama-baman, amma kuma ruwa ya janye mata yaranta guda biyar.
Tana riƙe da wani jikanta yanzu, wanda iyayensa, da ƙaninsa duk sun mutu.

Asalin hoton, Handout
Amma ina makomar waɗanda aka bari? yanzu ba a samun waya, kuma yanzu makonni ke nan babu layin sadarwa Maungdaw, amma da ƙyar BBC ta samu wani mutum, wanda ya buƙaci a sakaya sunansa saboda tsoro.
"Sojojin Arakan sun tilasta mu barin gidajenmu, sannan yanzu haka suna tsare da mu a wasu makaranta da masallatai," inji shi, sannan ya ƙara da cewa, "ina tsare ne tare da wasu mutum shida ƴan gida ɗaya a wani ƙaramin gida."
Sojojin Arakan sun shaida wa BBC cewa sun tseratar da fararen hula guda 20,000 daga garin. Sun ce suna ba su abinci da magani, sannan suka ƙara da cewa, "muna wannan aikin ne domin tabbatar da tsaro da kariya ga mutanen, ba wai tilasta musu barin garin ba."
Amma wanda BBC ta tattauna da shi ya ƙaryata batun, inda ya ce, "yanzu haka sojojin Arakan ɗin sun faɗa mana cewa za su harbe mu idan muka yi yunƙurin guduwa. Mun fara fuskantar ƙarancin abinci da magani. Yanzu haka ba ni da lafiya, kuma mahaifiyata ba ta da lafiya. Mutane da dama suna fama da amai da gudawa."
Sai ya fashe da kuka, yana roƙon a taimaka musu: "Dubban mutanen Rohingya suna cikin fargaba. Idan za ku iya, don Allah ku cece mu."
A bakin tekun a can tsallekn Bangladesh, Nisar yana zaune yana hangen Myanmar, yana tunanin daidai inda aka kashe iyalansa.
"Ba na fata in koma ƙasar."
Da ƙarin bayani daga Aamir Peerzada da Sanjay Ganguly
*An sauya sunayen mutanen saboda tsaro.












