Ukraine ba ta shirya wa zaman lafiya ba - Putin

Vladmir Putin

Asalin hoton, Getty Images

Shugaba Putin ya kare matakin da fadar Kremlin ta ɗauka na kama wasu masu sukar mamayar da Rasha ta kaddamar a Ukraine.

Ya kuma ce bai yi watsi da ra'ayin tattaunawar sulhu kan rikicin ba.

Vladimir Putin ya amsa tambayoyi da dama a wani taron manema labarai da ya yi da daddare bayan kammala taron Rasha da Afirka a St Petersburg.

Da yake tattaunawa da wani dan jaridar Rasha, ya tambaye shi ko dai dai ne kama mutane don kawai sun furta wasu kalamai, ko sun yi rubuta ra’ayinsu, shugaban ya ce matsawar ana son cimma nasara a rikicin da ake yi da Ukraine, dole ne kowa ya bi wasu ka'idoji ba cutar da Rasha daga cikin gida ba.

Ya nanata matsayin kasarsa na dama damar sasantawa don wanzar da zaman lafiya, sai dai ya ce a duk sa’ad da suka yi kokarin yin hakan, sai Ukraine ta tsagalgale ta yi kunnen kashi.

Ya ce sojojin Ukraine ne ke kai hari, su suke tsanantawa, da fadada hare-harensu, don me za mu amince a tsagaita wuta, ai kamar yarjejeniya zaman lafiya ce, ba mu muka yi watsi da ita ba’.

Yanzu haka dai mahukunta a Rasha sun haramta sukar mamayar da Moscow ta yi wa Ukraine.

Mutanen da aka kama kwanan nan saboda ra'ayoyin da suka saba wa goyon baya sun hada da masu sharhi kan al’amuran yau da kullum, da malaman jami’a da kuma yan adawa.