Valencia ta nemi a ɗage wasanta saboda gobarar da aka yi

..

Asalin hoton, Getty Images

Ƙungiyar kwallon kafa ta Valencia ta nemi a ɗage wasanta da aka tsara yi a ranar Asabar ita da Granada, saboda wata mummunar gobara da ta tashi a birnin.

A ƙalla mutum hudu ne suka mutu bayan wutar ta ratsa wasu gidaje biyu a ranar Alhamis a birnin na ƙasar Sifaniya, abin da ya yi sanadin ɓatan mutum 15.

Valencia wadda aka tsara za ta karɓi baƙuncin Granda a filin wasa na Mestalla a ranar Asabar, yanzu tana jira ta ji hukuncin da La Liga za ta yanke.

Ƙungiyar ta ce "wutar ta girgiza ta".

"Muna bayar da taimakonmu d cibiyoyi da kuma duk wata buƙatar gaggawa da za ta taso ga al'uma," in ji kulob ɗin.

Ɓangaren mata da maza na ƙungiyar sun yi shiru na minti ɗaya gabanin su fara atisaye a ranar Juma'a da safe, kuma za a yi ƙasa da tuta a gine-ginen kungiyar.

An kira jami'an da ke kashe gobara ne da misalin ƙarfe biyar na yammacin Sifaniya, kuma an rika ciro mutane daga ginin da tsanuka.

Sama da tawaga 20 ce ta masu kashe wuta ce ta rika yunkurin kashe wutar, wadda iskar da ake yi ta rika munanata.

Mutum 15 ciki har da masu kashe gobara shida da wani ɗan yaro na cikin waɗanda suka jikkata, amma rayuwarsu ba ta cikin haɗari.

Hukukoki sun ware kwanaki uku domin jimami da abin da ya faru da kuma rayukan da aka rasa.

Valencia na matsayi na takwas a teburin La Liga, maki huɗu tsakaninta da Real Sociedad da ke matsayi na shida.

..

Asalin hoton, Getty Images