Kalaman Buhari kan yajin aikin ASUU sun tayar da ƙura

Asalin hoton, Presidency
Kiran da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi wa ƙungiyar malaman jami'oi ta ASUU na ta janye yajin aiki ya haifar da ce-ce-ku-ce tsakanin ƴan ƙasar.
Ƙungiyar ASUU ta shafe watanni tana yajin aiki. Kuma a lokacin da yake jawabi a Daura, Buhari ya faɗa wa gwamnonin APC da shugabannin jam'iyyarsa cewa "yajin aikin ya isa haka nan."
Buhari ya bayyana damuwa kan tasirin yajin aikin ga makomar ilimi da ci gaban Najeriya.
Ya ce duk da ya fahimci buƙatunsu, amma za a ci gaba da tattaunawa yayin da ɗalibai ke ajin karatunsu.
"Muna fatan ASUU za ta ji tausayin mutane kan tsawaita yajin aikin, gaskiya ya isa haka nan a ajiye ɗalibai a gida," in ji Buhari wanda kuma ya yi kira ga wasu manyan ƴan Najeriya da ke da kusanci da ƙungiyar malaman da su shiga tsakani su shawo kan malaman.
Kalaman na shugaban sun ja hankalin ƴan Najeriya, musamman a kafofin sada zumunta na intanet.
Yajin aikin ASUU ya kasance ɗaya daga cikin batutuwan da aka fi tattaunawa tsakanin Litinin zuwa Talata a shafin Twitter a Najeriya.
Me ƙungyar ASUU ta ce?
Ƙungiyar ASUU ta mayar da martani kan kalaman na Buhari, Inda ta ce ta yi mamakin kalaman na shugaban.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Farfesa Abdulkadir Muhammad shugaban ASUU shiyyar Kano ya shaida wa BBC cewa ba su ji daɗin kalaman na Buhari ba, yana mai cewa “maganar ta fito ne daga bakin mutumin da kamar bai san abin da ke faruwa ba ko halin da kasa ke ciki.”
“A tunaninmu a matsayinsa na shugaban kasa, wannan yajin aikin ba yau muka fara ba, yau an shiga wata biyar, sai muke ganin ƙila ya farka daga bacci ne. Ko kuma ya daɗe bai yi magana ba yanzu ne ya ga damar yin magana kan yajin aikin.”
“Mun yi watanni ba albashi, kuma hakan bai sa mun mutu ba. Don haka maganar fatar baki ba za ta yi maganin yajin aikin ba sai idan gwamnati ta yi abin da ya kamata,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa idan har Buhari ya ce yajin aikin ya isa haka nan, to ai shi ne ya kamata ya ɗauki matakin ganin an kawo ƙarshensa.
ASUU ta ce kwamitin da shugaban ya kafa ne ya kamata ya kira ya fada masu cewa zaman ya isa hakan nan kuma yana son sanin dalilin da ya sa ba a janye yajin aikin ba.
“Komi yana hannun gwamnati idan ta ga dama a janye za a janye,”
Maganar da Buhari ya yi ya nuna wa ƴan Najeriya cewa gwamnatinsa ta gaza ko ba ta san me take yi ba kan muhimmancin ilimi,” in ji Farfesa Abdulkadir.
Me ƴan Najeriya ke cewa?
Ƴan Najeriya da dama sun bayyana ra'ayi kan roƙon da shugaba Buhari ya yi wa ƙungiyar ASUU na ta janye yajin aikin da ta shafe watanni kusan biyar tana yi.
Da dama na ganin idan har gwamnati ta damu da yajin aikin, a nata ɓangaren ya kamata ta yi abin da ya dace.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 1
Wani mai amfani da Twitter a Najeriya @nas9ja tambaya ya yi cewa, shin shi ya yi abin da ya dace da har za su janye yajin aikin? ASUU za ta janye yajin aiki ne kawai idan har gwamnatin tarayya ta yi abn da ya dace ba wai yin barazana ba.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 2
Adesina Ibrahim ya ce: Ba wai roƙon ASUU ba ne, ya kamata a biya buƙatunsu
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 3
@Junipero47 ya ce: Ni ban ga dalilin da zai sa gwamnatin tarayya tana roƙon ASUU ta janye yajin aiki ba maimakon ta nemo mafita, yanzu kusan rabin shekara kenan babu wata amsa daga gwamnatin tarayya.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 4
A ra'ayin Paul Okayim a Twitter, ya ce ƴaƴan talakawa ne za su ci gaba da zama a gida kan yajin aikin ASUU da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa.
Wasu ƴan Najeriya kuma sun buƙaci Buhari da kansa ya zauna da ASUU ya ji korafinsu idan har ya damu.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 5
Buƙatun ASUU
An daɗe ana kai ruwa-rana tsakanin gwamnatin Najeriya da ASUU kan biyan buƙatun da ƙungiyar ke son a biya mata kafin komawa bakin aiki.
Bukatun sun ƙunshi samar da wadatattun kuɗi wanda za a yi ayyuka domin farfado da jami'oi.
Akwai buƙatar biyan alawus na malamai wanda ya taru har ya kai shekaru ba a biya su ba.
Akwai batun samar da wani kwamiti da zai rika ziyartar jami'o'in gwamnatin tarayyar domin ganin irin ayyukan da suke yi don gano nasarori da ma matsaloli da aka samu
Da saɓani kan sabon tsarin biyan albashi na bai-daya da gwamnati ta ɓullo da shi na IPPIS.