Me ya sa ake samun bambancin hukunci a kotunan Najeriya?

Asalin hoton, GETTY IMAGES
- Marubuci, Abdullahi Bello Diginza
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa
- Aiko rahoto daga, Abuja
A ƙarshen makon da ya gabata ne kotun ƙolin Najeriya ta yanke hukuncin ƙarshe kan zaɓukan wasu gwamnonin jihohin Najeriya, inda kotun ta soke wasu hukunce-hukuncen kotun ɗaukaka ƙara kan zaɓukan, tare da tabbatar da wasu.
Alal misali, a shari'o'in zaɓen gwamnan Kano da Zamfara da Filato, duka kotun ƙolin ta soke hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara ta yi ne game da shari'o'in.
A shari'ar zaɓen gwamnan Kano kotun sauraron ƙorafin zaɓe ta cire wa Abba Kabir na NNPP ƙuri'a kimanin 165,000, inda ta ce Nasiru Gawuna na APC ne ya lashe zaɓen.
Sai kuma aka je kotun ɗaukaka ƙara, inda kotun ta ce babu sunan Abba Kabir a rajistar ‘yayan jam'iyyar NNPP da aka gabatar wa hukumar INEC gabanin zabe.
To sai dai Kotun koli ta yi fatali da duk waɗannan hukunce-hukuncen tare da yin kakkausar suka kan kotun ta baya, daga nan kuma ta tabbatar da shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar da aka gudanar ranar 18 ga watan Maris na 2023.
Haka ma batun yake a shari'ar zaɓen jihar Filato inda kotun sauraron ƙorafin zaɓen jihar ta yi watsi da ƙarar da jam'iyyar APC ta shigar gabanta, ta kuma tabbatar da nasarar gwamnan jihar Caleb Muftwang.
To amma sai kotun ɗaukaka ƙara ta soke hukuncin inda ta ce ba Caleb Muftwang ba ne halastaccen gwamnan kasancewar jam’iyyarsa ta PDP ba ta yi biyayya ga hukuncin wata kotu ba game da zaben shugabannin jam’iyyar a jihar ta Filato.
Irin wannan hujja ce ta sa aka soke zaben wasu ‘yan majalisa daga jihar ta Filato, lamarin da ya sa da dama daga cikin su suka rasa kujerunsu kasancewar shari'o'in zaɓensu na ƙarewa ne a kotun ɗaukaka ƙarar.
To amma a lokacin da aka je kotun ƙolin ƙasar, sai ita kuma ta rushe hukuncin kotun ɗaukaka ƙarar inda ta tabbatar da nasarar gwamnan.
Haka zalika a nata ɓangare kotun ɗaukaka ƙarar ita ma ta soke wasu hukunce-hukuncen da kotunan sauraron ƙorafe-ƙorafen zaɓe suka yanke.
Shin me ke kawo bambance-bambancen?
Akwai abubuwa da dama da ke haifar da waɗanna bambance-bambance kamar yadda masana shari'a suka bayyana.
Kuma a kan haka me BBC ta tattauna da wasu masana shari’a guda biyu, wato Farfesa Auwalu Yadudu na jami’ar Bayero da ke Kano, da kuma Barista Bulama Bukarti, lauya mazaunin birnin Landan da ke Birtaniya.
Bambancin fahimtar dokoki

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Farfesa Auwalu Yadudu ya ce kotuna na amfani ne da doka, kuma wadannan dokoki a rubuce suke, to akan samu bambancin fahimta wajen fassara waɗannan dokoki tsakanin alƙalai.
''Ana samun bambancin fahimtar kalamin da aka yi amfani da shi wajen rubuta dokokin, kuma wannan ba wani sabon abu ba ne, domin ko tsakanin malaman addini ma akan samu bambancin fahimtar wasu ayoyi da hadisai'', in ji Farfesa Yadudu.
Barista Audu Bulama Bukarti, wani lauya mai zaman kansa da ke zaune a ƙasar Birtaniya ya ce abu na farko da ke haddasa wannan shi ne kasancewar alƙalan 'yan’adam.
Abin da doka ta ɗora musu shi ne su kalli doka su kuma fassara ta kamar yadda aka gabatar da ita a gabansu.
To amma Bukarti ya ce duk inda aka samu mutum sama da ɗaya wajen fassara wata doka, to dole ne a samu bambancin fassara a tsakaninsu.
Shi ma ya jaddada cewa irin haka na faruwa a wajen malaman addini, inda ake samun bambancin fahimtar wata aya ko hadisi, duk kuwa da cewa kowannensu na da ilimi da tsoron Allah.
''To haka wannan batu yake a ɓangaren alƙalai su ma, hakan ne ma ya sa aka tanadi matakan shari'a daban-daban domin daukaka ƙara idan ba ka gamsu da hukuncin da wata kotu ta yi maka'', in ji Bukarti.
Son rai daga ɓangaren alƙalai
To sai dai Barista Bukarti ya ce idan aka yi la'akari da yadda ake samun bambance-bambance hukuncin kotunan ƙasar abin akwai a bin tayar da hankali.
Barista Bukarti ya ce a hukunci takwas da kotun ƙolin ƙasar ta zartar a makon da ya gabata, uku daga ciki na nuna cewa kotun ɗaukaka ƙara ta yi kuskure.
''Ka ga kuwa a ce hukunci uku duk an samu kurkure ai wannan babban dubawa ne'', in ji shi.
Ya kuma yana ganin wannan ba ya rasa nasaba da son rai da kuma zarge-zargen cin hanci da rashawa da ya shiga ɓangaren shari'ar ƙasar.
''Domin kuwa babu yadda za a yi a ce an samu waɗannan manya-manyan bambance-bambance har guda uku ba''.
Rashin ƙwarewar lauyoyi

Asalin hoton, Getty Images
Farfesa Yadudu ya ce ana samun rashin ƙwarewa tsakanin lauyoyi da ke janyo matsalaa shari'a.
''A wasu lokuta akwai hujja ƙwaƙƙwara da ya kamata lauya ya gabatar a gaban kotu, to idan bai gabatar da ita ba, tabbas za a iya kayar da mutum a shari'a'', in ji shi.
Ya ce a shari'a zaɓen Kano kotun sauraron ƙorafin zaɓe ta zaftarewa gwamnan jihar kuri'a kusan 165, amma lauyoyinn jam'iyyar NNPP ba su jajirce wajen sukar buƙatar janye ƙuri'un da jam'iyyar APC ta yi ba.
"Amma da aka je kotun ƙoli lauyan hukumar INEc da na NNPP sun jajirce, suka kuma bayar da hujjoji ƙwarara fiye da wanda lauyoyinsu suka bayar a kotun farko'', in ji Farfesa Yadudu
A nasa ɓangare Barista Bukarti ya ce kwarewar alƙalai ka iya sauya akalar shari'o'in, to amma ya ce in ma lauyoyin ba su da kwarewa su alƙalan sun san duka dokokin shari'a, don haka duk dokar da lauyoyin suka gabatar ana, tunanin cewa su dole ne su fi lauyoyin sanin aihinin dokokin da kuma aiki da su.
''Don haka ko da lauya bai gabatar masa da doka ba, shi a ɓangarensa ana buƙatar ya yi la'akari da wannan dokar wajen yanke hukuncinsa''.
Shi ma a nasa ɓangare Farfesa Yadudu ya ce duka hukunce-hukuncen da kotunan baya suka yi ba za a ce rashin ƙwarewar alƙalai ba ne, saboda su alƙalai suna hukunci ne kan abin da aka gabatar musu na hujja da shaida da kuma abin da doka ta ce.
Abubuwan da alƙalai ke la'akari da su wajen hukunci

Asalin hoton, Getty Images
Barista Bukarti ya ce a lokacin shari’o i na zabe akwai abubuwa da alƙalai ke la'akari da su wajen zartar da hukunci. Abubuwan su ne:
1 - Dokoki
Akwai manya-manyan dokoki guda uku da alƙalai ke la'akari da su wajen yanke hukunci a shari’ar da ta shafi zabe, kamar yadda Barista Bukarti ya bayyana.
Dokokin kuwa sun hada da dokokin kundin tsarin mulkin ƙasa, da dokar zaɓe da kuma kundin gudanar da zaɓe wato election manual da hukumar INEC take yi.
Wadannan manya-manyan dokokin uku su alƙalai ke dubawa, in ji Barista Bukarti.
2 - Hujja da shaidu

Asalin hoton, Getty Images
Farfesa Yadudu ya ce hujjar da ake gabatarwa a gaban kotu iri-iri.
Yadudu ya ce babban abin da alƙalai ke la'akari da shi wajen yanke hukunci shi ne hujja tabbatacciya da aka gabatar musu, wadda kuma ba a soke ta ba a gaban kotun.
''Alƙalai na la'akari da hujja tabbatacciya da aka gabatar musu, wadda ba a soke ta ba ko aka yi mata yankan tsaye kuma sun gamsu cewa shaidar da aka gabatar musu ingantacciya ce'', in Farfesa Yadudu.
Barista Bukarti ya ce ''ita doka cewa ta yi idan abu kaza ya faru to ga hukunci, to kuma babu yadda za a tabbatar da wannan abun ya faru sai ta hanyar hujjoji da kuma shaidu''.
Ya ƙara da cewa a shari'o'in zaɓe manya-manyan shaidu iri biyu ake gabatarwa.
Na farko shaidu na mutane waɗanda za su zo gaban kotun su bayyana haƙiƙanin gaskiyar abin da suka gani ko suka ji ko suka rubuta.
Na biyu shi ne sahihan takardu, ko takardun zaɓe ko na makaranta da sauran takardun da ke da alaƙa da wannan shari'a.
3 - Hukuncin kotun ƙoli na baya
Haka kuma Farfesa Yadudu ya ce alƙalai musamman a kotunan ƙasa da na tsakiya kan yi la'akari da hukuncin da kotun ƙoli ta bayar a kan wata shari'a mai kamanceceniya da irin wadda ke gabansu domin bayar da hukunci.
Masanin shari'ar ya ce kotunan kan yi la'akari da irin shari'un da kotun ƙoli ta yanke a baya domin gudanar da wata shari'a da ke gabansu.
"Ba kima da martaba ba ne kotu ta taɓa yanke hukunci a baya, yanzu kuma ta yanke wani hukunci daban da ya saɓa wa hukuncin da kotun ƙolin ta taɓa bayarwa a baya'', in ji shi.
Ya ƙara da cewa hatta ita kanta kotun ƙolin bai kyautu ta yi wani hukuncin da ya saɓa wa wanda ta taɓa yi a baya kan wata shari'a da ke kamanceceniya da wadda ke gabanta ba.
Abin da alƙalan kotun ƙoli ke la'akari da shi

Asalin hoton, SUPREME COURT
Barista Bukarti ya ce akwai wani abu da alƙalan kotun ƙoli ke la'akari da shi, wanda kuma shi ne buƙatar al'umma.
''Misali a ce idan aka rusa shari'a kaza yaya wannan hukuncin zai shafi wannan al'umma ko kuma ƙasa baki-ɗaya''.
Barista Bukarti ya ci gaba da cewa ''misali idan ka rusa zaɓen shugaban ƙasa to ka ga biliyoyin da aka kashe wajen shirya zaɓen ke nan duka sun tafi a banza, sannan yawan kwanakin da aka kwashe ana shirye-shiryen zaɓen da dakatar da mutane da aka yi daga zuwa aiki da zuwa wuraren sana'o'insu da sauran harkokinsu a ranar zaɓukan duka an dawo da hannun agogo baya, sai an je an sake wannan gaba-ɗaya''.
''To a nan sai a ce a duba masalahar al'umma wato ''public interest'', to a nan sai alƙalan su ce idan har akwai kuskure ma a cikin zaɓe, idan kuskuren bai zama mai girma sosai da ya yaɗu sosai ba har ya kawo mummunan rashin adalci ga wani ɓangare ba, to a bar wannan zaɓen a matsayin ya yi daidai ya fi a maimakon a ce za a rushe domin sake kashe kuɗi a ɓata lokaci watakila ma a rasa rayuka wajen sake zaɓen'', in ji Barista Bukarti.











