Manyan kalubale a zaɓen Afirka ta Kudu

Jami'an zabe

Asalin hoton, AFP

A wannan Larabar al'ummar Afirka ta Kudu ke kada kuri'unsu a zabe mafi muhimmanci tun bayan kawo karshen mulkin wariyar launin fata a shekara ta 1994.

Fiye da mutum miliyan 27 ne suka yi rijista domin kada kuria'arsu a zaɓen da ake ganin zai kasance kalubale ga jam'iyyar ANC mai mulki.

Akwai jam'iyyu 70 da ake da su, da kuma wasu 11 masu zaman kansu da za su fafata a zaben na 'yan majalisar dokoki da kuma shugabannin larduna.

Nelson Mandela ne ya jagoranci kawo karshen mulkin farar fata a ƙasar a karkashin jam'iyyar ANC da ke neman wa'adi na bakwai a kan mulki.

Sai dai a karon farko ana ganin jam'iyyar za ta iya rasa mafi yawancin kujerunta a majalisar dokokin kasar abin da zai tursasa mata haɗewa da wasu jam'iyyun adawa.

Ana sukar gwamnatin da ke kan mulki da aikata abubuwa da dama kama da ga batun cin hanci da rashawa da kuma rashin aikin yi musamman a tsakanin matasa abin da ke janyo aikata munanan laifuka a kasar.

Babbar jam'iyya adawa a kasar ta DA, wato Democratic Alliance, ta sanya hannu kan wata yarjejeniya tare da wasu jam'iyyu 10, inda suka amince da kafa gwamnatin haɗaka idan har suka samu kuri'un da suka kamata domin su hambarar da jam'iyyar ANC mai mulki.

To amma ba lallai hakan ta yiwu ba saboda ita kanta jam'iyyar ANC na ganin za ta iya sake samun nasara a zaben, inda itama ta ke neman jagorantar jam'iyyun haɗaka.

A zaben da ta gabata ta samu kashi 57 da digo biyar cikin 100 na kuri’un da aka kada idan aka kwantanta da DA da ta samu kashi 21 cikin 100.

Tsohon shugaban kasar Jacob Zuma, ya bayar da mamaki bayan da ya sanar da cewa zai bar jam'iyya a watan Disambar bara tare da sanar da sabuwar jam'iyyar da ya koma ta MK.

Kodayake dama dai an hana shi tsayawa Takara saboda laifin raina kotu.

Ana ganin shi ma zai iya samun kashi 10 cikin 100 da za a kada.

Adadin matan da suka yi rijista ya kai kashi 55 cikin 100 wato kusan miliyan 15 kenan a cewar hukumar zaɓen kasar.

Kuma yawanci matasa 'yan tsakanin shekarun 30 zuwa 39 ne suka fi rijista a zaben inda adadinsu ya kai miliyan 26 da dubu dari bakwai.

An dai girke jami'an tsaro a runfunan zaben da ke sassan kasar domin tabbatar da cewa an yi shi cikin lumana.