An yanke wa 'yan luwadi hukuncin kisa a Bauchi

Asalin hoton, Getty Images
Wata babbar kotun shari’ar Musulunci a Bauchi da ke arewacin Najeriya ta yanke wa mutum uku hukuncin kisa ta hanyar jefewa, bayan ta same su da laifin yi wa wasu yara luwadi.
Lamarin ya faru ne a karamar hukuma Ningi.
Kotun ta samu mutanen uku, da suka hada da matasa biyu da kuma wani babban mutum da mai sama da shekara 70, da wannan laifi, wanda suka amsa.
Sai dai wani jami’in kotun, wanda ya yi wa BBC bayani, ya ce babu wani lauya da ya wakilci mutanen a yayin zaman shari’ar, da kotun ta yanke hukunci ranar Laraba, 29 ga watan Yuni, 2022.
Kwamandan Hisbah na karamar hukumar ta Ningi, Adamu Dan Kafi, ya shaida wa BBC cewa an kama mutanen ne a kauyen Wada a watan Mayu, bayn da suka yaudari yaran da dabino da kuma kwakwa.
Mutanen suna da damar daukaka kara cikin wata daya.
Wani hukuncin a Jihar Filato
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A wata shari’ar kuma a jihar Filato da ke arewa maso tsakiyar Najeriya, wata babbar kotu ta yanke wa wasu mutane uku hukuncin kisa ta hanyar rataya ko allurar guba.
Kotun ta same su ne da laifin kasha wani matashi ta hanyar daba masa wuka.
Lamarin ya faru ne a lokacin wani sabani tsakanin matasan a lokacin bikin Kirsimeti a 2015.
Lauyan mutanen David Adudu, ya gaya wa BBC cewa ba su gamsu da hukuncin ba, wanda kotun ta yi ranar Alhamis, 30 ga watan Yuni, 2022, kuma suna shirin daukaka kara.
Mutum na hudu da aka gurfanar kan laifin kisan ya rasu kafin a gama shari’ar.
Masu gabatar da kara sun bayyana gamsuwarsu da hukuncin da cewa an yi adalci.
Sai dai a Najeriya ba kasafai ake aiwatar da hukuncin kisa ba, yawanci saboda batun kare hakkin dan-Adam.
A maimakon haka, wadanda aka yanke wa hukuncin kisa kan zauna a gidan yari har sai abin da hali ya yi.
A bisa doka, a Najeriya, sai gwamnan jihar da aka yanke hukuncin ya sanya hannu kafin a aiwatar da shi.











