Kotu ta yanke wa fasto hukuncin kisa a Najeriya

Asalin hoton, Getty Images
Wata kotu a jihar Ondo da ke kudu maso yammacin Najeriya ta yanke wa wani fasto hukuncin kisa sakamakon samunsa da laifin kashe wani yaro ɗan shekara 11 kan zarginsa da satar masa kifi wajen kiwon kifinsa.
Antoni Janar na jihar Ondo Adekola Olawoye ya shaida wa BBC cewa batun kisan yaron ya samo asali ne tun a 2016 inda lamarin ya faru a yankin Oke-Igbo na jihar ta Ondo.
Ya bayyana cewa Fasto Kolawole Samson ya kama wasu yara uku suna kamun kwaɗi ba bisa ƙaida ba, amma yara biyu sun tsere sai ya kama na ukun su wanda shi ne ke da shekaru 11.
A cewar Antoni Janar na jihar, daga nan ne faston ya tafi da yaron gida inda ya sassare shi da adda a kansa, daga baya yaron ya mutu sakamakon raunin da ya samu.
Kotun da ke zama a Akure babban birnin jihar ta samu faston da laifin kisa inda ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya. Sai dai faston ya musanta zargin da ake yi masa na aikata kisan.
A halin yanzu, faston na da damar ɗaukaka ƙara nan da kwanaki 90 ƙarkashin ƙundin tsarin mulkin Najeriya. Haka zalika, kafin rataye faston, sai gwamnan jihar ya saka hannu kafin a aiwatar.







