Laifuka a Kano: Mutanen da aka yanke wa hukuncin kisa a jihar a 2020

..

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan da BBC Hausa ta samu sun nuna cewa mutum tara aka yanke wa hukuncin kisa a jihar Kano da ke arewacin Najeriya daga watan Janairu zuwa watan Agustan 2020.

Takardun kotuna daban-daban da BBC Hausa ta samu sun nuna cewa an yanke hukunce-hukunce kan mutanen ne bayan samunsu da hannu a aikata mabambanta laifuka.

An samu bakwai daga cikinsu da aikata kisan kai, mutum ɗaya ya aikata fyaɗe yayin da aka kama ɗaya da laifin ɓatanci ga Annabi Muhammadu (SAW).

An yanke hukuncin farko ne ranar 11 ga watan Fabrairu, inda za a kashe Ali Abdullahi ta hanyar rataya bayan samunsa da laifin kisan kai.

Wannan layi ne

Ga jerin mutanen da aka yanke wa hukuncin kisan:

Ali Abdullahi

Kotu mai lamba Shida ta kama shi da laifin kisan kai inda ranar 11 ga watan Fabrairu aka yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Yakubu Ɗalha

Shi ma Yakubu Kotu mai lamba Shida ce da ke birnin Kano ta kama shi da laifin kisan kai, kuma ranar 3 ga watan Maris ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Abdullahi Isyaku

Babbar Kotun Kano ta same shi da laifin kisan kai kuma ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya ranar 16 ga watan Maris.

Mujahid Sa'id

Kotu mai lamba 13 ta same shi da laifin kisan kai inda a ranar 24 ga watan Maris ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya.

..

Asalin hoton, Getty Images

Wannan layi ne

Naziru Ya'u

Kotu mai lamba Ɗaya ta same shi da laifin aikata kisan kai inda ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya ranar 13 ga watan Yuli.

Shehu Ado Shehu

Kotu mai lamba Shida ce a Kano ta same shi da laifin kisan kai kuma a ranar 26 ga watan Yuni ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Isah Auta

Kotu ta mai lamba Ɗaya ta yanke hukuncin kisa ta hanyar ratayewa a kan Isah Auta bayan ta kama shi da laifin kisan kai. An yanke masa hukuncin ne ranar 29 ga watan Yuni.

Yahaya Aminu

Babbar Kotun Shari'a ta jihar Kano ce ta same shi da laifin yin ɓatanci da Annabi Muhammadu (SAW), inda ranar 10 ga watan Agusta ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Mati Abdu

Shi ma Babbar Kotun Shari'a ta Kano ta kama shi da laifin fyaɗe kuma ranar 12 ga watan Agusta ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar jefewa.

Wannan layi ne