Osimhen ya fi son komawa Chelsea fiye da Saudiyya, Sterling na son Man U

Asalin hoton, Getty Images
Dan wasan Najeriya mai taka leda a Napoli Victor Osimhen, mai shekara 25, zai fi son komawa taka leda a Chelsea maimakon kulub din Saudiyya kamar yadda ake yada jita-jita. (i)
Shi ma dan wasan Ingila Raheem Sterling, mai shekara 29, zai fi son komawa Man U, sai dai ba zai ci gaba da tattaunawa kan hakan ba har sai ya gama tattaunawa kan kwantiraginsa da Chelsea. (Telegraph - subscription required)
Crystal Palace na gab da amincewa dauko dan wasan Ingila mai taka leda a Arsenal Eddie Nketiah kan kudi sama da fam miliyan 30. (Athletic - subscription required)
Celtic na son dan wasan Faransa Odsonne Edouard, mai shekara 26, daga Crystal Palace. (News Shopper)
Atletico Madrid na duba yiwuwar dauko dan wasan tsakiya na Portugal mai taka leda a Manchester City Matheus Nunes, ko da ya ke har yanzu ba su yi wa kungiyar dan wasan tayin karbo shi aro ba. (Athletic - subscription required)
Golan Georgia, Giorgi Mamardashvili zai yi gwajin lafiya a Sifaniya a ranar Litinin, bayan kammala daidaitawa kan kudi fam miliyan 30, domin komawa kungiyar Liverpool. Dan wasan mai shekara 23 zai ci gaba da zama a Valencia, ya yin da zai koma Merseyside a lokacin bazarar shekarar 2025. (Times - subscription required),
Nottingham Forest na shirin dauko dan wasan tsakiya na Ingila James Ward-Prowse, 29, wanda ba ya cikin 'yan wasan da sabon manajan West Ham Julen Lopetegui ke muradi. (Football Insider)
West Ham din ka iya sauraron tayi kan dan wasa Ward-Prowse, sai dai ba wai sun zaku su saida dan wasan ba ne. (Sky Sports)
Fam miliyan 29 da Nottingham Foresta kebe kan dan wasan Mexico mai taka leda a Feyenoord Santiago Gimenez, sun tashi a banza, bayan dan wasan ya yi watsi da tayin da sukai a kan shi. (Telegraph - subscription required)











