Victor Osimhen ba zai buga wa Najeriya gasar kofin nahiyar Afirka ba

Victor Osimhen

Asalin hoton, Getty Images

Victor Osimhen zai yi jinyar wata uku kamar yadda Napoli ta sanar ranar Talata, bayan raunin da ya ji a karshen mako.

Hakan na nufin mai shekara 22 ba zai buga wa Super Eagles gasar cin kofin nahiyar Afirka ba da za a fara ranar 9 ga watan Janairu a Kamaru.

Dan kwallon ya ji rauni ne ranar Lahadi a gasar Serie A da Inter Milan ta doke Napoli da ci 3-2 ranar Lahadi.

Osimhen, shine kan gaba a ci wa Napoli kwallaye mai tara a raga a wasa 14 a bana, an kuma canja shi a minti na 52, bayan da ya ji ciwo sakamakon karo da ya yi da dan kwallon Inter Milan, Skriniar.

Wannan labarin zai ja koma baya ga Najeriya da kuma Napoli, bayan da dan kwallon ke kan ganiyarsa.

Osimhen ya ci wa Napoli kwallo biyar a Serie A da kuma hudu a Europa League a kakar nan, sannan ya ci wa Super Eagles kwallo biyar da hakan ya sa ta kai wasan cike gurbi a shiyyar Afirka da za a yi cikin Maris a wasannin neman shiga gasar cin kofin duniya.

Haka kuma ya yi kan-kan-kan wajen cin kwallaye a wasannin neman shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka da za a yi a badi a Kamru.