Kasuwar 'yan kwallo: Victor Osimhen ya yi wa United tsada, Madrid ta matsu ta ɗauko Mbappe

.

Asalin hoton, Getty Images

Manchester United ba ta shirya biyan fam miliyan 100 ba domin sayen ɗan wasan gaban Najeriya mai shekara 23 Victor Osimhen daga Napoli. (Star)

Manchester United ɗin ta kuma nuna sha'awarta kan ɗan wasan tsakiyar Sporting Lisbon mai shekara 26 Joao Palhinha, inda ta tura masu farautar ƴan wasa su je su kalli wasan shi sau takwas a wannan kakar. (Record, via Sun)

Ƙungiyar Inter Miami ta David Beckham za ta yi duk mai yiwuwa domin ganin ta sayi Lionel Messi idan ɗan wasan mai shekara 34 na Argentina ya ce zai bar Paris St-Germain a farkon kakar nan. (Miami Herald, via Mail)

Real Madrid ta ƙagara ta kammala yarjejeniyar da ta saka a gaba ta sayen ɗan wasan gaban Faransa Kylian Mbappe mai shekara 23 daga PSG kafin kulob ɗin ya soma batun sauran cinakayyar 'ƴan wasa da tsawaita musu kwantiragi.

Jonathan David wanda Arsenal ke nema ya shirya barin Lille a ƙarshen wannan kaka, wanda wannan wata dama ce ga Gunners ɗin su ƙulla yarjejeniya da ɗan wasan na Canada mai shekara 22 a ƙarshen kaka. (Sky Germany, via Express)

Ɗan wasan Ingila Bukayo Saka na cikin "farin ciki" a zamansa da yake yi a Arsenal duk da rahotannin da ke cewa ɗan wasan mai shekara 20 ya dakatar da tattaunawa kan batun kwantiraginsa. (Fabrizio Romano)

Nottingham Forest ta soma tattaunawa da ɗan wasan tsakiyar Ingila Ryan Yates mai shekara 24 a daidai lokacin da suke ƙoƙarin ganin sun riƙe Brennan Johnson wanda ake alaƙantawa da komawa Tottenham. (Mirror)

LA Galaxy ita ma tana son sayen goggen ɗan wasan bayan Sifaniya Sergio Ramos mai shekara 35 wanda ya yi ta gwagwarmaya a PSG samakon rashin lafiya.

Ajax na son ɗaukar mai bayar da shawara kan wasanni na Barcelona Jordi Cruyff a matsayin sabon daraktan wasanninta bayan Marc Overmars ya tafi. (Marca - in Spanish)

Juventus ce kan gaba a wajen neman ɗan wasan Italiya mai shekara 22 Nicolo Zaniolo inda ta ke kawo cikas wajen ƙoƙarin da Roma ke yi na sabunta kwantiraginsa.