Abin da ya sa Sarki Charles ba zai halarci taron COP27 na bana ba

Fadar Buckingham ta sanar cewa Sarki Charles ba zai halarci taron sauyin yanayi na COP27 ba da za a gudanar a Masar nan gaba a wannan shekarar.

Fadar tana mayar da martani ne kan wani labari da aka wallafa a jaridar The Sunday Times wanda ya yi iƙirarin Firaiminista Liz Truss ta umarci Sarkin da kada ya halarci taron.

Fadar ta ce Sarkin ya nemi shawara inda Ms Truss ta bayar. "Bisa mutuntaka da girmama juna, akwai wata yarjejeniya da ke cewa Sarkin ba zai halarci taron ba," in ji Fadar.

Kafin hawansa kan mulki a watan da ya gabata, Sarkin - a wannan lokacin Yariman Wales - ya nuna ba zai je taron na shekara-shakera ba. Wakilin BBC a Masarautar Johnny Diamond ya ce BBC ta bayyana wa Masarautar cewa dole ne Sarkin ya ji takaici ganin yadda ya shafe shekaru da dama yana fafutukar kare muhalli.

Amma Fadar ta mayar da martani cewa nuna Sarkin bai ji daɗi ba, ba haka lamarin yake ba kuma yana lura da batun yin aiki bisa shawarar gwamnati.

A watan Nuwamba, a lokacin da yake matsayin Yarima, Sarkin ya yi bulaguro zuwa Masar tare da amincewar gwamnatin lokaci domin ya nemi gwamnatin Masar kan ƙoƙarinta, ganawa da Shugaba Abdel Fattah Al-Sisi yayin wata ziyara.

A baya, Sarkin ya nuna jajircewarsa kan batutuwan da suka shafi muhalli kuma a matsayin Yariman Wales, yana da daɗaɗɗn tarihi game da yaƙin rage mummunan tasirin sauyin yanayi.

A shekarar da ta gabata ne kawai ya yi jawabi a bikin buɗe taron COP26 a Glasgow, lokacin da Birtaniya ta karɓi baƙuncin taron. Marigayiya Sarauniya ita ma ta gabatar da jawabi a taron.