Rayuwar Sarki Charles na III cikin hotuna

Charles III, da ya kasance yarima mai jiran gadon sarautar Birtaniya mafi dadewa a tarihi, a yanzu ya zama Sarki.

Ya dauki shekara 70 a matsayin mai jiran gadon sarautar ta Birtaniya, wanda hakan ya sanya shi mutum mafi shekaru da yawa da ya zama sabon Sarki.

Ga wasu daga cikin muhimman hotunan rayuwar Sarki Charles na III mai shekara 73 a yanzu.