Yadda ake ƙoƙarin sulhu tsakanin Bello Turji da malaman addini a Najeriya

Asalin hoton, FB/Sheik Ahmad Gumi
A Najeriya, Masana sun fara sharhi kan wasu rahotannin da ke nuna cewa an cimma yarjejeniya da ƙasurgumin ɗanbindigan nan da aka dade ana nema ruwa a jallo, wato Bello Turji.
Hakan dai ya biyo bayan yunkurin da wani kwamiti na musamman da ya ƙunshi malaman addinin musulumci ya yi, da nufin ƙulla yarjejeniyar sulhu.
Daya daga cikin malaman musuluncin da ke cikin kwamitin, Malam Musa Yusuf wanda aka fi sani da Asadus-Sunnah, ya yi bayani a wajen wani taron wa'azi a Kaduna, cewa Bello Turjin ya sako mutum talatin da biyu da ya yi garkuwa da su, tare da bayar da wasu daga cikin makamansa.
Wannan a cewar Malam Asadus-Sunnah, nasara ce daga cikin nasarorin da masu fatan ƙulla sulhu da ƴanbindiga k alfahari da samu a game da yunƙurin magance matsalar tsaro a tsaknin al'umarsu.
Ɓullar wani bidiyo da Malam Asadus-Sunnah ke wannan bayani a ciki ya janyo martini daga masu ruwa da tsaki da kuma musamman jama'ar yankin Arewa maso Gabas da harkokin ƴanbindiga irin su Bello Turji ya fi shafa.
Dr Audu Bulama Bukarti, wani mai nazari ne a kan ƙungiyoyin ta'addanci a Afirka, kuma yana ganin irin wannan sasanci ba laifi ba ne.
Ya ce: ''abu ne mai kyau idan an yi shi bisa tsari kuma an lura da abubuwan da ya kamata a lura da su wajen yin sulhun.''
Mai Nazari a kan harkokin tsaron ya ce ƙulla sulhu mai ɗorewa a kan matsalar tsaro irin wannan tana buƙatar janyo mutane daga dukkan ɓangarorin da abin ya shafa.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ya ƙara da cewa ''a tattaunawar da na ji shi Malam Asadus-Sunnah ya yi, bai kawo cewa an tuntuɓi wakilan al'ummar da aka cutar, aka ɗaiɗaita gidajensu aka kuma kashe ƴan'uwansu ba.
''Ya dai ce sun yi zama da ƴanbindiga, kuma daga abubuwan da ya bayyana, za ka iya lura cewa mai yiyuwa akwai sa hannun gwamnatin tarayya a wannan batu.''
A kan haka ne, Dr Audu Bulama Bukarti ya lissafo abubuwan da yake ganin sai an aiwatar da su ne za a iya cimma nasarar ƙulla yarjejeniyar sulhu da ƴanbindiga, musamman irin su Bello Turji.
Abubuwan da masanin tsaron ya lissafo sun haɗa da:
- A tabbatar cewa duk abin da za a yi, an yi shi tare da dukkan al'ummar da abin ya shafa.
- Lallai ne a lura da kura-kuran da aka yi a baya, don a baya gwamnatoci sun yi ta ƙoƙarin irin wannan sulhun kuma wasu daga ƴanbindigar sun yi yaudarar cewa sun karɓi sulhun, amma daga baya suka dawo suka ci gaba da ta'addancin su.
- Idan da hannun gwamnatin tarayya kamar yadda shi Malam Asadus-Sunnah ya ke nunawa, to lallai ne gwamnati ta fito ta yi wa ƴan Najeriya bayani dalla-dalla: me ya sa ta ɗauko wannan hanyar, wane alfanu ta ke ganin za a samu, wane shiri ne da su na tabbatar da cewa waɗanda za su shiga wannan shulhun ba za su koma ruwa daga baya a ga Ungulu ta koma gidanta na samiya kamar yadda aka gani a baya ba?
- Sannan ina mafita ga su al'umma da aka ɗaiɗaita, ina dukiyoyin su da suka rasa, ina rayukan ƴamn'uwa da suka rasa, ina cin zarafin su da aka yi masu, shin gwamnatin tarayya za ta yi wani tsari na basu diyya da kuma maida su gidajen su, da kuma tallafa masu, ko kuwa dai iya ɓangaren su ƴan ta'addan kawai za a duba, ba za a duba al'ummar da abin ya shafa ba?
- Dangane da fargabar da wasu ke yi kan kada wajen gudun gara a faɗa gidan zago, a game da wannan yunƙuri kuwa, Dr Audu Bulama Bukarti ya ce babu makawa tubalin shiri irin wannan shi ne adalci.
Ya ƙara da cewa ''Na san cewa malaman da suka je sulhu suke nema, zaman lafiya suke nema, to amma ba a samun zaman lafiya sai da adalci, kuma adalcin nan shi ne a dubi dukkan ɓangarori, a dubi menene matsalolin su, a kuma yi ƙoƙarin magancewa.''
Masanin tsaron ya yi gargaɗin cewa za a iya faɗawa babbar matsala idan aka yi kuskure wajen yin wannan.
Wannan shirin sulhu na baya-bayan nan da ƴanbindiga dai, ana iya cewa wani zakaran gwajin dafi ne, kuma tasirinsa da dorewarsa su za su tabbatar da ingancinsa ko akasin haka, musamman ta la'akari da halin da ake ciki dangane da matsalar tsaro a Najeriya.










