Yayin da rikicin Gabas ta Tsakiya ke ƙara ruruwa, me za a yi a kawo ƙarshensa?

Asalin hoton, EPA-EFE/REX/Shutterstock
- Marubuci, Paul Adams
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakilin Difilomasiyya
- Lokacin karatu: Minti 5
Hotunan da muka dinga gani cikin shekara ɗaya da ta wuce masu tayar da hankali ne ƙwarai.
Yayin da har yanzu Isra'ila ke jimamin harin da 'yanbindingar Hamas suka kai mata mafi muni a tarihi, da kuma yadda aka jefa cikin bala'in luguden wuta, lamarin ya yi kama da wata sabuwar turba a yankin gaba ɗaya.
Rikicin Isra'ila da Falasɗinawa na tsawon shekaru da muka kwana biyu ba mu gani ba ya sake kunno kai.
Abin ya bai wa kowa mamaki, saboda mako ɗaya kafin ɓallewar rikicin mai bai wa shugaban Amurka shawara kan tsaro, Jake Sullivan ya faɗa cewa: "Yankin Gabas ta Tsakiya ya ɗan yi shuru yanzu sama da yadda aka saba gani shekara 20 da suka wuce."
Shekara guda kenan yanzu yankin yana ci da wuta.
An kashe sama da Falasɗinawa 41,000. An raba mazauna Gaza miliyan biyu da muhallansu. A gaɓar yamma da Kogin Jordan kuma, an kashe wasu Falasɗinawan 600. A Lebanon, an raba wasu sama da miliyan ɗaya da nasu muhallan da kuma kashe wasu sama da 2,000.
'Yan Isra'ila fiye da 1,200 aka kashe a ranar da Hamas ta kai harin. Tun daga lokacin kuma Isra'ila ta yi asarar wasu sojojin 350 bayan ƙaddamar da samame ta ƙasa a Gaza. 'Yan ƙasar sama da 200,000 ne aka tilasta wa tserewa daga gidajensu da ke kan iyakokin Gaza da Lebanon. Ƙungiyar Hezbollah ta kashe kusan Isra'ilawa 50 cikinsu har da sojoji.
A faɗin Gabas ta Tsakiya, wasu sun shiga yaƙin. Yunƙurin Amurka na shiga tsakani, da suka haɗa da ziyarce-ziyarce na jami'an difilomasiyya, da kuma kai manyan kayan yaƙinta, gaba ɗaya ba su yi amfani ba.
An yi ta harba rokoki daga Iraƙi da Yemen - ƙasashe masu nisa daga Isra'ilar.
Ga kuma abokan gaba biyu Iran da Isra'ila da suka yi wa juna ɓarin wuta, inda ake sa ran za a sake yi.
Ba a fiya samun lokacin da Amurka ke nuna gazawa ba a fili kamar yanzu.
Rayuwar mazauna Gaza kafin 7 ga watan Oktoba ta kusa ɓacewa a zukatan al'umma yayin da mafi yawan kafofin yaɗa labarai suka mayar da hankali kan yiwuwar "barkewar gagarumin yaƙi" a Gabas ta Tsakiya baki ɗaya.
Su ma wasu Isra'ilawa da aka sauya wa rayuwa sakamakon harin Hamas na jin cewa ba a ba su kulawar da ta dace.

Asalin hoton, Reuters
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ba duka Isra'ilawa ne ke da sassauci game da halin da ake ciki ba. Da yawa daga cikinsu na ganin hare-haren Hamas da kuma sauran ƙungiyoyin da ƙasar faɗa da su yanzu shiri ne na shafe Yahudawa daga duniya.
Ganin yadda Isra'ila ta mayar da martani - ta hanyar farfasa na'urorin pager a Lebanon, da kashe ɗaiɗaikun shugabannin ƙungiyoyi, da muggan hare-hare ta sama - ya sa wasu na jin alfahari da ƙasarsu ya dawo.
"Babu inda Isra'ila ba za ta iya kaiwa ba a Gabas ta Tsakiya," kamar yadda Netanyahu ya yi alfahari a makon da ya gabata.
Farin jinin firaministan ya yi ƙasa sosai watanni bayan harin ranar 7 ga watan Oktoba. Yanzu ya fara farfaɗowa.
Ko za a ce kamar wani lasisi ne yake samu na ci gaba da abin da yake yi?
Sai dai abin tambayar a nan shi ne, har zuwa ina za a dakata?
"Babu wanda ya san lokacin da za a tsahirta da kuma inda kowa zai tsinci kansa a lokacin," a cewar Simon Gass, tsohon jakadan Birtaniya a Iran yayin hirarsa da BBC.
Har yanzu akwai hannun Amurka a cikin abubuwan nan. Yayin da zaɓen shugaban ƙasar ya rage mako huɗu kacal da kuma yadda Gabas ta Tsakiya ke sake rincaɓewa, wannan ba lokaci ne da Amurkar za ta ɗauki manyan matakai ba.
A yanzu dai babban ƙalubalan shi ne kawo ƙarshen rikicin da ake yi.
Ƙawayen Isra'ila baki ɗayansu na ganin tana da 'yanci - ko kuma ma wajabci - rama harin makamai masu linzami da Iran ta kai mata.
Ba a kashe mutum ko ɗaya ba a Isra'ila saboda yadda Iran ta hari gine-ginen soja, amma Mista Netanyahu ya ci alwashin mayar da zazzafan martani.

Asalin hoton, EPA-EFE/REX/Shutterstock
Bayan makonni tana samun nasarori, da alama hakan sun ƙara wa Netanyahu dogon buri.
Cikin wani jawabi da ya yi wa Iraniyawa, ya nuna cewa akwai shirin sauya gwamnati a ƙasar. "Idan Iraniyawa suka samu 'yancin kansu, kuma lokacin na tafe nan gaba kaɗan, komai zai sauya," in ji shi.
Wasu masu sa ido na ganin manufarsa na ɗauke da irin kalaman da wasu jami'an Amurka suka dinga yaɗawa daf da lokacin da Amurkar ke shirin auka wa Iraƙi a 2003.
Gwamnatin ka iya burin ganin bayan Isra'ila, amma tana sane sarai cewa ba ta da ƙarfin da za ta iya tunkarar ƙasar da ta fi kowacce ƙarfi a Gabas ta Tsakiya, musamman a daidai lokacin da Hezbollah da Hamas - manyan ƙawayenta na "ƙawancen gwagwarmaya" - suke shan luguden wuta.
Ita ma Isra'ila da ke neman kawo ƙarshen barazanar Iran, na sane cewa ba za ta iya yin hakan ita kaɗai ba, duk da nasarorin da ta ɗan samu kwana biyu.
Ba sauyin gwamnati ne a gaban Shugaba Joe Biden ba, har ma da mataimakiyarsa Kamala Harris.
A wajen Donald Trump kuma, karo na ƙarshe da ya kusa kai wa Iran ɗin hari - bayan ta harbo wani jirgin leƙen asirin Amurka a watan Yunin 2019 - tsohon shugaban ƙasar ya dakata daga ƙarshe (duk da cewa ya ba da umarnin kashe wani babban janar ɗin ƙasar, Qasem Soleimani, wata bakwai bayan haka).
Yayin da ɓaraguzai suka cika tituna, kuma har yanzu abubuwa ke ci gaba da faruwa cikin sauri, masu faɗa-a-ji da sauran mutane na fama da faruwar abubuwan.
Yayin da yaƙin Gaza ke shiga shekara ta biyu, maganar abin da zai faru bayan yaƙin - yadda za a farfaɗo da Gaza da kuma gudanar da mulkin yankin - ta ɓace ko kuma faɗaɗar yaƙin ya shafe ta.
Haka ma duk wata hanyar sasanci tsakanin Isra'ila da Falasɗinawa, rikici na tsawon shekaru da ya kawo mu halin da muke ciki a yanzu.
Nan gaba, duk lokacin da Isra'ila take ganin ta gama lallasa Hamas da Hezbollah, sannan Iran da Isra'ilar suka gama cacar baki tsakaninsu, kuma aka kammala zaɓen shugaban Amurka, babu mamaki a samu damar bin hanyar difilomasiyya.
Amma dai, a yanzu babu wannan maganar.










