Ingila za ta fafata da Sifaniya a wasan ƙarshe na Euro 2024

Asalin hoton, BBC Sport
Tawagar ƙwallon kafan Ingila ta yi nasaran kai wa wasan ƙarshe na gasar cin kofin nahiyar turai, Euro 2024 bayan ta yi nasaran doke Netherlands da ci 2-1 a wasan daf da na ƙarshe aka buga a filin wasan BVB Stadion da ke birnin Dortmund.
Xavi Simmons ya fara zura wa Netherlands ƙwallo a raga a minti na 7 da fara wasa, amma Harry Kane ya farke wa Ingila da bugun fenariti a minti na 18, inda aka tafi hutun rabin lokaci ana ci 1-1.
Oli Watkins wanda ya maye gurbin Harry Kane a minti na 81 ne ya ci ƙwallo a minti na 90 kuma ya baiwa Ingila damar zuwa wasan ƙarshen gasar.
Wannan shi ne wasa na uku da Ingila za ta yi da Sifaniya a tarihin gasar cin kofin nahiyar Turai kuma ta yi nasara a wasanni biyun da suka gabata, a 1980 da kuma 1996.
Ingila ba ta taɓa lashe gasar ba a tarihinta amma Sifaniya ta yi nasaran lashe gasar a 1964 da 2008 da 2012. Tana neman zama ƙasa ta farko da ta taɓa lashe gasar sau huɗu.
Za a buga wasan ƙarshen gasar bana a ranar lahadi mai zuwa a filin wasan Olympiastadion da ke birnin Berlin.






