Amfanin ƙwai ga lafiyar ɗan'adam

Asalin hoton, Getty Images
Ƙwai na ɗauke da fa'idodi masu tarin yawa ga lafiyar ɗan adam. Ko a ci shi a dafe, ko a soye, ko ma a sha shi ɗanye, wannan abinci mai sauƙin samu yana ɗauke da sinadaran gina jiki sosai.
Ƙwai na da muhimmanci ga yara da manya saboda tana ɗauke da muhimman sinadarai da jiki ke buƙata da suka haɗa da Sinadarin gina jiki na Furotin da sinadaran bitamin B da B12 da Iron da Bitamin A da Lutein da choline da kuma sinadarin antioxidants da ke kare jiki daga gurbɓataccen abinci kamar yadda Dr. Hadiza Abubakar, ƙwararriya a fannin abinci da lafiyar jiki ta shaidawa BBC.
Ta kuma ce ana iya amfani da ƙwai wajen kula da fata da gashi inda ta ba da misali cewa za a iya shafawa fatar fuska kwai domin rage ƙuraje ko tsarkake fatar, da sa fuska ta yi laushi.
Haka ma ana haɗa ƙwai cikin sabulu ko man gashi saboda yana taimakawa wajen ƙarfafa gashi da sa shi sheƙi da kauri. in ji ta.
Ƙwararriyar ta ce cin kwai akai-akai yana taimakawa wajen inganta lafiyar jiki baki ɗaya.
Ga wasu muhimman fa'idodin amfani da ƙwai da ƙwararriyar ta lissafo
Ƙarfafa garkuwar jiki
Dr. Hadiza ta ce sinadaran Furotin da bitamin da ke cikin kwai suna taimakawa jiki wajen zama a matsayin rigakafi daga cututtuka.
Inganta lafiyar kwakwalwa

Asalin hoton, Getty Images
Sinadarin Choline da ke cikin kwai in ji ƙwararriyar yana taimakawa kwakwalwa wajen ajiye bayanai da inganta aikin tunani.
Ga yara kuma, ƙwai yana taimakawa kwakwalwarsu ya bunkasa da kyau yayin da suke girma.
Ƙarfin tsoka da gina jiki
Sinadarin gina jiki na furotin mai yawa da ke cikin ƙwai yana taimakawa wajen gina tsoka da ƙarfafa ƙasusuwan jiki in ji Dr. Hadiza.
Kula da lafiyar ido
Ƙwararriyar ta ce sinadarin Bitamin A da lutein da ke cikin ƙwai suna kare ido daga matsaloli kamar amasalin ido da kuma gani dishi-dishi.
Ƙarfafa ƙwayoyin jini
Sinadarin Iron da ke cikin kwai yana taimakawa wajen samar da jini mai lafiya, musamman ga yara masu girma da mata masu ciki in ji Dr. Hadiza.
Inganta lafiyar fata da gashi
Sinadarin Bitamin B da sauran sinadarai na kwai suna taimakawa fata da gashi su kasance cikin koshin lafiya.

Asalin hoton, Getty Images
Rage haɗarin kamuwa da cututtuka
Sinadarin gina jiki na furotin da antioxidants da ke cikin ƙwai na taimakawa jiki wajen yaƙi da cututtuka, in ji ƙwararriyar.
Kiyaye lafiyar zuciya
Cin kwai daidai gwargwado yana taimakawa wajen kiyaye lafiyar zuciya saboda yana rage haɗarin hauhawar cholesterol wato kitse kenan mara kyau.
Dr. Hadiza ta ƙara da cewa, "Ba dole sai lalle an daga ƙwai ko soya ta ba kafin a ci, ana iya zuba ɗanyen kwai a cikin lemun smoothies a haɗe a markaɗe, ko a haɗa a cikin kayan marmari, duk zai bayar da fa'idar da ake buƙata."
Ta kuma ce yaa da kyau a tabbatar da cewa ɗanyen kwai na da tsabta ko kyau kafin an yi amfani da shi saboda gujewa kamuwa da cutar salmonella."
Abubuwan da za a iya yi da ƙwai

Asalin hoton, Getty Images
- Soyawa
- Dafawa
- Gasawa.
- Egg roll
- Miyar ƙwai
- Soya shinkafa da ƙwai
- Soya taliya da ƙwa
- Kek
- Kwai a cikin custard ko akamu
- Kwai a cikin lemun sha ko smoothies.
- Haɗa man shafawa da ƙwai, da dai sauransu.










