Manyan malamai da ba a cika jin amonsu ba a Arewacin Najeriya

Asalin hoton, FB/Others
- Marubuci, Aisha Babangida
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Broadcast Journalist
- Aiko rahoto daga, BBC News, Abuja
- Lokacin karatu: Minti 5
Arewancin Najeriya na da malaman addinin Musulunci masu tarin yawa da suka ƙware a fannonin addini da dama da suka haɗa da ilimin Al-Ƙur'ani da Fiqihu da Hadisi da Tauheedi da gwaninta a harshen Larabci da dai sauransu.
Yayin da wasu suka yi shuhura tsakanin al'umma sakamakon yawan jin su da ake yi, ko dai a wuraren wa'azi ko kuma a kafafen sada zumunta, wasu da dama ba a san su ba sakamakon 'ƙanƙan da kai' da ɓuya da suke yi a sorayensu suna bayar da ilimi.
A bincikenta dangane da irin waɗannan malaman da kuma bayanansu, BBC ta tattauna da sheikh Abubakar Abdulsalam Baban Gwale, ɗaya daga cikin limaman juma'a kuma tsohon shugaban sashen koyar da ilimin Musulunci da Al-Ƙur'ani a Kwalejin Shari'a da addinin Musulunci ta Aminu Kano da ke Kano a Najeriya.
Sheikh Abdulsalam ya bayyana cewa, "akwai malamai da yawa a Arewacin Najeriya waɗanda ke koyarwa da yin wa'azi amma ba a san da su ba. Wasu daga cikinsu sun sadaukar da rayuwarsu wajen yaɗa ilimi cikin natsuwa."
BBC ta zaƙulo kaɗan daga cikinsu:
Sheikh malam Arabi, Kano
Sheikh Malam Arabi babban malami ne da yake zaune a unguwar Gadon Kaya, a birnin Kano.
"Malami ne mai zurfin ilimi wanda ya shahara a yankinsa, kuma abokin Sheikh Umar Sani Fagge ne," in ji Sheikh Abdulsalam.
Ya ƙara da cewa, "Malam Arabi yana da wallafa-wallafe da dama, wasu har yanzu ba a fitar da su ba, yawancinsu a fannin Fiqhu da Hadisi."
"Ɗaya daga cikin ƴaƴansa akwai limamin masallacin Usman bin Affan, Malam Abu Fatada Al-arabi," in ji Sheikh Baban Gwale.
Sheikh malam Yahaya na malamɓoyi, Sokoto
Sheikh Abdulsalam ya bayyana Malam Yahaya a matsayin "babban malami wanda ya fi shahara a Sokoto da kewaye."
"Malami ne wanda ba za ka gaza shi da karatuttuka waɗanda aka naɗe su musamman a murya, daga 3000 zuwa sama ba," in ji shi.
Ya ƙara da cewa malami ne wanda har rubutu ya yi kuma ya ci gyaran wasu malamai a kan wasu al'amura kamar su ƙira'a ta al-Qur'ani a jami'ar Musulunci ta Madina wanda har wasu malamai ma suka so da su gan shi tun sama da shekara 30 da suka wuce.
Ya na da masallacin juma'a kuma yana koyarwa.
Sheikh Muhammad Muktar, Kano
Sheikh Abdulsalam ya bayyana Sheikh Muhammad Mukhtar da ake yi wa laƙabi da Malam Mama da cewa, "matashi ne da Allah ya ba hazaƙa wajen bincike a fannin Hadisi a jihar Kano."
Ya ce, "Malami ne da yake sadaukar da kansa wajen karantar da ɗalibai tun daga matakin farko har su kai ƙwararru. Na ƙirga kusan ɗalibansa 40 zuwa 50 waɗanda suka zama masu da'awa da masana."
Ya ƙara da cewa, "Ban taɓa ganinsa da ido ba, amma na tabbata Allah ya ba shi yalwar ilimi."
Malami ne sosai amma ba a san shi a kafafen sada zumunta ba.
Sheikh Muhammdu Sani (Mai Larabci), Yobe
Wannan malamin ɗan asalin Gashuwa ne daga jihar Yobe, amma ya zauna a Kano.
Sheikh Abdulsalam ya bayyana shi da cewa, "Masanin Larabci ne wanda da wuya a samu irin sa. Manyan malamai da suka saurari karatuttukansa sun tabbatar da zurfin iliminsa."
Ya ce, "Tsohon lauya ne, amma bai bari wannan ya hana shi yaɗa ilimin Larabci ba. Duk da an fara yada karatunsa a kafafen sada zumunta, sai ya hana, yana cewa ba ya so."
Sheikh Muhammadu Sani ya horar da ɗalibai da dama waɗanda yanzu sun zama masu wa'azi da malamai a fannin Larabci kuma mahaddacin al-Ƙur'ani ne.
Malam Nuhu, Kano
Sheikh Abdulsalam ya bayyana Malam Nuhu da cewa, "Shehi ne da yake a unguwar Makasa a Kano, wanda malamai da dama suka amfana da iliminsa."
Ya ce, "Marigayi Malam Yusuf Uba Mandawari, wanda ya koyar da malamai da dama har suka zama Farfesoshi, shi ma ɗaya daga cikin waɗanda suka yi karatu a wurin Malam Nuhu ne."
Ya ƙara da cewa, "Shehunnan malamai irin su Malam Jafar Mahmud Adam da Dr Nazifi Inuwa da wasu da dama duk sun yi karatu a wurinsa."
Yanzu malamin ya manyanta sosai, amma har yanzu ana girmama shi saboda irin gudunmawar da ya bayar wajen gina malamai a Kano.
Wannan malamin kuma shi aminin malam Umar Sani Fage ne.
Sheikh Umar Balarabe, Zaria

Asalin hoton, Kasar Zazzau a Jiya Da Yau
Marigayi Sheikh Umar Balarabe babban malami ne daga Zariya masani ne musamman a fannin ilmin Fiqihu da ya taso a gidan da akwai malaman addini da dama a cikin birnin Zaria.
An ce malamin ya rubuta litattafai kimanin hamsin (50) a kan fannoni daban-daban na addini kamar yadda aka binciko bayan rasuwarsa.
Malami ne da ya shahara wajen koyarwa da karatun zaure, kuma ya karantar da ɗalibai da dama da suka zama malamai da masu wa'azi musamman a tsakanin Zaria da cikin garin Kaduna.
Sheikh Umar Balarabe ya rasu a shekarar 2020, kuma ya bar ƴaƴa da jikoki waɗanda a cikinsu akwai malamai masu karantarwa.
Malam Kabiru Ibrahim na Madabo, Kano

Asalin hoton, Facebook/Shamsuddeen Kassim
Ana yi wa wannan malamin laƙabi da Babban Malami na Madabo. Shehun Malamin ya shahara sosai a fannin koyar da addini, musamman fiiƙihu wanda ya rayu a unguwar Madabo da ke ƙaramar hukumar Dala a ƙwaryar birnin Kano.
Kafin rasuwar Malamin ya kasance babban mai bai wa Sarkin Kano shawara kan al'amuran da suka jiɓanci fiƙihu da kuma shari'a da mua'mala.
Yana ɗaya daga cikin zuriyar da suka kafa babbar makarantar ko jami'ar koyar da ilimin addinin Musulunci a Madabo shekaru kusan 600 da suka gabata.
Malam Aminu Adamu Dan-Nepu

Asalin hoton, FB/Aminu Adamu
Malam Aminu Adamu, wanda ake wa laƙabi da Aminu Adamu Dan Nepu ya kasance ɗaya daga cikin malaman da suka dage wajen koyar da litattafai a birnin Zariya.
Malami ne wanda ya gaji malunta daga mahaifinsa tare kuma da yin karatu a hannun mashahuran malamai daban-daban na addinin Musulunci.
Ya yi rubutu daban-daban a harshen Hausa da kuma na Larabci, sannan ya fitar da tsari na karatun zaure, wanda ya shafi fiƙihu da hadisi da sanin harshe da kuma nahawu domin taimaka wa ɗalibai sanin makamar karatu.
Malamin ya fi mayar da hankali ne kan koyar da karatu a zaure, kuma ba a cika jin ɗuriyarsa a kafafen sada zumunta ba.











