Me ya sa Trump ya fi sauran ƴan takarar Republicans farin jini?

Asalin hoton, Getty Images
Ko ka so shi, ko ka ƙi shi, ya dawo.
Tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya ayyana kansa a matsayin ɗan takarar da ke kan gaba a jam'iyyar Republican a zaben shugaban ƙasar Amurka da za a yi a 2024, biyo bayan nasarar yanke shakku da ya samu a jihar Iowa.
Nasarar ta sa ya samu ƙarin ƙuri'u masu yawa sama ga dukkan 'yan takarar idan aka haɗa wuri guda.
Daga baya, mai kamfanin nan na sarrafa tsirrai, Vivek Ramaswamy, wanda ya nemi tayar da ƙura a muhawarar da aka yi daga farko farko amma ya gaza yin wani tasiri.
Daga ƙarshe ya janye daga takarar ya kuma nuna goyon bayansa ga Mr Trump. Asa Hutchinson shi ma ya janye daga takarar.
Idan Trump ya iya samun tikitin takararsa a jam'iyyarsa ya kuma lashe zaɓen da za a yi a ranar 5 ga watan Nuwambar shekarar nan, zai zama shugaban Amurka na farko a tarihin baya-bayan nan da ya shugabanci ƙasar ya kuma faɗi ya sake koma kan gwamnati.
Wanda ya yi haka a baya a tarihi shi ne Grover Cleveland a 1892.
Duk da cewa ya yi wuri a kwanakin nan a takarar ace ga shugaban Amurka na 60 a tarihi, amma nasarar Mista Trump wata alama ce da ke nuna irin yadda yake ci gaba da karɓuwa tsakanin 'yan Republican.
Bari mu yi duba kan wasu dalilai da suka janyo hakan.
Tattalin arziƙi

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
"Zai farfaɗo da tattalin arziƙi ya kuma sakko da farashin gas" in ji wata magoyin bayan Trump a Iowa, ta bayyana haka ne lokacin da aka tambayeta dalilin da yasa take son Trump ya dawo kan mulki.
Ba ita kaɗai ba ce da irin wannan tunani. Tattalin arziƙi shi ne babban saƙon da tawagar neman zaɓen Trump take magana a kai.
Dan Trump, Eric ya shaida wa BBC cewa "mutane na buƙatar ci gaba da ƙarfafa kasarmu".
"Mahaifina ya samar da kyakkyawan tattalin arziki mai ƙarfi a tarihin ƙasar nan, ya yi maganin rashin aikin yi da kaso mai yawa, ya rage hauhawar farashin kayayyaki, da na gas."
Gaskiya ne gabanin annobar korona, tsarin tattalin arziƙin da Trump ya samar ya tsaya da kafafunsa.
Amma akwai lokacin da ya fi haka ƙarfi lokacin shugaban Obama kuma yake ci gaba da ƙarfi ƙarƙashin jagorancin jam'iyyar Democrat.
A wannan lokacin tattalin arziƙin Amurka babu shakka ya hadu da koma baya wanda bai taɓa fuskanta ba a tarihi, sakamakon barƙewar korona.
Lokacin shugaba Biden yaƙin da ake yi a Ukraine ya sa an samu tashin farashin makamashi da kayyaki sama da wanda aka gani cikin shekaru 40, ko da yake dai yanzu farashin na raguwa kuma tattalin arzikin na kyautatuwa sama da yadda aka yi tsammani a bara.
Trump 'mai karsashi da Joe 'mai likimo'

Asalin hoton, Getty Images
Tarihin aiki tsakanin mutane biyu sai ya fi yi wa Trump daɗi, inda daraktan yaɗa labarai na yaƙin neman zaɓen Trump a 2020, Marc Lotter: " daya daga cikin abubuwan da Biden ba shi da shi a 2020, " kamar yadda ya shaida wa BBC.
Ya ƙara da cewa "Yanzu Biden na da tarihi sai dai mutane ba su da muradin tarihin nasa".
Harkokin kasuwanci Trump da kuma tarihin da yake da shi na shahara mai makon na ɓangaren siyasa kawai, ya kara masa farin jini, kamar yadda wani mai goyon bayan shi a Iowa ya ce: " Babu buƙatar wani ɗan siyasa ya ci gaba da tafiyar da ƙasar nan, na yi amannar wanda zai fi dacewa shi ne wanda ya san yadda ake kasuwanci."
Daukakar Trump ta sanya mutane da dama suna masa kallo na daban idan aka kwatanta shi da shugaba Biden wanda masu suka ke kiransa da mai "Joe mai Likimo" bayan an nuna shi a kyamara yana gyangyadi a taron sauyin yanayi na COP26.
Amma a baya da suka kara da juna, Biden ne ya yi nasara.
Batun bakin haure

Asalin hoton, Getty Images
Lokacin da Trump ya ce 'yan cirani na "cutar da 'yan ƙasarmu" yayin wata tattaunawa da ya yi da The National Pulse a watan Oktoba, sai shugaba Biden ya zarge shi da kalaman marasa kyau irin na 'yan Nazi.
"Trump ya ce, idan ya dawo kan mulki, zai kori duka waɗanda suka riƙa adawa da shi, ya kuma kori waɗanda ya kira masu cinye arzikin Amurka.
"Kana jin kalaman sun yi irin na 'yan Nazi da ke Jamus a shekarun 1930," kamat yadda Biden ya bayyana, kuma ba wannan ne karon farko da yake faɗin haka ba.
Masana tarihi da kwararru da suka karanci farfagandar da Nazi ta riƙa amfani da ita sun shaida wa BBC kwatancen da Biden ya yi ya yi daidai. "Abin bai tsaya iya kalaman Nazi ba, hatta yadda suke motsa jikkunansu," in ji Anne Berge ta jami'ar Pennsylvania masaniyar tarihi.
Amma ƙuri'da CBS ta tattara sun nuna yadda 'yan Republican ke nuna goyon bayan waɗannan kalaman nasa.
CBS ta tambayi 'yan Republican waɗanda suka yi rijista ko sun yarda da kalaman Trumo ta hanya biyu. Rabin wanda suka bayar da amsar sun riƙa tambaya ne 'su wane ne ke cutar da ƙasarmu' kuma suka bayyana ra'ayoyinsu ba tare da tambayar wanda ya fada ba. Yayin da rabin waɗanda suka masar aka shaida musu Trump ne ya bayyana hakan.
Kwakkwaran goyon baya daga matasan Amurka

Asalin hoton, Getty Images
Wani goyon bayan na ban mamaki da aka ga Trump na samu a yanzu, yana nuna yadda yake ƙara kerewa Biden tsakanin matasa. Kuri'un da New York Times da kwalejin Siena suka wallafa a tsakiyar watan Disamba sun nuna yana saman Biden da kashi shida tsakanin matasa 'yan shekara 18 zuwa 29.
Babu mamaki hakan na da alaƙa da gazawar Biden wajen karɓuwa tsakanin matasa masu zaɓe, Suna cewa sun fusata ne da yadda yake tafiyar da rikicin Isra'ila da Hamas.
Mary Weston, ita ce shugaban matasan Republican a Iowa, ta shaida wa BBC cewa tana ganin matasan Republican za su sake cicciɓa Trump zuwa kujerar iko.
Yanzu shekararta 23, tana shekarun makaranta lokacin da yake shugaban ƙasa, ta ce mutane da dama suna "tsokanarta tare da cin zarafinta" kan goyon bayan shi.
Ta yi amannar yana "tsayawa kan abubuwan da yake da yaƙini a kansu" kuma "baya fargabar a san shi kan manufarsa" wannan abu na birge matasa.
Shari'un kotu 'yi wa mutane ba daidai ba'

Asalin hoton, Getty Images
Sau hudu ana tuhumar Trump a lamura daban-daban, kuma yana da shari'o'in da zai halarta a 2024 lokacin da yake neman sake komawa White House.
An shigara da shi ƙara a New York kuma haka a Georgia, Florida, Manhattan da Washington, yayin da masu gabatar da ƙara a matakin tarayya da na jiha ke buɗe bincike iri-iri a kansa.
Wasu ƙararraki da aka shigar a jihohi da yawa na neman a cire shi daga cikin jerin 'yan takarar shugaban ƙasa, ana cewa yana da hannu kan rikicin ƙasa da ya faru a yayin zanga-zangar da aka yi shekara uku baya.
Dole ya yi tsammanin wasu ƙararrakin kamar yadda wani tshon kwararren mai sharhi Frank Lance ya ce wa BBC hakan fa taimakawa Trump zai yi.

Asalin hoton, Getty Images
Idan Trump ya zama ɗan takarar Republican yana da abubuwa da yawa da zai yi a gabansa.
Zai fuskanci kwakkwaran ƙalubale daga tsohuwar wakiliyar Majalisar Ɗinkin Duniya a New Hampshire a yayin zaɓen fidda gwani a makon gaba.
Bayan nuna goyon bayansu da suka yi a kansa karon farko a Iowa, shi ne mafi farin jini tsakanin magoya baya a tsakanin masu zaɓe a Republican.











