Fitattun ƴan ƙwallon Najeriya da ba za su buga gasar Afcon ta 2025 ba

Lokacin karatu: Minti 5

A makon da ya gabata ne mai horar da ƴanwasan tawagar Super Eagles ta Najeriya Éric Sékou Chelle ya fitar da sunayen ƴan ƙwallo 28 waɗanda za su wakilci ƙasar a gasar cin kofin nahiyar Afirka ta 2025.

Kocin zai je gasar, wadda za a buga a ƙasar Morocco ne da zimmar samun nasara gagaruma bayan an yi waje da Najeriya a wasannin neman gurbin gasar cin kofin duniya ta 2026.

Daga cikin ƴan ƙwallon da Chelle ya fitar, akwai guda biyar da ba su taɓa wakiltar Najeriya a babbar tawaga ba, lamarin da ya janyo cece-kuce, a gefe ɗaya kuma wasu suke yaba masa da fito da sabbin ƴanwasa.

Sabbin ƴan wasa biyar ɗin su ne ɗan wasan baya Ryan Alebiosu da ɗan wasan tsakiya Ebenezer Akinsanmiro da Usman Muhammed da Tochukwu Nnadi waɗanda su ma duk ƴanwasan tsakiya ne, sai ɗan wasan gaba, Salim Fago Lawal.

Najeriya za ta buga wasanta na farko ne a ranar 23 ga Disamba, inda za ta fafata da ƙasar Tanzaniya a filin wasa na Sportif de Fès a birnin Fès.

Sai dai wani abu da ya ɗauki hankalin magoya bayan tawagar shi ne rashin ganin wasu fitattun ƴan ƙwallon ƙasar, a daidai lokacin da aka gayyaci sabbi, lamarin da ya janyo ake tafka muhawara.

Wannan ya sa BBC ta rairayo wasu zaratan ƴanƙwallon Najeriya da ake ganin akwai rawar da za su iya takawa a gasar in da an gayyace su.

Alhassan Yusuf

Alhassan Yusuf Abdullahi, ɗan wasan tsakiya ne da yanzu haka yake ƙwallo a ƙungiyar New England Revolution da ke fafatawa a gasar MLS ta Amurka.

Kafin ya koma Amurka da ƙwallo, ya taka leda a ƙungiyar Royal Antwerp ta ƙasar Belgium, inda ya buga wasa 90, ciki har da wasannin champions league.

Zuwa yanzu ya buga wa Najeriya wasa shida, yawanci a gasar cin kofin Afirka ta shekarar 2023, inda Najeriya ta zo ta biyu.

Maduka Emilio Okoye

Maduka Emilio Okoye mai tsaron ragar Najeriya ne a yanzu haka yake ƙwallo a ƙungiyar Udinese a gasar Serie A ta Italiya.

Asali an haife shi a ƙasar Jamus, amma ya zaɓi ya buga wa tawagar Super Eagles ta Najeriya, ƙasar mahaifinsa, duk da cewa mahaifiyarsa ƴar asalin Faransa ce mazauniyar Jamus, wanda hakan ya sa zai iya wakiltar ƙasashen Faransa da Jamus da Najeriya.

Ganin irin ƙungiyar da yake taka leda, da kuma irin rawar da yake takawa, inda daga kakar 2023 zuwa yanzu ya tsare ragar ƙungiyar a wasa 46, sai wasu ke mamakin rashin ganinsa a jerin ƴan wasan da za su je Moroko domin gasar ta Afcon.

Ya buga wa Najeriya wasa 16 daga lokacin da ya fara wakiltar ƙasar a shekarar 2019.

Terem Moffi

Terem Igobor Moffi matashin ɗanwasan gaban Najeriya da aka haifa a watan Mayun 1999, wanda shi ma yanzu ake ganin yana kan ganiyarsa.

A yanzu haka ɗan wasan yana taka leda ne a ƙungiyar Nice ta gasar Ligue 1 a Faransa, inda daga zuwansa ƙungiyar da farko a matsayin aro kafin daga baya ya zama na dindindin, ya zura ƙwallo 20 a wasa 61 da ya buga.

Ya buga wa Najeriya wasa 19 daga shekarar 2021 da ya fara wakiltar ƙasar, inda ya zura ƙwallo huɗu.

Victor Boniface

Victor Okoh Boniface ɗanwasan Najeriya ne da aka haifa a watan Disamban shekarar 2000, wanda yanzu haka yake buga wa ƙungiyar Werder Bremen ta Jamus ƙwallo.

Yana taka wa ƙungiyar leda ne a matsayin aro daga ƙungiyar Bayer Leverkusen ta Jamus.

Boniface ya ƙara fitowa duniya ne a kakar 2023 zuwa 2024 lokacin da ƙungiyar Bayer Leverkusen ta lashe gasar Bundesliga ta Jamus da kofin DFB-Pokal, sannan ta lashe gasar DFL-Supercup.

Sai dai ɗanwasan, duk da ƙwarewarsa wajen taka leda, ana ƙorafin bai samu nasarar nuna kansa ba a tawagar Super Eagles, inda har yanzu bai zura ko ƙwallo ɗaya ba a wasa 13 da ya buga wa ƙasar.

Ola Aina

Temitayo Olufisayo Olaoluwa Ola Aina fitaccen ɗanwasa ne da yake matuƙar ganiyarsa a tawagar Super Eagles ta Najeriya da ƙungiyar Nottingham Forest ta Ingila.

Yana cikin zaratan ƴawasan da aka yi tunanin za su taka rawar gani sosai a gasar wajen taimakon Najeriya ta samu nasara, amma sai kwatsam ya ji rauni, inda yake buƙatar makonni domin wartsakewa.

Haifaffen ƙasar Ingila, ya wakilci ƙasarsa ɗin ta haihuwa a matakin matasan ƴan ƙwallo masu ƙananan shekaru, kafin ya yanke shawarar komawa ya ci gaba da wakiltar Najeriya.

Umar Sadiq

Umar Sadiq ɗan wasan gaban Najeriya ne da yanzu yake taka leda a ƙungiyar Real Sociedad da ke Spain amma yanzu ya tafi ƙungiyar Valencia a matsayin aro ita ma a ƙasar Spain.

Ɗanwasan ya wakilci ƙasar a gasar Olympic ta shekarar 2016, inda Najeriya ta lashe azurfa.

Ya wakilci babbar tawagar Najeriya ta Super Eagles sau 12, inda ya zura ƙwallo 1 kacal.

Ahmed Musa

Ahmed Musa ne asalin kyaftin ɗin tawagar Super Eagles ta Najeriya da aka yi tunanin zai buga gasar.

Fitaccen ɗanwasan ya halarci gasar ta shekarar 2023, amma bai buga wasa ba, inda ya kasance wani babban jigo da ke ƙarfafa gwiwar matasan ƴanwasan da suke buga gasar ta hanyar taimakon kocin tawagar na wancan lokacin.

Bayan zuwan koci Chelle ne ya sake gayyatar Musa domin buga wasan sada zumunta, inda aka yi tunanin zai gayyaci ɗanwasan zuwa gasar cin kofin Afirka ta 2025.

A watannin baya, ɗanwasan gaban tawagar, Victor Osimhen ya bayyana yadda kasancewar Ahmed Musa a tawagar ke ƙarfafa musu gwiwa.

A yanzu haka yana buga ƙwallo ne a ƙungiyar Kano Pillars ta Kano.