Yadda ƴanmata ke shiga ƙwallon ƙafa don guje wa auren dole

    • Marubuci, Divya Arya
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
  • Lokacin karatu: Minti 7

A wata rana da yammacin bazara lokacin da Nisha Vaishnav take da shekara 14, ita da ƴar uwarta mai shekara 18 Munna, sun kasance suna atisaye a filin kwallo lokacin da suka gano wasu mutum biyar na ɗaukarsu hoto.

Ba a jima ba Nisha ta gano abin da ya sa ake buri a kanta - mutanen sun fito cikin iyali ɗaya, kuma har da wasu ma'aurata da ke nema wa ɗansu matar aure.

Mahaifiyar Nisha, wadda ita ma take wurin, ta ƙarfafa cewa auren mai yiwuwa ne.

Dukkansu sun koma zuwa ƙauyen Vaishnav da ke Padampura, a jihar Rajasthan da ke arewa maso yammacin Indiya.

"Mahaifiyata ta buƙaci in taɓa yatsun kafansu a matsayin alama ta girmamawa," in ji Nisha.

"Ni kuma na ki yin haka."

'Matan ƙauye na nuna mu da yatsa'

Yayin da aka amincewa yarinya ƴar shekara 18 ko kuma matashi ɗan shekara 21 su yi aure a Indiya, abu ne da aka saba gani.

Kusan kashi 25 na matan da ke rayuwa a Indiya sun yi aure ne kafin su kai shekarun da aka kayyade, a cewar asusun kula da yara na Majalisar Ɗinkin Duniya Unicef.

Sai dai, aurarraki tsakanin yara ya ragu matuka a shekaru 30 da suka wuce.

A can baya a shekara ta 1992-93, kusan kashi 66 na matan Indiya sun yi aure kafin su kai shekara 18, a cewar wata cibiyar kula da lafiyar iyalai.

A jihar Rajasthan, alkaluman aurarraki na yara ya ƙaru fiye da shekarun da aka kayyade a ƙasar, kuma da wuya ƴan mata su ki amincewa da batun aure ko kuma saɓa wa umarnin iyayensu.

Sai dai, Nisha ta samu wani ƙwarin gwiwar tsayawa kan matsayarta bayan samun kwallon kafa - wasan da ta ce ya sauya mata rayuwa.

Ƴar uwarta Munna ce ta fara kwaɗaita mata wasan a 2022, bayan shiga wasan shekara guda ta hanyar wata ƙungiya - wadda ke da burin taimakawa ƴan mata samun ingantaccen rayuwa ta hanyar kwallon kafa.

Munna ta bijiro da batun wasan kwallon kafar a ƙauyenta, inda ta yi ta fuskantar kalubale wajen tafiye-tafiye zuwa gasanni da kuma saka kayan kwallon kafa guntaye maimakon doggin wanduna - wani mataki na musamman a ƙauyen da matan aure ke rufe fuskokinsu a cikin maza a bainar jama'a.

"Kwanaki biyu zuwa uku na farko, matan ƙauyen na nuna mu sannan su ce, 'Kalli waɗannan yara suna bayyana ƙafafunsu a waje," in ji Munna.

"Mun yi biris da su, mun ki kula su, inda muka ci gaba da saka guntayen wandunan kwallo."

Nisha ta samu ɗaukaka da wuri a kwallon kafa, inda har ta kai ta buga wa tawagar jihar Rajasthan wasa a gasar ƙasa a 2024.

Ta kuma rage girman gashinta - wata alama ta turjiya a ƙauyen da ake son ƴan mata su bar gashinsu ya girma.

Lokacin da mutanen da suke kallonta a fili tana buga wasa suka zo tambayar aurenta, Nisha ta ki aminta.

Ta bayyana ƙarara cewa ta yi ƙanƙanta ta yi aure kuma tana son ci gaba da ganin ta cimma burinta a fagen kwallon kafa.

Bayan wata ɗaya, iyalin suka janye buƙatarsu.

Nisha da Munna sun kuma yi watsi da batun haɗakar aure daga wasu iyalai a 2025, wanda ya kunshi dukansu da kuma kaninsu.

Ƴan matan suna adawa da batun auren wuri kuma suna son mayar da hankali na cimma burinsu a ɓangaren wasanni.

Lokacin da mahaifinsu ya tambayi Nisha idan tana da masoyi a wajen da take zuwa buga kwallo, ta ce: "Ba ni da wani masoyi. Ina son buga kwallon kafa - ita ce masoyiya ta."

Samun aiki ta hanyar kwallon kafa

Ƴan matan da suka yi aure da wuri na cikin barazanar tilasta musu yin jima'i, ɗaukar ciki da wuri, rashin abinci mai gina jiki da kuma rashin isasshen lafiya, a cewar bincike da aka gudanar.

Akwai kuma waɗanda ke barin makaranta da wuri, abin da ke rage musu damar inganta rayuwarsu.

Padma Joshi, daga ƙungiyar Football for Freedom, wanda wani ɓangare ne na ƙungiyar mata ta Mahila Jan Adhikar Samiti, na son faɗakar da iyalai kan irin waɗannan barazana.

Ta ce ƙungiyarsu ta horar da ƴan mata sama da 800 a faɗin ƙauyuka 13 a jihar Rajasthan tun bayan kafa ta a shekara ta 2016.

"Lokacin da muka fara tattaunawa da iyaye ba mu taɓa cewa za mu ɓullo da kwallon kafa don dakatar da auren wuri ba," in ji Joshi.

Sai dai, "lokacin da muka fara aiki da ƴan matan kuma suka gano hakkokinsu da kuma illar aure da wuri" daga nan suka fara tashi don yin magana, in ji ta.

Joshi ta kuma faɗa wa iyayen yara cewa samun ɗaukaka a kwallon kafa zai taimakawa yaransu wajen samun aiki, saboda jihohin Indiya sun keɓe wasu gurabe ga mazan da suke kwallo da kuma mata.

Talauci, da kuma batun al'ada, na cikin abubuwan da ke saka iyalai ci gaba da yi wa ƴaƴansu mata aure, waɗanda yawanci ake ɗauka a matsayin jidali.

Wasu lokutan ana aurar da su ga matasan da shekarunsu yake ɗaya, amma wani lokaci kuma ga manya.

Ƴan matan na komawa karkashin kulawar mazajensu da zarar an ɗaura aure, abin da ke nufin cewa duka ɗawainiyarsu ta koma kan mazajensu ba kuma iyayensu ba.

Nisha da Munna suna da babbar yaya wadda aka yi wa aure a shekara ta 2020 lokacin tana da shekara 16, ita ma mahaifiyarsu Laali, auren wuri aka yi mata.

Da take kare matakin ta, Laali ta ce: "Ina cikin damuwa saboda ƴaƴa na mata. Ƙauyawa na cewa idan ƴan mata suka fita daga gidajensu, za su haɗa da masu nuna musu munana abubuwa da kuma wasa da yara maza, don haka ne muke musu auren wuri."

Da aka tambaye ta cewa ko tana son ta saɓa wa ka'ida wajen aurar da babbar ƴarta a lokacin da take shekara 16, ta kaɗa kai, tare da cewa babu wanda zai sani: "Mun auren cikin tsanaki, ba mu buga katunan gayyata ba ko kuma ƙawata gida ko kafa tanti."

Sai dai dokar ta bayyana komai a fili - yin aure da wuri babban laifi ne.

Manya da ke gudanar da bukukuwa, haɗe da iyalai da ke yin auren wuri ko kuma suka ki dakatar da abin, za su sha ɗaurin kusan shekara biyu da kuma tarar rupee 100,000 (dala 1,100).

Sai dai, Anjali Sharma, shugabar kwamitin kula da walwalar yara a birnin Ajmer da ke jihar Rajasthan, ta ce da wuya a iya samun masu laifi saboda shaidu ba su cika bayar da hujjojin da suka kamata ba ga hukumomi.

"Idan iyalai suka gano cewa mun san batun auren wuri, za su rage ranar bikin da kwana ɗaya ko kuma ƙarawa da kwana ɗaya ba ranar da muke tsammani ba," in ji Sharma, inda ta ce ɗaukacin ƙauyuka na haɗa baki wajen ɓoye batun auren wuri.

Idan amarya ko ango ya kai ƙorafi wajen jami'an tsaro, ana iya soke auren, sai dai da wuya su kai ƙarar iyayensu saboda sun haka zai janyo ɗauri ko kuma tara.

Idan ba a kai rahoto na batun auren wuri ba, ana rajistarsu daga baya lokacin da suka kai shekarun da aka kayyade na aure kuma babu wanda za a hukunta.

Rahotanni sun bayyana cewa auren wuri da ake yi wa ƴan mata na ƙaruwa sannu a hankali a Indiya yayin da ake ƙara inganta batun wayar da kai.

An ruwaito cewa an aurar da ƴan mata sama da 1,050 a shekara ta 2021 idan aka kwatanta da 395 a 2017, a cewar ma'aikatar mata da ci gaban yara.

Sai dai, wannan kaɗan kenan cikin alkaluman ƴan mata ƴan ƙasa da shekara 18 kusan miliyan 1.5 da aka kiyasta ana aurar da su a kowace shekara a Indiya, a cewar Unicef.

Nisha, wadda ke shekara 15 kuma take makaranta har yanzu, na fatan buga wa tawagar kwallon kafa ta Indiya wata rana.

Idan ba ta samu damar ba, samun aikin gwamnati zai ba ta damar riƙe kanta da kuma samun ƴanci.

Domin samun ɗaya daga cikin guraben aiki da aka tanadawa maza da kuma mata na ɓangaren kwallon kafa, tana buƙatar ci gaba da buga wasa a matakin jiha ko kuma jajircewa har sai ta gama karatun jami'a.

Yayin da Munna wadda ke shekara 19 a yanzu, ke koƙarin ƙauce wa auren wuri, har yanzu akwai yiwuwar gabatar da buƙatar neman aurenta.

Har yanzu iyalin da suka auri babbar yayarta na kokarin ganin an haɗa aurenta da ɗansu.

Sai dai tana ci gaba da yin watsi da buƙatar.

Munna ba ta kai matakin da Nisha ta kai ba a kwallon kafa, sai dai tana taimakawa wajen horar da ƴan mata kuma tana karatu a jami'a.

Tana fatan zama malamar kwallon kafa a wata makaranta - wani abu da zai samar mata da kuɗi da kuma ƴancin zaɓar rayuwar da ta dace da ita.

Kafin lokacin, yanzu tana nunawa ƴan matan da take horarwa illar auren wuri.

"Ko da zan dakatar ko kuma ƙasa dakatar da aurensu, ina son taimaka musu wajen zama wani abu a rayuwa, don cimma burinsu."